Page 31&32

16 2 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan na kasa_*

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*

*Page 31&32*

Motar Asibiti na iso wa aka ɗauki gawar matar da har yanzu babu wanda ya san sunanta, ana shirin sanya Hajiya Asiya cikin Motar Asibiti sai ga Mijinta,cikin sauri ya sallami mai Taxi ɗin da ya kawo shi,bayan Ambulance ɗin ya bi har Asibiti, Emergency aka shiga dasu,taimakon gaggawa aka ba Hajiya Asiya,an yi gwaje-gwaje akan gawar matar nan suka gano ciwon Cancer ne ya kasheta,inda ake ajiyar gawa aka kaita aka aje.
Hajiya Asiya tana farfaɗowa ta rinƙa kuka mai tsuma zuciya,ji take kamar zuciyarta za ta faso kirjinta ta fito,tana cikin kukan aka turo ƙofa aka shigo,jin ƙamshin turaren wanda ya shigo shi ne ya sanar mata da ko waye, ɗagowa ta yi ta kalle shi ta ce,"Sai da na faɗa maka yarinyata ba ta mutu ba,ku ka ƙaryata ni ga shi yau an tabbatar man da gaskiyar al'amarin."
Cikin sauri har yana harɗewa da rigar jikinsa ya ƙaraso in da take ya ce,"ban fahimta ba ki yi man bayani ta yarda zan fahimta!"
"Wannnan gurguwar da na ke faɗama ka tana kallona akan hanyar dawowa daga Masallaci,ashe ba kowa ba ce baƙuwar da ta zo wurina ba yau sai ita,kuma ita ce aka haɗa baki da ita aka sace man Ɗiya!" Ta ƙarasa maganarta cikin wani irin yanayi na ƙunar rai,kallonta ya rinƙa yi har sai da ya ji ta yi shiru kafin ya ce,"yanzu ina matar?"
Hannu ta sanya ta share shawayen da ke zuba akan fuskarta ta ce,"ina tunanin fa ta mutu muna cikin magana ta fara aman jini daga ƙarshe ma ta faɗo daga kan kekenta."
"Ba ri naje na duba halin da take ciki, Allah yasa dai ba ta mutu ba,dan wallahi sai na ɗaureta!" Ya yi maganar a fusace tare da nufar hanyar fita daga ɗakin,har ya fita tana jiyo sautin faɗansa.
Ya daɗe da fita sai ga shi ya dawo jiki a saɓule,ko magana ka sa wa ya yi,da kallo ta bi shi har ya zauna,ko ba a faɗa mata ba yanayin shi kaɗai ya isa tabbatar mata da matar ta mutu,taso ace matar na da rai ko dan ta amsa mata tambayoyin dake danƙare a cikin ranta, ƙarfin halin magana ta yi ta ce,"Ta mutu koh?"
Ba tare da ya ɗago ba ya ce,"eh ta mutu har gawar sai da na gani da idanuwana."
"Yanzu sai mu wuce Nigeria tun da ta faɗaman in da zan ga ɗiyata."
Ta yi maganar hawaye na sake wanke mata fuska,babu abin da ke damunta sai kewar ɗiyarta da begen ganinta.
"Ta faɗa maki in da za a samu yarinyarmu ashe? Ina ta ce za a ganta?"
Ya faɗa tare da juyowa yana kallonta,nan ta faɗa masa yarda suka yi da matar,nan ya tashi ya fita domin nemar masu jirgin tafiya Nigeria.
Ya sha wuya sosai kafin ya samu jirgin da zai tashi ƙarfe ukku na dare,nan da awa biyar kenan, Asibitin ya koma in da ya karɓi sallama suka wuce masaukinsu,kayansu suka shiga haɗawa,nan yake faɗa mata ya samu jirgin da zai kai su Katsina,ta yi murna sosai tare da yi masa godiya dan dama abin da take son ce masa kenan,ƙarfe biyu da rabi suka nufi Airport.
Zuwansu babu daɗewa aka fara kiran suna,ko a cikin jirgin babu wata magana dake shiga tsakaninsu dan kowa da abin da ke damunshi,ko da jirgi ya saukesu a Airport ɗin Katsina,zaman jiran motocin da ya sanya a kawo ma shi suka yi,zamansu da kamar minti goma sai ga motocin sun iso,nan suka shiga kai tsaye Ƙanƙara suka nufa,duk da yaso su tsaya a wata hotel su huta amma sai Hajiya Asiya ta nuna rashin amincewa akan haka.
          ******************
Ƙwanan Inna Asibi biyu da dawowa ta kira Hafsatu har cikin ɗakinta,zaune ta isketa akan gado ta hakimce, ƙasa ta durƙusa tare da sunkuyar da kanta ƙasa,sai da Inna Asibi ta gama shan ƙamshinta lokacin ta ce,"Yau da ƙarfe biyu na rana za a ɗaura maki aure da Tasi'u na gidan Tasallah dan ha..."
Ɗagowar da Hafsatu ta yi a tamanin ita ce ta datse ma Inna Asibi magana,cikin rawar jiki da kyarmar murya Hafsatu ta ce,"Inna ki taimakeni ki yi man rai dan Allah ka da ki aura man Tasi'u,wallahi Inna shaye-shaye yake yi!"
Bugu Inna Asibi ta kai mata a baki ta ce,"Ke ji man ƴar iskar yarinya ke ba taimakonki zai yi ba? Ko da yake shaye-shaye ai yana da Iyaye ke ina na ki iyayen?"
Tamkar an doka mata guduma haka Hafsatu ta ji,maganar ta daketa sosai dan haka tsit ta yi daga kukan da take, tamkar an ɗauke wutar lantarki haka kukan ya tsaya,ba ta ƙara magana ba ta tashi ta fito daga cikin ɗakin, ɗakinta ta koma ta zauna tare da buga uban tagumi,abin duniya duk ya dameta duk wulaƙancin da Inna Asibi ke mata,ba ta taɓa yi mata gorin ina iyayenta suke ba,sai dai ta ce mata ƴar tsintuwa dan haka abin ya tsaya mata a rai.
Bayan fitarta daga cikin ɗakin Inna Asibi ta yi shiru,sai kuma ta ji ba ta ji daɗin maganar da ta yi ma Hafsatu ba,ko dai a fasa wannan auren?dan har cikin zuciyarta tana son Hafsatu duk abin da take mata ƙawarta ce ke zugata.
Hafsatu haɗa kayanta ta yi tare da kayan jariran da Malam ya bata,leƙowa ta yi tsakar gidan ta ga babu kowa sai ta nufi hanyar waje,tafiya take tana kuka ta yi alƙawarin sai ta gano iyayenta,hanyar fita daga garinsu ta yi tana tafiya amma ko gabanta ba ta gani,ta yi nisa da tafiya kawai ta ji an yi sama da ita an maido ƙasa, ƙara guda ta yi sai kuma ta faɗi ƙasa a sume,kayanta suka warwatse akan hanya.

Hussy Saniey.🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now