*بسم الله الرحمن الرحيم*
*🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_Dumin shiga shafin,mu na Bakandamiya dana shudin rubutun nan na kasa_*
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________**Page 27&28*
Inna Asibi ba ta dawo daga tafiyar da ta yi ba sai da ta yi ƙwana ukku,wurin la'asar sakaliya sai ga ta tamkar wadda aka tillo,ta yi wujiga-wujiga kallo ɗaya za ka yi mata kasan a matuƙar galabaice take,Hafsatu ta gaza motsawa daga in da take zaune sai dai ta rinƙa bin ta da kallo, Inna Asibi ba ta lura da kallon da Hafsatu ke bin ta dashi ba har sai da ta zauna akan tabarmar da Hafsatu ta tashi daga kanta,ƙwala ma ta kira ta yi,jin Hafsatu ta amsa daga kusa da ita yasa ta juyawa tana kallonta,harara Inna Asibi ta watsama Hafsatu sai ta ce,"Za ki iya ban ruwa na sha ko sai kin gama ƙareman kallo?"
Ba tare da Hafsatu ta ce komai ba ta miƙe,ruwan ta kawo mata cikin kofin ƙwano ruwan sun yi sanyi ƙarara,tun da Inna Asibi ta ka fa kofin a baki ba ta ɗauke ba sai da ta shanye ruwan tas,ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,sai kuma ta jirkice nan kan tabarmar, ƙwanciyarta babu daɗewa bacci ya yi awon gaba da ita.
Ganin ta yi bacci yasa Hafsatu tashi ta nufi kitchen dan ɗoramasu sanwar abincin dare,da sauri take aikin dan so take ta gama kafin Inna Asibi ta tashi daga wanchan baccin da ta ƙwanta,makaroni da wake ta ɗora (duk da kasancewar a ƙauye suke sosai amma cimar ƴan Birni suke,dan Inna Asibi akwai cin daɗi ba ta banzar cima,shi yasa duk da Hafsatu tana rayuwa a ƙauye ba ka taɓa cewa a nan take rayuwa ba.)
Lokacin da aka kira sallar magrib har ta kusa gamawa,har ta gama sallah ta sauke sanwar da ta ɗora Inna Asibi ba ta tashi daga baccin ba,tana son tashinta amma dole ta haƙura saboda ta san abin da zai iya biyo baya,sanya abincin ta yi cikin wata kula da suke zuba abinci,dai-dai wanda za ta ci ta zuba ta koma ƙofar ɗakinta ta zauna,ko da ta gama cin abincin sai ta yi alwallah sallar isha'i,kular abincin ta ɗauka ta kai ma Inna Asibi gefe tabarma ta aje,kofi taje ta ciko da ruwa ta kawo ta aje gefen kular, ɗakinta ta shige ta shimfiɗa kallabinta ta gabatar da sallah,ko da ta gama Azkar ta zauna tana yi,ba ta san lokacin da bacci ya ɗauketa ba anan zaunen.
Sai wurin ƙarfe tara na dare Inna Asibi ta farka da wata mahaukaciyar yunwa, kuskure bakinta kawai ta yi ta hau cin abinci, idanuwanta har lokacin cike suke da bacci dan haka tana gamawa ta tura ƙyauren gidansu sannan ta shige ɗakinta.
*******************
Bayan ƙwana biyu da yi ma Asiya magana jirginsu ya ɗaga ƙasa mai tsarki,baccin gajiya suka yi a ranar da suka sauka,washe garin ranar kuma Alhaji ya fita gabatar da harkokin da suka kawoshi ƙasar,da wannan damar Asiya ta yi amfani wurin ƙara kusanta kanta da Ubangiji kullum idan ta fita daga gida sai dare take dawowa,tun da ta fara zuwa Masallaci sai ya kasance ba ta da wani abin yi kullum cikin addu'a take akan Allah ya bayyana mata ƴarta,tana ji a ranta yarinyarta na da rai dan har yanzu ta ka sa yarda wai mutuwa ta yi.
Yau ma kamar kullum tana zaune a Masallaci tana karatun Alkur'ani,ba ta ankara ba wani bacci ya yi gaba da ita,mafarki ta fara na wata yarinya mai kama da ita tamkar an tsaga kara,tun daga nesa ta hango yarinyar ta nufo in da take sai murmushi take,ita kuma cikin wani yanayi na shauƙi ta rinƙa miƙa mata hannu alamar ta zo,sai da yarinyar ta kusa isowa in da take kawai ta farka,shiru ta yi tana tuna mafarkin da ta yi,har aka yi sallar la'asar ta kasa ci gaba da karatun dan haka ta yanke shawarar komawa masauki,akan hanyarta ta komawa masaukinsu dan babu nisa shi yasa take takawa da ƙafa,tana cikin tafiya sai ta ga wata gurguwa a gefe zaune cikin keke tana bara,har za ta wuce sai kuma ta dawo baya nufi wurin gurguwar dan ta bata sadaka,tun da ta tunkaro matar sai ta ga matar ta kafeta da idanuwa,har ta bata sadaka ta juya matar na bin ta da kallo,ta yi nisa da wurin matar sosai ta juyo amma ga mamakinta har zuwa lokacin kallonta matar take yi,nan tsoro ya kamata sauri ta kara yi,har taje masauki ta kwanta abubuwan da ta gani a mafarki da irin kallon da matar nan ta rinƙa bin ta da shi ya kasa barin zuciyarta,yau dai haka nan ta wuni tamkar marar lafiya,dan har lokacin da Mijinta ya dawo sai da ya tambayi meke damunta,nan ta ba shi labarin duk abin da ya faru, addu'a aka. Allah ya bayyanar masu da alkhairin dake ciki ya yi,nan yai ta ƙwantar mata da hankali har sai da ta samu natsuwa.Hussy Saniey.🥰
YOU ARE READING
UƘUBA
AdventureLabarin wata yarinyane mai suna Hafsatu wadda ta tashi a hannun mariƙiyarta sanadiyar tsintar ta da aka yi inda ta sha wahalar rayuwa sosai kafin daga baya ta hɗu da iyayenta