part twelve

17 1 0
                                    

*💔SO DA SHAQUWA*💔

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461

Free page
     *twelve*

Tunda motarmu ta shiga cikin wannan tangamemen gida na saki bakina da hancina ina kare masa kallo,hakika tunda naxo duniya bantab'a cin karo dagida irin wannan ba,awajena zan iya kiransa da aljannar duniya.
Bani kadai ba har yakumbo kanta tasha mamakin wannan katon gida mai dan karen kyau da girma.
Parking akai muka fito daka kallemu zaka ga tsantsar kauyanci tattare damu,kasancewar dare yayi sosai yasa yabada umurnin akaimu can Boy's quarter mu kwanta kafin gari ya waye.

Matar data kawomu da gani dai yar aikin suce,itace ta kawo mana abinci mai rai da lafiya ga namomi asama,dayake duk yunwar mukeji muka saki ciki mukaci sosai da sosai tass saida muka ga bayansa.muka sha ruwa harda lemu salolin mu mukai sannan muka fara shirin bacci
Daya ke mun gaji sosai sai bamu jiba baccin duk ya kwashemu.

Washe gari da safe tunda nai sallar asuba ban koma ba nida yakumbo,har gari yawaye muna laximi muna yiwa baffa addua ganin haske yaketo yasa yakumbo tace"zeenatu ko zakije ki kama masu wani aikin,ba munyi zaune ba haka saidai adafa abamu"

Daman so nake na zaga gidan nai saurin mik'ewa nace "to yakumbo"
Hijab d'ina nasaka na nufi kofa na fice.
Duk wani waje na compound din gidan saida na lek'a sak'o da lungunsa na gani,har lambun dake gidan acan ma nafi dadewa wurin yayi masifar burgeni ainun,daker na bar wajen wani na gani yana ba flowers ruwa na tambayesa ya nuna mani hanyar cikin gidan.
Ya gwada mani na nufi hanyar kenan zan shiga naga anbude k'ofar wani saurayi ya bayyana gabana,zaro idanuna nai sosai ina kallonsa daga sama har k'asa.
Turus yayi gabana yana kallona shima kamar yadda nake masa,amman shi fuskarsa ayamutse take alamun dai bai sanni ba kuma bai zaci ganina anan ba.
*nazeer Abdulhady salis* kenan tabbas yaron ya had'u idan nace had'uwa to ta ko'ina yagama hadewa,tun daga fuskarsa har xuwa gangar jikinsa bazan iya tsayawa fayyace kyansa ba amman tabbas nazeer karshe ne.............muryarsa mai dan karen dadi ce ta katse mun shagala da kallonsa danayi,yana cikin uniform da alama makaranta zashi.

"Ke lafiya?wakike nema mekike anan?"

Duburcewa nai ina jujjuya hannu ina rausayar dakai cikin ladabi nace "ammm daman.......daman zan shiga cikine........katseni yayi yana dalla mun harara.
"Kiye me acikin,wai waye yakawo ki mu bamu sanki ba,kinga hanya wuce kinyi mistake ne kila ba nan gidan kike nema ba"

Raina yab'aci ganin yadda yake nuna kyamarsa akaina naja tsaki,aikuwa ya sake jin haushi cikin yar tsawa yace "keeee ubanwa kikewa tsaki anan?baki da hankali zaki bar nan ko saina daukeki da mari"

Naja baya ina harararsa nace "wallahi badai ubana ba,baffana yana can cikin kasa karka sake zagarmun shi,don munxo gidan ku bashine zaisa ka ringa zaginmu ba"

Ganin matsoni yake zai kwasa mun marin na daddaga aguje nakoma wajen yakumbo ina shashsheka............

"Kaida waye ne lil bro"

Wani matashin saurayi wanda shima ya had'u sosai amman da ganinsa zaka gane yayan wannan karaminne.

Dogon tsaki yaja yace "wata yar iskar yarinya ce kazama take kokarin zagina,wlh dana zubar da banza anan ko uban wa ya kawota ohu naga tayi boy's quater aguje"

Murmushi yayi masa ya rik'o hannunsa yace "to zonan muje dady yana kira koma miye zamuji daga garesa."
Suka juya xuwa cikin gidan.

"Lafiya zeenatu meyafaru?"

Yakumbo tatashi zaune daga kwanciyar datai tana tambayar yar tata.

Raina b'ace ina shashsheka nace "wani marar mutuncin yarone yazageni,da alamun d'an gidanne"

SO DA SHAQUWAWhere stories live. Discover now