Page 25&26

17 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan_*

*_ ASSALAMU ALAIKUM MY FANS DAN ALLAH KUYI HAKURI DA JINA SHIRU DA KU KEYI HAKAN YA FARUNE SAKAMAKON RASHIN JIN DAƊIN JIKINA DA BA NA YI_*

_*WANNAN PAGE ƊIN NAKI NE MY ƘAWALLIYA ROMAN JAƁA AISHA MUSA JIKA(Marubiciyar sai na cika burina)_*

25&26

Har Hafsatu ta yi bacci Inna Asibi ba ta dawo ba,kallo ɗaya za ka yi ma Hafsatu kasan cewa kafin baccin ya ɗauketa a tsorace ta ke sosai,duba da yadda ta duƙunƙune jikinta guri guda, da kyar ta samu har baccin ya ɗauketa,ba ita ta farka ba sai da aka ƙwala kiran Sallar farko,sabawa da ta yi na tashi a lokacin yasa har jikin ta ya saba,shiyasa yanzu ma lokacin na yi ta tashi,gaskiya sabo wani abu ne mai girma duk lokacin da kake abu da ya yi to za ka ga jikin ka ya saba,shiyasa duk irin baccin da take yi da lokacin yin sallah yayi sai ta tashi.

Dan haka yanzu ma motsawa ta fa ra yi kafin ta buɗe idanuwan ta,bisa rufin ɗakin ta sauke idanuwan ta,zuba ma izarun da aka yi rufin ɗakin dasu idanuwa ta yi ta na kallo,kamar yau ta fa ra ganinsu.

Ta na tuna yadda ta samu bacci ya ɗauke ta,ko ina Inna Asibi ta tafi jiya har ta yo dare haka? ko da yaushe ta dawo? Ita dai tasan har bacci ya ɗauke ta ba ta ji motsin dawowar Innar ba ko kaɗan.

Tashi ta yi zaune ta na miƙe hannun ta na haggu da ya yi ma ta sanyi,da alama kwanta shi ta yi ba ta juya ba,ta daɗe ta na jan hannun sannan ta miƙe tsaye jin wasu masallatan sun fa ra kiran sallah.

Tsakar gidan ta fito ta yi tsaye,ƙofar ɗakin Inna Asibi ta kalla,yana nan yadda yake da  ƙwaɗo a jiki alamar ba ta dawo ba kenan,shiru Hafsatu ta yi ta na tunanin in da Inna Asibi ta je jiya take, saboda ko kaɗan Inna Asibi ba al'adarta ba ce ta yi tafiya ta kwana, komin dare dai za ka ganta ta dawo gida,amma yau ga shi babu ita babu alamar ta.

Ganin tsayuwar ba ta da amfani yasa Hafsatu duƙawa ta ɗauki buta ta shiga banɗaki,ruwa ta kama ba ta daɗe ba ta fito, ta na fitowa zama ta yi saman Dutsin da suke zama idan za su yi Alwala,nan ita ma ta zauna,tana gama wa ta koma cikin ɗakin ta,abin Sallah ta shinfiɗa ta kabbara sallar,sai da ta yi Raka'atul Fijr sannan ta yi sallar Asuba.

Ta na idar da sallar,ta shi ta yi tsaye ta  cire abayar da ta yi sallar,tsakar gidan ta sake fitowa,tsintsiya ta ɗauka ta share gidan tas,sannan ta haɗa itatuwa ga murhu ta hura wuta,tukunya ta ɗora bisa wutar sannan ta zuba ruwan koko.

Kayan wanke-wanke ta kwaso duk da basu da yawa shaf-shaf ta gama,kwashesu ta yi ta maida kayan inda suke ajesu,ƙullun kokon ta haɗa lokacin ruwan har sun tafasa,dama kokon ta yi ta rufe shi.

Sauran Abincin da aka rage jiya ta ɗauko ta ɗumama shi,ta na gamawa ta kashe wutar ta ɗauke komai ta mai da shi ma'adanar shi,share ko ina ta yi kamar ba gurin da ta yi aiki gurin ba,ɗakin ta ta koma ta fidda kayan jikinta wani zane ta ɗauro ta sanya abaya,ruwa ta ɗiba cikin bokitin wanka ta shiga kewaye.

Cikin sauri ta idar da wankan saboda tasan yanzu an fara shigowa sayen koko,ba ta daɗe da fitowa ba ta na cikin ɗakinta ta na sanya kaya aka fara sallama,cikin sauri ta idar da sanyawa ta fito,nan fa akai ta shigowa ana saye babu daɗewa kuwa kokon ya ƙare,dama kokonsu shaf-shaf yake ƙarewa saboda gyara shi da take yi.

Tana gama sai da kokon ta wanke guraren,sannan ta ɗebo abinci ta zauna ta ci ta ƙoshi,ta na gamawa ta ga ruwansu ya ƙare sauran shi ne ma yanzu ta yi jiƙon gero,bokiti ta ɗauka ta rufe gidan ta tafi ɗebo ruwa,inda Allah ya taimake ta babu layi shiyasa cikin sauri ta rinƙa ɗiba.

Sai da ta cika tukanen su da robobin su da ruwa sannan ta ɗebo wani ta aje cikin bokitin,wanka ta ƙara yi sannan ta shiga ɗakin ta ta gyara shi,ta na idarwa ta kwan ta bisa tabarma ta na ƙara tunanin inda Inna Asibi taje.

Tana nan kwance ta na tunanin duniya har taji bacci take son yi,dan haka tashi ta yi taje ta tura kyauren gidan,ɗakin ta ta koma ta kwanta nan da nan bacci ya kwasheta.

         *********************

Kwance take ta na tunanin yadda rayuwa ke juya mata,ko sai yaushe ne wahalar ta za ta ƙare a duniya,ita har mamakin mutane masu sha'awar rayuwar ta take yi,da sun san yadda rayuwar ta take da basu yi sha'awar ta ba.

Mikewa ta yi ta nufi wani ƙaramin akwati ta buɗeshi,kayane irin na jarirai ta daɗe ta na kallon kayan ta na hawaye,motsi ta jiyo za'a shigo ɗakin ta shiyasa cikin sauri ta maida marfin akwatin ta rufe,ta koma inda take zaune da farko ta zauna.

Wani yaro ne ɗan kimanin shekara goma ya shigo da sallama,"Aunty haka Abba yace ki zo yana kiran ki."

Hannu Asiya ta mika ma shi alamar ya matso kusa da ita,babu musu kuwa ya ƙaraso in da take,riƙe hannunshi ta yi ta jawoshi jikin ta,ta shafa kanshi ta yi sannan ta ce,"Anwar wa ya maido ka ?"

Kwantar da kanshi yayi bisa cinyar ta ya ce,"Ni da Ya Saleem muka dawo."

"To ya ka baro Ummin ka?"

"Tana nan lafiya lau ta na gaidaki ma"ya faɗa ya na ƙara kwanciya bisa cinyarta.

"Ina amsawa sosai,ka tashi mu tafi kiran da ake man"ta faɗa ta na janyeshi daga jikin ta,hannun shi ta kama suka fito falon in da ta tadda Abba zaune yana kallon labarai a NTA.

"Assalamu Alaikum" ta faɗa murmushi shinfiɗe akan fuskar ta.

Ɗagowa ya yi daga kallon T.V ɗin da ya ke yi,ya juyo inda take saboda ya juya ma kofar ɗakin ta baya,kallon ta ya yi tare da wadata fuskarshi da murmushi ya ce,"Wa'alaikissalam Amarya bakya laifi ko kin kashe yaran masu gida,farar mace alkyabbar mata,amarya a gida na."

Dariya ta yi fuskar ta ta wadatu da fara'a har cikin ranta take jin daɗi idan Alhaji yana ma ta kirarin nan,"Kai Abban su wannan kirari haka!"

Shima dariyar ya yi sannan ya ce"ko na faɗi ba dai-dai bane Amarya ta"ya karasa yana ɗauke jaridar dake kusa dashi ya maida ta bisa center table ɗin gabanshi.

Ƙin zama ta yi kamar yadda ta fahimci yana nufi,kitchen ta shiga ta ɗauko tataccen Inibi da ta yi mashi ya yi sanyi sosai,fitowa ta yi ta iske shi ya na kallon labaran,tebur ɗin gaban shi ta gyarama takardun zama sannan ta ɗora jug da cup ɗin sama,tsiyayawa ta yi cikin cup ta miƙa mashi.

Jin be karɓa ba yasa ta ɗago kai domin ta ga meya faru,gani ta yi ya kafeta da ido ya na ta murmushi,ita ma murmushin ta yi ta ce,"Bissimillah Abban su."

"A kullum ina ƙara yi ma Allah godiya da ya azurtani da samun ki a rayuwa,lalle Manzo ya yi gaskiya da ya ce mace ta gari rabin addini ce,Allah ka azurta sauran mazaje da samun mata nagari,ko dan su ɗanɗani ni'imar duniya,"inji Alhajin.

"Ameen ya Allah ka amsa kada sanyin ya rage kuma kafi son shi da sanyi" ta faɗa ta na ƙara mika mashi cup ɗin.

Amsa ya yi ya fara sha,be aje cup ɗin ba har sai da ya shanye shi gaba ɗaya,sannan ya aje cup ɗin ƙara tsiyayawa ta yi ya ƙara shan rabin kofin sannan ya yi hamdala.

Gyara zaman shi ya yi yace"Asiya abin da yasa ki ka ji na kira ki saboda na sanar maki tafiya ce ta kamani zuwa Saudiyya shiyasa na yi tunanin ko kina da lokaci mu tafi tare?"

Ɗagowa ta yi ta kalleshi sannan ta maida kanta ƙasa ta ce,"Ni mai biyayyace akan duk abin da ka umarceni dan haka ban da zaɓi in dai abin zai faran ta maka rai,dan haka yanzu ma in dai kan  tafiyar nan ce sai dai in ce Allah ya maido mu lafiya."

Faɗaɗa fara'ar kan fuskarshi ya yi ya ce,"Nagode ma Allah da ya bani ke a matsayin mata,da ma nasan ba zan samu matsala dake ba,farko Hajiya Kaltume (yana nufin kishiyar ta babbar matar shi)nayi ma magana amma ta ce ita ba za taje Saudiyya ba sai dai in wata ƙasar zamu." ya ƙarashe maganar fara'ar fuskarshi na raguwa.

Ganin haka yasa ta chanza masu firar,dan wannan maganar ba za tayi mamakin ta ba duba da yanayin halayyar Hajiyar.

Hussy Saniey.🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now