*بسم الله الرحمن الرحيم*
*🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_Dumin shiga shafin,mu na Bakandamiya dana shudin rubutun nan na kasa_*
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*13&14
Hafsatu ta dad'e zaune cikin halin tsoro, da k'yar ta samu taje ta yi alwallar la'asar, tana gama sallar ta yi zaune tana addu'oin da yanzu suka zame mata abin yi koda tana zaune ne hakanan.
Bayan ta gama addu'oin ta sai ta mike tsaye tana k'ara gyara hijabin dake jikinta, tsakar gida ta fito ta kara gyara shi duk da babu dattin da yayi amma dai gudun fad'an Inna Asibi yasa ta k'ara gyarawa.
Tana gamawa ta fita dan zuwa gidan Baba Yalwa ko zata ji saukin kewar da ke damunta, tana shiga babu kowa tsakar gidan dan haka ta kwada sallama.
"Assalamu Alaikum da mutum a gidan nan? " cewar Hafsatu dake kwala sallama.
"Wa'alaikissalam ganin cikin d'aki muryar wa nake ji kamar ta Hafsatu? " Baba Yalwa dake fitowa daga d'aki ke amsawa Hafsatu da har lokacin tana tsaye tsakar gidan.
"Ni ce Baba zaman gidan ya isheni babu kowa sai ni kad'ai ciki kamar mayya" Hafsatu ke maganar tana juyawa alamar tana neman wani abu.
"Ai kadaici beda dad'i yau ina Innar taki ta shiga ne duk yau banji ihun taba" Baba Yalwa ke maganar tana dariya.
Ita ma Hafsatu dariyar ta yi kafin tace, "wallahi yau bansan inda ta nufa ba tun safe bata gidan ko ina ta nufa Allah kad'ai yasani."
Baba Yalwa dake shimfid'a tabarma tayi murmushi sannan tace, "Ai yau dai kinsamu sauk'i kafin ta dawo dan dai ba fasawa take ba."
"Ni fa wani lokaci Baba banganin laifin Inna saboda in dai ba d'an uwanka ba wannan lokacin ai baka samun mai rik'e maka d'a ko da yan uwan ma wasu basu rik'ewa ko da rabin rikon da take yi man" Hafsatu ta fada da iyakar gaskiyar ta.
Murmushin takaici Baba Yalwa ta yi, "Hakane gaskiya Hafsatu rikon d'a wahala gare shi nima wani lokaci ba ta b'ataman rai saboda ina ganin kokarin ta sosai sai ma kinji irin jajircewar da tayi akan ki zauna nan hannun ta, saboda da lafiya lau take rik'on ki daga baya dai ne mazuga suka zugeta. "
"Baba ashe da Inna tana so na? " cewar Hafsatu da ta fuskanci Baba Yalwa dan neman k'arin bayani.
Jinjina kai Inna Asibi tayi" Tabbas da kinsamu rik'o mai kyau a hannun Asibi sai daga baya ne abin ya chanza."
"Allah sarki Inna to meye mafarin chanjin na ta Baba?" Hafsatu ta tambayi Baba Yalwa.
Daga kai sama Baba Yalwa ta yi alamar tunani kafin tace,"Gaskiya ni dai a iya sani na da Asibi tana son ki sai daga baya ne k'awar ta Tasallah ta zuge ta."
Murmushin takaici Hafsatu ta yi kafin tace, " Dama na dad'e ina zargin Baba Tasallah da zugar Inna."
Jinjina kai Baba Yalwa ta yi "gaskiya ne domin bazan manta ba lokacin da aka zo dake an tsinto ki da mayar dake za'ayi sai ita Asibi ita ta rink'a kuka har sai da aka bata ke, kuma lokacin ta kula dake sosai amma dai tun daga fara k'awancen su da Tasallah halayen ta suka chanza. "
Zubama Baba Yalwa idanuwa Hafsatu ta yi kafin ta had'e wani abu mai d'aci da ya tokare mata makoshi," Baba Yalwa kina so kice man da Inna Asibi ta kula dani sosai? "
"Kwarai da gaske Hafsatu taso ki fiye da yadda kike tunani ko bacci bata iyawa idan ba kin yi ba, in kuwa baki da lafiya ita ma ciwon take kwanciya, duk abinda kike ganin yana faruwa to laifin Tasallah ne" Baba Yalwa ta fadama Hafsatu da alamar tabbatar wa.
Shiru Hafsatu ta yi tana mamakin maganganun Baba Yalwa, dan dai ta san Baba baza ta yi mata k'arya ba da wani ya gayamata bata da ko kad'an bata yarda.
Baba Yalwa ta katse mata tunanin ta gurin fadin" ki tashi kije gida magrub ta kawo jiki kada ta dawo bata taddaki ba kuma kisha wani dukan. "
"To shikenan Baba amma da naso ki bani labarin meyafaru dani tun daga lokacin da aka tsinto ni kuma waya kawoni nan garin? " Hafsatu ta fada tana mai share hawayen fuskar ta.
"Insha Allah zan gayamaki amma ba yau ba sai mun samu damar yin hakan" Baba Yalwa ta fad'ama Hafsatu.
Jinjina kai Hafsatu tayi cikin alamar gamsuwa"to Baba Yalwa nagode kwarai Allah ya saka maki da alkhairi,Allah yayi maki sakamako da gidan Aljanna. "
"Ameen nagode kwarai nima da dauka ta da ki kai kamar mahaifiyar ki" inji Baba Yalwa.
"To Baba na wuce sai anjima," inji Hafsatu da ta juya domin tafiya gidan su.
"Ki amshi wannan sun yi maki amfani na manta ban gayamaki ba, d'a na dake zaune maraya zai zo anjima mu tafi chan zan koma, d'azun bayan tafiyar ki yazo ya tafi gabas ya gaido dangin baban shi," Inna Asibi ke fadin maganar kuma tana kokarin kwanto habar zanen dake jikin ta inda ta kulle kudin ta.
Wata irin juyowa Hafsatu tayi jikin ta da muryar ta na kyarma, " Ba..ba in..na zaki tafi? "
Dafa kafadar ta Baba Yalwa ta yi kafin ta ce,"kiyi hakuri idan na tafi zan dinga zagayowa kodan saboda ke, yanzu ma abinda yasa na yadda zan bishi saboda ciwon kafar nan nawa ya takuraman ko bacci ban iyawa duba kiga yadda kafar ta yi."
Hawaye ne suka wanke ma Hafsatu fuska,"yanzu shikenan mun..rabu Baba? "
Girgiza kai Baba Yalwa ta yi,"Bamu rabu ba Hafsatu zan dinga zagayowa duba ki,in kuma nasamu lafiya ma shikenan sai in dawowata."
Kuka ne ya kubcema Hafsatu na tausayin kan ta, dama nan take rab'awa taji sanyi gashi nan ita kuma tafiya zata yi ina zata saka rayuwar ta ne yanzu?
Girgiza kai Baba Yalwa ta yi ta naji kamar ta fasa tafiyar amma babu yadda zata yi tunda har ya riga yazo dan haka ta kwantar da murya," kiyi hakuri Hafsatu duk inda kike kada ki manta Allah yana tare dake shi zai kawo maki dauki."
Jinjina kai Hafsatu tayi cikin tausayin rayuwar da za ta fuskanta nan gaba, amma ta san Allah yana tare da ita, lallashin ta Baba Yalwa ta yi da kyar tasamu ta yi shiru,kudi masu yawa Baba Yalwa ta ba ta sun kai naira dubu ukku akan ta rinka dauka tana cin abinci in aka hana ta.
Gida Hafsatu ta koma lokacin har Inna Asibi ta dawo, tana shiga tana kuka Inna Asibi tabi ta da kallo har ta shige d'akin ta, nan ta dasa wani sabon kukan.
Inna Asibi ta dad'e tana kallon d'akin kafin ta mike tsaye tabi bayan ta, labilen d'akin ta daga tace,"ke lafiya zaki shigoman da kuka? "
Dagowa Hafsatu ta yi tana kallon Inna Asibi dake rike da labile har sannan " Baba Yalwa za ta bar garin nan."
Ita ma Inna Asibi taji ba dad'i amma sai ta dake " dan Yalwa zata bar garin nan shine kike rusa kuka wato abokiyar munafurcin taki zata bar gari ina zata koma ne? "
"Maraya zasu koma ita da d'an ta dake chan," Hafsatu ta fada tana mai kara fashewa da kuka.
Tabe baki Inna Asibi tayi sannan ta juya ta bar bakin kofar d'akin, ita ma ji take yi ba dad'i da Yalwa zata bar gari, shekara fin talatin suna tare amma yau za ta bar garin, hakanan dai ta daure ta ki nuna abin ya dame ta.
Da dare kuma d'an Baba Yalwa yazo da mota babu ba ta lokaci aka fara fitowa da kayan Baba ana sanyawa cikin boat din Motar, jin tsayawar mota ya sanya Inna Asibi da Hafsatu suka fito dan ganin tafiyar ta.
Sun tadda mutane da yawa kofar gidan ana jiran tafiyar Baba Yalwa, ana gama loda kayan cikin Mota, tazo tana sallama da mutane da suka taru dan ganin tafiyar ta.
Tana zuwa gurin Hafsatu sai kawai suka rungume juna suka kama kuka, da kyar aka samu aka raba su, nan Baba Yalwa ta shige mota ko juyowa bata yi ba, itama Hafsatu da gudu ta fada gida tana sakin kuka.
Hussy Saniey.🥰
YOU ARE READING
UƘUBA
AventureLabarin wata yarinyane mai suna Hafsatu wadda ta tashi a hannun mariƙiyarta sanadiyar tsintar ta da aka yi inda ta sha wahalar rayuwa sosai kafin daga baya ta hɗu da iyayenta