Page 1&2

64 5 1
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan_*

1&2

"Hafsatu ki tashi yanzu kije rafi ki deboman ruwa, " wata mata dake fitowa daga daki, take gayama wata yarinya wadda bata wuce shekara goma sha biyar ba.

"Inna kiyi hakuri dan Allah wallahi kaina ke ciw..." Kafin ta karasa fadin abinda zata fadi, wannan matar ta kife ta da wani mahaukacin mari.

"Wallahi ko zaki mutu sai gawar ki ta deboman ruwan nan, kaji man yar iskar yarinya mai bakin hali irin na uwa," matar ke fadin haka tare da  kamo hafsatun, tana kama hannun ta  taja ta zuwa cikin dakin da ta fito.

Rufe dakin Inna tayi ta dinga bugun Hafsatu, har sai da tayima ta jina-jina kafin ta turo ta tsakar gida.

"Na baki minti daya ki fita ki deboman ruwa na in ba haka ba wallahi sai nayi maki wanda yafi shi. "

Kafin ma ta rufe baki har Hafsatu ta dauki tulun da take debo ruwa dashi, ta kama hanyar rafi tana tafe tana kuka, duk inda ta gitta sai dai abita da kallo kowa na tausayin rayuwar da take yi cikin gidan su.

A haka har taje rafin, babu kowa bakin rafin saboda rana ta take, dama in dai da rana kaje to baka tadda kowa rafin, a haka ta debo ruwan ta dawo gida, ba ita ta gama dibar ruwan ba sai yamma lis, saboda duka kayan gidan sai data cika su da ruwa.

Tana gamawa taje inda Inna Asibi ke ajiyar kayan ta masu datti, kwaso kayan tayi gaba daya ta fito, tana tafiya tana hada hanya har ta isa inda suke wanki, dukawa tayi tana wankin kayan kamar ta kife cikin robar saboda azababbiyar yunwar da take ji, duk yau babu abinda tasaka ma cikin ta sai ruwa, dama haka Inna Asibi take duk ranar da taso cuta to hana ta abinci take yi.

Tana wankin tana kuka a haka har ta samu ta gama, gaba daya jikin ta ciwo yake ga kan ta sai sara mata yake yi, tana gamawa taje inda Inna Asibi ke zaune ta durkusa, "Inna nagama wankin. "

Gurmuda baki Inna Asibi tayi kafin ta muskuta ta gyara zaman ta "To shegiya dan kin gama sai kuma akace kizo ki tsareni da wadannan kwala-kwalan idanuwan naki, kije ki dora man abincin dare mana, har magriba tayi amma ba'a dora girki ba, kai ni dai wallahi Malam ya cuceni daya kawoman yar tsintuwa cikin gida tana niyyar kashe ni da raina! " ta fada tana mai fashewa da kukan munafurci.

"Dan Allah Inna kiyi hakuri wallahi bansan ranki zai baci bane da ban zo na tambaye ki ba, kefa uwata ce da... " kafin ta ida Inna Asibi ta kai mata wani naushi ga baki, runtse idanuwa tayi saboda azabar da taji ta ziyarce ta.

"Tir! Tir!! Tir!!!  Allah ya sawake in haifi diya kalar ki, wama yasani ko shegiya ce ke baki da uba, shiyasa aka jefar dake, shi kuma Malam da kwashe-kwashe yaje ya kwasoman ke. "

Mikewa Hafsatu tayi ta nufi madafi ta hada itacen da zata yi girkin dasu, fuskar ta sharkab da hawaye, wannan wace irin rayuwa ce ta keyi dabba ma ta fita gata.

Tana sanwar tana share hawayen fuskar ta, ga dare yayi cikin duhun tai ta girkin, ba ita ta gama ba sai wucewar isha'i, tana gamawa ta debi ruwa taje ta watsama jikin ta, tare da dauro alwalla ta shige dan akurkin dakin ta, wanda babu komai cikin shi sai tabarmar kaba, sai ledar kayan ta wadanda basu fi kala hudu ba.

Tana shiga dakin ta shimfida kallabin ta, wanda ta maida shi matsayin abin sallah, tana cikin sallah taji muryar Inna na kwalamata kira.

"Hafsatu! Hafsatu!! "

Jin shiru yasa ta daga labilen dakin, ganin sallah takeyi yasa ta tabe baki, "To dangin limamai sallar ce ake tayi ko to ayi lafiya. "

Ta fada tare da juyawa ta bar bakin dakin, tana ta sababin da ta saba yi.

Hafsatu na gamawa ta fito dakin, babu kowa tsakar gidan sai hasken farin wata daya haske gaba daya tsakar gidan, dakin Inna ta nufa kai tsaye ta daga labilan tare da sallama.

"Inna gani ina sallah kika kirani, " ta fada tana sunkuyar da kanta kasa gudun laifi.

Sai data kare mata kallo, kafin tace "yau mugun hali ya hanaki zuwa ki debi abinci. "

Girgiza kai Hafsatu tayi"A'a Inna sallah na fara yi. "

"Dalla chan tashi ki ban guri kilbabbiyar banza. "

Mikewa tayi ta nufi madafin ta debo tuwon dawa Miyar kuka, yau shi ta dafamasu, har lokacin tana jin gunin sababin da Inna keyi, girgiza kai kawai tayi ta nufi dakin ta, zama tayi ta cinye tuwon gaba daya, nan da nan sai ga zufa ta jike mata jiki gaba daya.

Mikewa tayi ta dauki kwanon ta fito tsakar gida, hadawa tayi har da wanda Inna ta bata ta wanke gaba daya, ta wanke bakin ta kafin ta juya zuwa dakin ta, kwantawa tayi tana tunanin irin UKUBAR da take ciki tun da ta tashi a haka ta tsinci kanta har kawo wa yanzu, ita dai tana sha'awar ganin iyayen ta ko ya suke tana son su tana son kasancewa tare dasu, da wannan tunanin bacci yai gaba da ita batare da ta shirya ba saboda gajiyar dake jikin ta.

Hussy Saniey🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now