Page 5&6

18 2 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan_*

5&6

"Wallahi yau sai dai uwar ki ta haifi wata, " ya fada yana mai tsaro wata sharbebiyar wuka daga kugun shi.

Runtse idanuwa tayi ta sadakar da rayuwa ita dai yau, kamar daga sama taji ya saki wata razananniyar kara, saurin bude idanuwan ta tayi dan ganin abinda ke faruwa, ganin shi tayi kwance kasa jini ya wanke mashi fuska, cikin sauri ta mike tana waige-waige dan son ganin abinda ya haddasa mashi ciwon dake kan shi.

Tana juyawa bangaren hannun ta na dama, sai taga wani maharbi tsaye da  kwari da baka da hannun shi, da alama shi ya harbe shi, inda take ya nufo kai tsaye, yana zuwa yaga yadda jikin ta yake bude sai ya ciro rigar shi ta sama ya mika mata, sai sannan ta tuna da cewa jikin ta mude yake, saurin amsa tayi ta sunkuyar da kan ta kasa cikin jin kunya.

"Ki sauri ki bar nan saboda tsayuwar ki akwai hadari nan gurin, wai mema ya hadaki da wannan har yake niyyar keta maki mutunci? " cewar wannan maharbin.

"Daga kasuwa nake na siyo gero, suka tareni shida yan uwan shi, " nan take ta bashi labarin duk abinda ya faru tsakaninta dasu.

Girgiza kai yayi yana mai matukar tausaya mata "kiyi hakuri ki tashi muje nara kaki har gidan ku, zan yima Innar ki bayanin abinda ya faru, yanzu ina geron da kika siyo," ya karasa maganar da fara waige-waige.

Ita wallahi sam tama manta da maganar gero, sai yanzu daya tambaye ta, gaban ta yai wata wawuyar faduwa tare dajin wani mahaukacin tsoro ya ziyarce ta, tasan yau mai raba ta da Inna Asibi sai Allah.

"Nima bansan inda yake ba tun sadda suka tareni kan hanya ya fadi," ta fada wasu sababin hawaye na wanke mata fuska.

"To shikenan muje mu gani ko za'a dace har yanzu in yana nan gurin, " ya gayama ta cikin sanyin murya ganin ta kara gigicewa fiye da farko.

Murmushin karfin hali ta saki,kafin ta nuna mashi hanyar da zasu bi, tana gaba yana biye da ita har zuwa gurin amma babu komai gurin, dama ba tayi tunanin samun shi ba, saboda yanzu rana har tayi sanyi sosai kuma tasan mutane na bin hanyar sosai tunda marece yayi.

"Kar ki damu kan ki zanyi ma iyayen ki bayanin abinda ya faru yadda zasu fahimta," ya fada ganin yadda ta shiga cikin tashin hankali.

Daga mashi kai kawai tayi dan kada yaga kamar ba taji abinda ya gayamata ba, amma tasan halin Inna bata hada kudin ta da komai ba,juyawa tayi ta kama hanyar gida tana gaba yana biye da ita, duk inda suka wuce kallon su ake yi kamar ranar aka fara ganin ta cikin kauyen.

Tunda ta shawo kwanar da zata sadata da gidan su, kirjin ta ke wani mahaukacin bugu, dauriya kawai take yi amma ko kafafun ta da kyar take daga su,bakin kofar gidan su taja tunga tana nuna mashi kofar.

"Nanne gidan," ta fada tana sunkuyar da kan ta kasa gudun kada ya fuskanci halin da take ciki.

"Ki shiga ki gayamasu ina sallama," ya fada mata.

Shiga tayi gidan kasancewar babu zaure gidan yasa tana shiga sai gata tsakar gidan, cikin karfin hali tare da juriya ta bude bakin ta tayi sallama, kamar jira Inna Asibi take yi tayi magana, sai gata kamar an tillo ta waje, tana fitowa ta dinga karema Hafsatu kallo kamar yau ta fara ganin ta.

Shan jinin jikin ta Hafsatu tayi da irin kallon da take bin ta dashi, cikin karfin hali Hafsatu ta bude bakin ta"Inna ana sallama dake kofar gida," ta fada don san katse mata wannan kallon kurillar da take bin ta dashi.

"Ina gero na dai yanzu, kuma waye ke sallama dani," ta fada tana kara tsare ta da mitsi-mitsin idanuwan ta.

Numfashin Hafsatu ne ya kusa daukewa saboda yadda ta hango tsantsar bala'i cikin idanuwan Inna Asibi, cikin karfin hali ta sake bude bakin ta" Inna jiran ki ake yi wajen," ta sake fadima Inna Asibi.

Babu musu Inna Asibi ta nufi hanyar  kofar gida, tana warware zanen data dauka bisa igiya ta yafama jikin ta, tana fita kofar gidan ta tadda wannan maharbin tsaye, binshi tayi da kallo kafin ta karasa inda yake.

"Malam lafiya kake magana dani? " ta fada tana kara bin shi da wani kaskantaccen kallo.

"Lafiya lau dama game da yarinyar wajan kine dana taimaka daga hannun wani azzalumi. "

"To sai akai yaya kenan? " cewar Inna Asibi tana kara bin shi da kallo.

Beyi kasa a guiwa ba ya zayyane mata dukkan abinda yafaru ya gayamata, sai daya kai karshe kana ta zunduma wani mahaukacin ashar ta nufi cikin gida da gudu.

Kuyi hakuri ina maku typing kadan wlh banda lokaci ko kadan ne hakanan nake

Hussy Saniey🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now