Page 37&38

12 0 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan na kasa_*

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*

*PAGE 37&38*

Sakin baki Hafsatu ta yi tana kallon matar da ta rungumeta tamkar tana gudun a rabasu,tunaninta ya yanke ne lokacin da ta ji muryar Inna Asibi tana ce wa,"Hajiya dan Allah ku yi man rai wallahi ina son Hafsatu sharrin Tasallah ne ita ta rinƙa zugani akan kar na jawota jikina wata rana tana iya kasheni ta gudu!"
"Inna su waye waɗannan mutanen daga ina suke?"
Hafsatu ta yi tambayar tana kallon fuskar Inna Asibi da ke ta share hawayen fuskarta.
Cikin muryar kuka Inna Asibi ta ce,"Hafsatu wannan mutanen iyayenki ne daga birni suka zo nemanki."
Cikin tsananin faɗuwar gaba Hafsatu ta rinƙa kallon matar da aka kira da sunan mahaifiyarta da kallo,wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta ko a yanzu Allah ya ɗauki ranta ta gode masa,tuna ƴar da ita kuma da matar ta yi yasa ta ji wani ɓacin rai mai tsanani ya ziyarceta,janye jikinta ta yi a hankali daga na matar ta juya mata baya,cikin rawar jiki Hajiya Asiya ta sanya hannuwanta biyu ta juyo da Hafsatu amma Hafsatu ta ƙi kallonta,har taune halshe Hajiya Asiya ke yi wurin magana ta ce,"ki juyo ki kalleni ɗiyata ni ce mahaifiyarki!!"
Idanunawa a rufe Hafsatu ta ce," ban buƙatarki a kusa dani saboda ba ki sona ba ki ƙaunata,dan haka nima ban sonki ko kaɗan ki matsa da..."
Maganarta ta datse ne saboda toshe mata baki da Hajiya Asiya ta yi,runtse idanuwanta Hajiya Asiya ta yi hawaye na zuba tamkar an buɗe famfo, ko damuwa ba ta yi ba akan ta share hawayen sai ma zagayowa ta yi inda fuskar Hafsatu ke kallo ta ce,"wannan kalmar da kika jefeni da ita tafi komai firgitar da ni fiye da halin da na shiga a baya,na kasa bacci saboda tunaninki duk duniya babu wanda ke maku soyayya ƙwatanƙwacin wadda na ke maki,ni fa mahaifiyarki ce!!"
Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da wani matsanancin kuka ta ƙara ƙanƙame Hafsatu a jikinta.
Matsowa Alhaji ya yi har inda suke ya dafa kafaɗar Hajiya Asiya,ɗagowa ta yi ta kalle shi da idanuwanta da suka yi jawur,kafin ya yi magana ta riga shi ta hanyar ce wa,"Alhaji ka ji abin da take faɗa ko? Dan Allah ka fadamata irin halin da na shiga ta sanadiyyar rashin ganinta!"
Girgiza mata kai ya yi sai kuma ya ɗora hannu a bakinsa alamar ta yi shiru,hannu ta sanya ta toshe bakinta,alama ya yi mata da matsa masa,babu musu kuwa ta miƙe daga inda take zaune,zama ya yi tare da kallon fuskar Hafsatu da har lokacin idanuwanta a rufe suke,hannu ya sanya ya jawota jikinsa,wata wawuyar ajiyar zuciya suka saki a kusan tare,shi kansa kallo ɗaya yai ma yarinyar ya amince da jininsa ta ce,duk da kamannin Hajiya Asiya ta ɗauko amma kallo guda za ka yi mata kasan ce wa jininsa ce dan murmushinta da yanayin kallonta duk kalar na babbar yayarsa ce Hajiya Umma.
"A kowa ne yanayi su mahaifa ba a faɗa masu magana ba a tauna ba, wannan mahaifiyarki ce duk duniya kowa ya yarda kin mutu amma ita duk da gawar da aka bamu ta kasa amince ma zuciyarta ce wa kin mutu,ko bacci ba ta iya yi saboda tunaninki..."
"Amma tana sona me yasa ta yarda ni? Na tashi cikin rashin gata na sha wahalhalu a rayuwata sosai me yasa ba tazo ta ɗauke ni ba?"
Hafsatu ta faɗa tare da tsare shi da idanuwa,muskutawa ya yi cikin taushin murya ya ce,"an ɗauke ki daga gabanta a lokacin da ko hayyacinta ba ta dawo ba daga haihuwarki,duk tsawon shekarun nan ba ta iya bacci sosai saboda tunaninki,mutane da yawa na mata kallon ta hauka ce saboda wata gawar da aka bamu a asibiti akan ce wa abin da ta haifa ya rasu,nan take ta musa akan wannan ba jaririnta ba ne amma babu wanda ya saurareta, mutane da yawa na mata kallon mai taɓin hankali amma ba ta taɓa damuwa ba,ni kaina da na ke mahaifinki ina mata kallon wadda ta samu matsala a kai, kullum maganarta ɗaya kenan ɗiyarta."
Nan fa ya bata labarin da wannan gurguwar ta basu a Saudiyya,hawaye ne ke ta zuba a fuskar Hafsatu na tausayin mahaifiyarta, hannu Hafsatu ta miƙawa Hajiya Asiya babu musu kuwa ta taho nan take suka rungume juna suna kuka, Inna Asibi kanta ta tausayama Hajiya Asiya dan haka ta gyara zama ta ce.
"Kamar yarda ku ka ji sunana Asibi ni haifaffiyar nan garin ce,nayi aure da mijina shekara arba'in da suka wuce amma har Allah yai ma mijina rasuwa bamu samu haihuwa ba,tun muna damuwa har dai muka ɗauki dangana muka sanya ma ranmu dan ganin yadda shekaru suka ja bamu samu haihuwar ba,bayan aurenmu da shekara ashirin wata rana da asuba Malam ya tafi gewayar gonarsa a chan wajen gari,bai daɗe da tafiya ba sai ga shi ya dawo da jaririya na ta tsala kuka,cikin rawar jiki na karɓeta daga hannunsa ban tsaya tambayarsa ba ganin yadda yarinyar ke kuka yasa na nufi wurin dabbobi na tatso mata nonon akuya,gefe na zauna na fara bata madarar, sai a lokacin Malam ke sanar da ni tsintota ya yi akan hanyarsa ta zuwa gonar,nan muka yanke shawarar kai jaririyar gidan maigari,sai da na yi mata wanka na giya lokacin muka tafi gidan maigari,nan Malam ya sanar da maigari da komai,nan aka jinjina wannan al'amari sosai,nan Malam ya roƙi alfarmar a bar masa jaririyar babu musu kuwa aka amince,nan muka dawo muka cigaba da rainon jaririyarmu wadda aka sanya ma suna Hafsatu,wanka da ruwan zafi nayi na sha ƙaiƙai nan da nan kuwa ruwan nono yazo,a haka na rinƙa rainon Hafsatu har ta kai shekara sha biyar,na ɗauki gurin duniya na ɗora akan Hafsatu ko yara suka bugeta har gida na ke zuwa na kai kashedi, anan ne na haɗu da ƙawata Tasallah,ganin yadda na ke son Hafsatu yasa Tasallah ta fara yi man muguwar huɗuba wai idan Hafsatu ta girma tana iya kasheni wannan tsoron yasa na rinƙa azabtar da ita,kullum cikin turani Tasallah take akan wai na sanya Hafsatu ta rinƙa jin tsorona,da wannan na rinƙa azabtar da Hafsatu sosai ko wannan auren ma Tasallah ta shirya mana shi dan ganin ɗanta ya rasa matar aure duk ƙauyenmu,dan Allah ku gafarceni na tuba dan Allah."
Kuka Inna Asibi ta rinƙa yi,lallashinta suka yi har ta yi shiru,nan Alhaji ya amso masu sallama dan yau suke son komawa garinsu dan su nuna Hafsatu,kaya suka haɗa yana dawowa suka ɗauki hanya.

Hussy Saniey.🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now