Page 21&22

15 2 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan_*

_*WANNAN SHAFIN NAKI NE MOMYN AHALAN KIYI YADDA KIKE SO DASHI_*

21&22

الشيباني-واسمه سعد بن*_ اياس-قال: حدثني صاحب هذه الدار.
Daga Baban Umar da shaybani ko kuma Sa'adu bin iyas yace,:Mai wan chan gidan ya bani labari.
واشاربيده الى دار عبدالله بن مسعد رضي الله عنه.
Sai yayi nuni da gidan Abdullahi d'an mas'ud Allah ya karamashi yarda.
قال-سالت النبي صلى عليه ؤسلم.
Na tambayi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi.
اي لاءعمال احب الله ؟ 
Wane ayyukane Allah yafiso?
قال- الصلاة على وقتاح.   
Sallah akan lokacinta.
قلت :ثم اي؟Sai nace sai kuma me?
قال: برالوالدين. Yi ma iyaye biyayya.
قلت :ثم اي? Sai nace sai kuma me?.
الجهادفي سبيل الله. Jihadi saboda Allah.
قال:
Sai yace.
حدثني بهن رسلول الله صلى الله عليه وسلم.
Sai manzo ya bashi labashi labari.
ولواستزدته لزادني.
Da kuma na nemi ya karaman wani ilimin da ya karaman_*.

         ***************
Kasancewar ta sha aiki,shiyasa ta na kwanciya bacci mai nauyi ya k'washeta,ba ita ta farka ba sai gurin karfe biyar na yamma, da addu'a d'auke a bakinta ta tashi, tayi mamakin irin baccin da ta yi, ita da ta k'wanta tun biyu da rabi na rana, amma sai yanzu ta ke tashi, gaskiya ta sha bacci ba kad'an ba.

Kuma idan ta yi duba da irin aikin da ta sha yau sai ta ga wannan ai ba abin mamaki bane, saboda ba k'arya yau ta aikatu cikin gidan nan, dama irin haka na kasancewa duk a irin wannan ranar, saboda da wuya ranar kasuwa ta zo Inna Asibi ba ta ci nama ba,in ka ga ba ta ci nama ba to ba ta gari ko ba ta da lafiya,sai dai  ita har mamakin Innar ta ke kamar mai aljannun cin nama haka ta ke,to duk irin wannan ranar ita kuma ta na aikatuwa cikin gidan, dan ma yanzu Inna Asibi ta daina saurin dukanta.

Ko da ma can in ka ga ta na yawan bugunta to Tasallah ke yawan zuwa gidan, amma in dai ta dad'e ba ta zo ba lafiya lau suke rayuwarsu, to duk ranar da ta zo kuma sai Allah saboda sai ta haddasa rigimar da sai ta fi wata tana cin UƘUBAR had'in da Tasallah ta yi.

Har ga Allah ita dai ta na son samun wanda zai ba ta labarin rayuwarta, da yadda akai ta zo gidan ko za ta samu hanyar nemo iyayenta, taso k'warai Baba Yalwa ta ba ta labarin rayuwarta amma sai gashi hakan ba ta samu ba har Baba Yalwa ta bar garin ba ta bata labarin ba.

O'h yanzu ko wa zai rink'a tallabarta, yanzu Baba Yalwa na can birni ta na rayuwarta hankali kwance, Allah sarki Baba ta tafi ta barta a wani hali, ko sai yaushe ne za ta samu yancin rayuwa kamar kowa, wasu hawaye masu zafine su ka gangaro mata a fuska, ba ta damu da goge su ba saboda saukar su na rage mata wani k'uncin dake zuciyarta.

Sai da ta yi kuka sasai   babu mai lallashinta, ko kad'an a duniya ba ta san wani abu ba wai shi lallashi, abu d'aya ta yi wayan sani shine aba ta umarni ko a hana ta ko da hakan na nufin za ta kasance cikin damuwa babu ruwan kowa da haka, guri d'aya take samun hakan kuma shima yanzu ya yi mata nisa, ita a cikin UKUBA ta tashi ita ta sani ba ta wani san jin dad'i ba, har garama yanzu a haka tana samun sauki.

Ta d'auki lokaci mai tsawo a zaune ta na sak'a da warwara, sai lokacin ta tuna da ba ta yi sallar la'asar ba, cikin sauri ta mike tsaye ta na gyara daurin kallabinta dake niyyar kwancewa, tsakar gidan ta fito yana nan yadda ta gyareshi, buta ta dauka ta nufi band'aki ta kama ruwa, ta na fitowa ta zauna bisa dutsin da suke alwalla, ta na gama alwallar  sannan ta tashi taje ta yi sallah.

Hussy Saniey 🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now