Page 23&24

14 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan_*

*_ ASSALAMU ALAIKUM MY FANS DAN ALLAH KUYI HAKURI DA JINA SHIRU KUN SAN DAI YANAYIN JIKIN NE,SANNAN ZAKU GA NA CHANZA MA LITTAFIN SUNA YA KOMA UƘUBA HAKAN YA FARUNE SABODA WANI BOOK DA NAGANI MAI IRIN SUNAN SABODA KU RARRAƁE YASA NA CHANZA MA NAWA SUNA DA FATAN ZAKU FAHIMCENI NAGODE_*

23&24

Tana idar da sallah ta fiddo tabarma tsakar gidan ta shinfiɗa,koma wa ɗaki ta yi ta ɗauko littafinta na ƙawa'idi,ta dawo gurin da ta shinfiɗa tabarma ta zauna,buɗewa ta yi ta na ƙara dubawa,ta daɗe zaune sannan aka kira sallar magrib,aje littafin ta yi ta nufi cikin ɗakinta dan ta yi sallah, saboda ta na da alwala.

Bayan ta idar da sallar ,ba ta tashi ba Qur'ani ta bude ta fara karatu,ba ita ta aje ba har sai da taji an tada sallar isha'i,mikewa ta yi ta kabbara, bayan ta idar da sallar ta daɗe zaune ta na addu'a duk rabin addu'ar ta na yin ta ne saboda Allah ya haɗata da iyayenta.

Ta na gamawa ta cire hijab ɗin jikinta,sannan ta fito tsakar gidan,in da ta tashi nan ta koma ta zauna,littafinta ta ɗauka ta ci gaba da dubawa,amma kuma rabin hankalinta ya koma kan Inna Asibi, saboda duk tafiyar da take yi in dai akai magrib to zaka ganta ta dawo,amma yau ga shi har anyi isha ba ta dawo ba,duk sai Hafsatu taji hankalinta ya tashi,ko ba komai Inna Asibi ta zama wani ginshiƙi ga rayuwarta.

Gaba ɗaya sai taji duk hankalinta ya ƙara tashi,ga wani tsoro da take ji kuma saboda bata saba zama cikin gidan ba ita kaɗai in dare ya yi,ga yau wata ya shiga duhu shiyasa garin ya koma kamar dare ya yi sosai.

Ta daɗe zaune cikin wannan halin,ganin babu alamun dawowar Innar ya sanyata komawa ɗakinta,har ta zauna sai kuma taji yunwa take ji dan haka ta tashi ta fito daga ɗakin,kitchen ta nufa ta dauki robar da za ta zuba abincin ciki,buɗa bokitin da ta zuba shinkafar ta yi ta ɗiba,miya ta zuba sannan ta koma gefe guda daga cikin kitchen ɗin ta zauna,nan ta fara cin abincin ta na ci ta na tunanin in da Inna Asibi ta tsaya har yanzu ba ta dawo gida ba.

Sai da ta gama cin abincin sannan ta ɗebi ruwa ta sha,ta wanke robar da ta yi amfani da ita,fitowa ta yi taje ta tura ƙyauren gidan,ɗakinta ta nufa ta je bisa tabarmar da take kwana ta zauna ta tsunduma cikin kogin tunani.

           ******************
"Assalamu Alaikum!"Assalamu Alaikum!!"Assalamu Alaikum!!!" wata mata ke kwaɗa sallama cikin falon,daga wata kofa wata yar matashiyar budurwa wadda da ganinta kasan hutu ya ratsa fatarta ta fito,kallon matar ta yi ta yamutsa kyakyawar fuskarta,cikin girman kai da izgilanci take bin matar da kallo,kafin ta nemi gurin zama cikin ɗaya daga cikin kujerun da suka ƙa wa ta falon.

Matar bin yarinyar da kallo ta yi wadda ta yi jika ma da ita,saboda ƙarantar yarinyar wadda da alama ba ta wuce shekara goma sha bakwai ba,kunnenta liƙe da earpiece da wata tabkekiyar waya a hannunta,sanye take cikin riga da wando,rigar pink ce yar ƙarama ta lafe a jikinta,kasancewar rigar ta roba shi ya ba komai na jikinta damar bayyana,wandon na jeans kuma blue ne mai hudoji,kanta kuma gashinta ne tayi donut dashi,gaban kuma ta yi mashi wani style mai kyau.

"Wai lafiya kike ta bina da kallo? haka kamar baki sanni ba!" yarinyar ta faɗa cikin yanayi biyu na tambaya kuma ta karashe da jin haushi.

Girgiza kai matar ta yi cikin sanyin murya ta ce,"kiyi hakuri Hajiya dama Talatu tace kin ce nazo zaki aikeni."

Ya mutsa fuska yarinyar ta yi sannan ta mai da kanta bisa screen ɗin wayarta,ta ɗauki kimanin minti ashirin kamar ba za tace komai ba sai kuma ta ɗago kai ta kalli matar da ke tsaye ta na jiran umarni,"kije kice ma Sule driver ya kai ki gidansu Besty zaki amso man saƙo gurinta."

Jinjina kai matar tayi cikin mamakin abin da yarinyar nan ke mata,duk da ba sabon abu bane gurinta na aikenta da take yi duk inda ta gadama,ba ta duba ga shekarun matar ko kaɗan ita dai abin da ta sa ni yar aiki aka ɗauko ma ta kuma biyanta ake yi.

"To shikenan hajiya bari na tafi."

Har ta juya ta fara tafiya yarinyar ta ƙwala ma ta kira"kinga Asabe kuma kada kije kiyi masu kidahumanci a gida dan nasan halinki."

Kamar saukar aradu haka matar taji wannan maganar,kamar ta mai da ma yarinyar amsar maganar da ta yi mata sai kuma ta ga ko ta mai da ita ce a ƙasa kenan babu riba, babu yadda ta iya dole ta haɗe maganganunta.

"Shikenan Hajiya zan kiyaye" ta faɗa ta na mai fita daga falon ta na share hawayen fuskarta.

Tsoki yarinyar ta ja mai tsawo kamar zata cire bakinta,wata mata doguwa baƙa bata da kyawun fuska ko kaɗan amma kasancewar gayu ya kama mata jiki yasa kallo ɗaya zaka ga kyanta, yar dattijuwace wadda ba zata wuce shekara hamsin ba,ta fito daga wata ƙofa jikinta sanye cikin wani ɗanyen lace mai ruwan ganye,ɗinkin riga da zani ta sha  ɗaurin kallabi tamkar wata budurwa,wuyanta da hannuwanta gwala-gwalai ne ke ta walwali.

Taku take cike da isa da kasaita,kai da ganin yadda take takun kasan macece wadda ta yadda da kanta,ga uban ƙamshi dake tashi daga jikinta,zama tayi bisa doguwar kujerar da yarinyar take zaune.

Kallon yarinyar tayi ta ce.
"Lafiya Auta nake ta jiyo muryarki daga ɗaki kina ta hayaniya ke da wa kuma?"

Shagwabe fuska yarinyar ta yi ta matso sosai kusa da matar,kanta ta dora bisa kafaɗar matar kafin ta ƙara narkar da murya.
"Momcy ni da waccan banzar Asaben mana dan zan aiketa gidansu Besty ta karboman saƙo,shine tai ta sa ni hayani."

Maimakon matar ta yi mata faɗa kan abin da tayi A'a sai ma ta ce.
"Ki daina biye ma ta kina hayaniya kada kanki yayi ciwo,ni ban ga abin da yasa Alhaji liƙewa ba kan ba'a korar ta daga gidan nan ba?"
ta karasa maganar da sigar tambaya.

Tabe baki ɗiyar ta yi kafin tace,"Ai shi Dady wallahi wani lokaci bakauye ne ya ƙi wayewa hakanan kum..."saurin daɗe mata baki matar ta yi dan gudun kada ta karasa abin da tayi niyyar faɗa.

"Kina haukane idan tsautsayi yasa yaji abin da kika faɗa fa?mekike tunanin zai faru idan yaji?" ta karasa tana tambayar yarinyar.

Dafe gaba yarinyar tayi tare da fiddo kananun idanuwanta,kafin ta waiwaiga ko ina sannan ta juyo ta kalli uwar,"Wallahi mantawa nayi a inda muke,in da yaji ai da na bani Allah kaɗai yasan abin da zai yi man kilama yace ya fasa kai ni waje karatun."

"Shiyasa nake ƙara nuna maki ki kiyaye bakin ki saboda kin dai san Alhaji baya ɗaukar shiririta,bake ba ko ni bai ragamawa dan haka ki san abin da kike yi"ta faɗa ta na mikewa tsaye dan komawa ɗaki.

Mikewa yarinyar tayi tace.
"Kinga Momcy nima tashi zanyi ka da ya shigo kuma ya samu abin da zai ce nayi."

Gaba daya suka fara tafiya kowacce ta nufi ɗakinta ,dan yin hidimar gabanta ,ita yarinyar tsoro yasa ta tashi,saboda duk iskancinta ta na tsoron Dadynta saboda ta san bai ɗaukar iskanci.

Hussy Saniey.🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now