Page 9&10

21 2 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan_*

9&10

  Bata dade da kwanciya ba wani bacci mai nauyi ya dauke ta, kasancewar gajiye take ga cikin ta yai mata tsami dan ma tayi wanka da ruwan zafi gidan Baba Yalwa, ba ita ta tashi ba sai da aka yi kiran assalatu, da kyar ta iya tashi zaune sbd yadda jikin ta ya kara yin tsami, ta dade zaune nan bisa tabarmar da take kwana, ganin ana shirin fara kiran sallah yasa ta yin karfin hali ta mike tana dafa bango, (so take tayi ruwan zafi ta kara yin wanka dashi kafin Inna ta fito dan tasan indai ta fito to yau bata da rabon yin wanka a gidan, duk da tasan ba lalle ne ta tashi ba a yanzu amma tasan duk lokacin da tai mata irin wannan bugun tana tashi da wuri saboda ta hana ta yin wanka).

Da bin bango ta samu ta fito tsakar gidan, ta dade tsaye tana karema gidan kallo yadda yai kacha-kacha, saboda jiya bata yini a gidan ba, shiyasa babu wanda zai gyara dama tasan indai bata nan Inna ba zata taba gyara gidan ba, wata barnar ma da gan-gan take yin ta dan dai gidan ya kasance da dauda asa ta gyaran shi.

Ganin tsayuwar bata da amfani yasa ta nufar gurin murhu, itace ta hada ta kunna wuta, babbar tukunyar da take dorama Inna ruwan koko ta dauko, ita ma dai babu wanki ga wani kingin koko duk ya bushe jikin ta dole ta jika ta, kafin ta jiku kuma sai ta koma ta fara tattara kayan dake baje tsakar gidan, tana yi tana girgiza kai saboda wani abun ma da keta ake yin shi, rai daya cikin gida amma gida ya koma kamar anci kasuwa cikin shi.

Sai data share gidan kal kafin ta koma gurin tukunyar data jika, cikin sa'a kuwa ta tadda ta jiku, wankewa tayi ta gyara iccen ta dora ruwan zafin, gurin data hada kayan wanke-wanke ta nufa, dukawa tayi ta cigaba da wankewa tun tana karfin hali harta galabaita sosai saboda jikin ta dake mata ciwo, hakanan dai tasamu ta gama wanke-wanken.

Tukunyar da ta dora ruwan zafin ta duba, bata tafasa ba amma sunyi zafi sosai, bokiti ta debo ta dibi ruwan ta surka da wasu na sanyi, kara ruwan tayi cikin tukunyar dake kan murhu, ta dauki ruwan wankan ta kewaye ta nufa harta sanya kafa daya ciki kamar daga sama taji an ruge bokitin hannun ta, gaban ta yai wata irin faduwa ko ba'a gayamata ba tasan ko aikin waye, dan haka babu gardama ta saki bokitin.

"Ke har kin isa kiyiman wanka cikin gida to daga yau na soke yin wanka gurin ki sai so daya a rana, shima saboda kina tabaman kayan kunu kuma kinsan bansan kazanta dan haka yau dai babu maganar wanka gurin ki, " cewar Inna Asibi dake rike da bokitin da Hafsatu za tayi wanka.

"Inna dan..., " kafin ta ida maganar da zata yi sai ji tayi an sakar mata wani bahagon mari wanda yasa jinta na sakanni ya dauke.

"Wallahi har na kara jin bakin ki nan sai nayi maki bugun da zaki suma nan gurin, " tana gama fadar haka ta tunkude bokitin ruwan ya zube gaba daya a kasa ta yadda bokitin gefe guda.

"kuma ki tabbatar kin gama man koko na kan lokaci, " cewar Inna Asibi tana gama fadin haka ta koma bakin dakin ta tayi zaune dan ma kada ta koma dakin Hafsatu ta sake dibar ruwan wankan.

Bakin murhun Hafsatu ta koma ta cigaba da iza wutar, a haka har tukunyar ta tafasa, dauko kullun kokon tayi ta gyara shi yadda zata dama, haka ta dauko tukunyar ta dama shi, tana cikin damawar Inna ta dawo kusa da ita ta zauna tana kallon abinda take yi, sai data gama damawar duka gurin gyara ma tukunyar zama da rufe marfin wani ya dan zuba kasa, mikewa Inna tayi bata ce komai ba.

Kofi ta dauko ta dibi kokon kamar zata sha, kafin Hafsatu ta ankara sai taji Inna ta wanke mata kafa dashi, wani ihun azaba ta saki ta dafe kafar ta, Inna bata ce komai ba babu tausayi a fuskar ta ko kadan juyawa tayi ta koma dakin ta, nan tsakar gidan Hafsatu tai ta kuka ga kafar na mata wani bala'in zafi, ta dade tana kuka ganin kukan be mata maganin datake ciki yasa ta mikewa, ruwan alwalla ta diba saboda dama batayi sallah ba, lokacin da aka tada sallah Inna na zaune gurin babu damar ta tashi taje tayi, hakanan ta dinga d'angyasa kafar har tayi alwallar kasa wanke kafar tayi sai dai tayi ta zuba mata ruwa.

Dakinta ta koma ta kabbara sallah sai data gama sannan ta zauna, nan inda tai sallar take jingine da bango tana jin yadda jikin ta ke ciwo ba ma kamar kafar ta, tasan wannan wutar da wuya in ba sai ya tashi ba.

Wani baccin wahala ne yai gaba da ita nan inda take zaune, tana cikin wannan baccin taji an take mata kafar ta mai wutar, wani wahalallan ihu ta saki da muryar ta da ko fita bata yi sosai, bude idanuwan ta tayi da suka chanza kala sun koma jazur saboda  bacci ga azabar da take ji dama, bisa kan Inna ta sauke idanuwan ta, wadda ke tsaye tana huci sai kace kububuwa.

"Sannu shafaffa da mai ina chan ina wahala ke kina nan kina bacci sannu yar hutu!"  Cewar Inna tana kai mata rankwashi tsakiyyar kai.

Dafe gurin tayi tana mai share hawayen idanuwan ta, "kiyi hakuri Inna kafata ke ciwo wallahi. "

"Ki tashi kije ki gyaraman gidana kije ki deboman ruwa, " cewar Inna tana mai kara kai mata bugu a baya, sannan ta sa kai tayi waje tana ta sababin ta, runtse idanuwa Hafsatu tayi tana mai kara tausayama rayuwar ta, tunda ta tashi a haka ta tsinci rayuwar ta cikin bauta ko sai yaushe zata samu yancin kan ta.

Mikewa tayi ta fita tsakar gidan wanda yayi kacha-kacha sai kace duk yau bega tsintsiya ba, tana d'angyasa kafar ta, ta fara tattara gidan nan da nan gidan yayi fes, tulu ta dauka dan debo ruwa, jinta takeyi har iska na daukar ta ga jikin ta dake ciwo ga kafar ta da ita tafi takurama ta.

Tana fita ta shige gidan Baba Yalwa, zaune ta tadda ta bisa kujera tana sauraren radiyo, da gudu ta isa inda Baba Yalwa take bisa ita ta fada ta saki wani mahaukacin kuka, kamar ranta zai fita tana jin rayuwar tayi mata kunci.

Hussy Saniey🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now