*💔SO DA SHAQUWA*💔
*its for sale*Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461Free page
*fourteen*Ban farka ba sai kusan bayan sallar magrib sai naji na samu sauk'i sosai bedroom din momy naganni,mik'a nayi ina salati sannan na sakko kafafuna zan shiga toilet naji anbude kogar anshigo kyawawan idanuna masu kalar bacci na sauke akansa,yayin da shima ya zuba mani nasa masu kama da maijin bacci,lumshe nawa nayi na kauda kai na koma na jingina da makarin gadon ina lumshe idona,don mayen k'amshinsa ya cika d'akin,bansan meyasa yake son saka turare har haka ba.amma duk da haka kamshin yayi mani sosai,ina masifar son kalar turaren dayake anfani dashi.
Maida k'ofar yayi ya rufe yana jingina bayansa da k'ofar muryarsa so cool kamar an fiddota cikin frig naji yace mun.
"How are u feeling now"
Ahankali na bude idanun nawa na kalli kafin na bude d'an bakina nace "I'm ok."
Shiru muka sake yi don zan iya cewa wannan ranar ce mukayi mgn tun farkon xuwanmu gidan da muka ringa samun sab'ani.
Fitsari nakeji kuma bazan iyashiga toilet gabansa ba so kuma ba dadi nace yatafi,na dan yamutsa fuska nace "pls I need ur help"
Kamar jira yake yace "uhun tell me what u want"
Na narke fuska saboda yadda fitsarin ya matseni nace "kace ma momy yunwa nakeji akawo mun abinci anan bazan iya fitowa ba"
"Ok sorry give some minute"
Ya fice daga d'akin naja tsaki ina tashi na shige agurguje nai fitsarin na canza pad da yake naga momy ta ajiye wata a toilet din.
Ina fitowa suka shigo tare har da yusrah murmushina nai masu na koma bakin gado na zauna tunda ba salla zanba.
Momy tace "sannu dota,ya kikejin jikin naki to"
Nai mata murmushi nace "momy I'm feeling better,yunwar ce kawai take damuna kamar an mun sata acikina"
Dariya sukai mun ita da yusrah shikuwa ya sani gana da kallo,ban kulasa ba.
Yusrah tace "sannu anty Anam,wlh kin bamu tsoro d'axun"
Na dingure mata kai nace"daman fa ina yin haka idan raina ya b'aci sosai,ina yakumbo bata fad'a maku ba."Momy tace "tana falo nace ta shigo ta ganki ta nuna halinku na fulani"
Murmushi nai nace "bari naci abincin naje na ganta,"Yusrah tace "dady ma yadawo zaizo yaganki"
Cikin farin ciki nace "wayyo dady munyi kewarsa da yaushe ya dawo"Momy tana xuba mun dafeffen dankalin turawa da miyar kwai tasha vegetables sai xuba k'amshi take,tace "kici abincin banson yawan mgn."
Na ansa ina gyara zamana yusra tace "Bari naje na copying din assignment din da yaya yamun na dawo,"
Dakai na ansa mata saboda lomar danakai bakina da spoon.Momy tace "zanje na had'a dinner dadynku karfa kici kad'an kitabbatar kin cinyesa,nazeer kayi mun gadinta"
Kamar tasan kau ba fitar zaiba.
Bayan duk sun fice ban sake kallonsa ba na ringa cin abincina,Amman inajin mayun idanunsa akaina har na dauko loma zan saka bakina na fasa na d'ago da kaina,na kallesa muka had'a ido girarsa ya dage na daure fuskata nace.
"Kana so na kwarene?"
Girgiza kai yayi nace "to meyasa ka tsareni da ido"
Ya zaro idonsa masha Allah har saida na kauda kai yace "keda baki kallan ba yakika gane ina kallonki"
Nai banza dashi na cigaba da cin abincin,bai kuma fasa kallon nawa ba karshe ina cin rabi na ajiye na dauki ruwa nasha.........."lalala aikuwa zan fad'a ma momy bakici da yawa ba"
YOU ARE READING
SO DA SHAQUWA
Randomlabarine akan tsantsar soyayya sadaukarwa jajircewa,da darasin rayuwa labarin yana koyar da zamantakewar duniya da yadda zaka zauna da mutane,karki bari ya wuceki tabbas so da shaquwa yana dauke da salo salo na musamman sai wanda ya bisa zaifahimci...