*بسم الله الرحمن الرحيم*
*🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_Dumin shiga shafin,mu na Bakandamiya dana shudin rubutun nan na kasa_*
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________**Page 33&34*
Cikin sauri Hajiya Asiya da Mijinta suka fito su ka nufi wurin da Hafsatu ke kwance tamkar matattarar,ba su ɗaya ɓata lokaci ba su ka sanyata cikin mota,duk da kasancewarsu baƙi haka suka rinƙa sharara gudu akan titi dan neman Asibitin da za su kai ta,ba su yi tafiya mai nisa ba suka haɗu da wata ƙaramar Asibiti a gefen hanya,a hankali ya rage gudu sai da yazo dai-dai get ɗin lokacin ya cilla hancin motarsa a ciki,har bakin ƙofar shiga Emergency ya kai motar,a ruɗe Hajiya Asiya ta yi cikin Emergency tana kuka,babu daɗewa ta dawo tare da wasu Nurses,kan gadon ɗaukar marasa lafiya aka ɗora Hafsatu da har lokacin ba ta farfaɗo ba.
Bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Hafsatu suka tsare, Hajiya Asiya ta kasa zama sai safa da marwa take yi,cikin tashin hankali ta kalli mijinta ta ce,"Ina tsoron yarinyar can ta mutu!"
A hankali ya taka har inda take, kafaɗunta ya riƙe tare da zaunar da ita akan kujera,gefenta ya zauna shi ma cikin kwantar da murya ya ce,"Insha Allah babu abin da zai sameta,nafi tunanin tsoratar da ta yi ce ta jawo mata suma kin ga ai ba ta bugu sosai ba."
"Duk da haka Allah tsoro nake ji,idan ta mutu ka ga ba zamu samu damar ƙarasawa garin can ba bare har na haɗu da ɗiyata,ya Allah kaine maji roƙon bawa Allah ka taƙaita man wahala ka sadani da yarinyata,ya Allah ban taɓa cutar da kowa ba ya Allah ka tausayaman ka jiɓanci lamurrana ka haɗani da farin cikina."
Hajiya Asiya ta ƙarasa addu'ar hawaye kwance akan fuskarta,jikin Mijinta ya yi sanyi ya kasa ce mata komai sai kallonta kawai da yake, tausayinta ya cika masa zuciya,ganin yarda kowa ke mata kallon mahaukaciya ashe da hankalinta,sai yanzu yake ƙara girmama girman mahaifiya ganin yarda ta haƙiƙance ƴarta na raye ashe kuwa da gaskiyarta.
Kafin ya samu zarafin yi mata magana sai ga Likita ya fito daga ɗakin da aka kwantar da Hafsatu,cikin sauri suka tare shi har suna haɗa baki wurin tambayarshi,"Likita ya jikin Patient ɗin?"
"Ku kwantar da hankalinku da sauƙi sosai bacci take yanzu," Likitan ya faɗa tare da miƙa ma Mijin Hjy Asiya takarda ya ƙara da ce wa,"Ka je ka kawo man waɗannan magungunan."
"To shi kenan Likita amma zamu iya ganinta?" Hajiya Asiya ta yi tambayar, Likitan ya maido dubanshi gareta ya ce,"A'a ku yi haƙuri ba a buƙatar motsi mai ƙarfi a kusa da ita,ku dai yi haƙuri har ta tashi."
Yana fadar haka ya nufi office ɗinsa, tafiya Mijin Hajiya Asiya ya yi domin ya siyo magungunan, Hajiya Asiya kaɗai aka bari babu abin da take cikin ranta sai addu'ar Allah ya haɗa ta da gudan jininta,ta daɗe a wannan halin har sai da Mijinta ya dawo,nan ne yake sanar da ita ya kamata su ƙarasa ƙauye kafin Patient ɗinsu ta tashi,tun da Likita ya sanar dasu za ta daɗe kafin ta farka,babu musu kuwa ta miƙe suka nufi ƙauyen.
Da tambaya aka kaisu har gidan Baba Asibi, ƙofar gidan suka aje motarsu sai Hajiya Asiya ta shiga gidan da sallama,"Assalamu Alaikum!"
Daga cikin ɗakin Inna Asibi aka amsa mata sallamar,zuwa chan sai ga Inna Asibi ta fito tsakar gidan,ganin ƴar gayu tsaye a cikin gidanta ya sanya Inna Asibi komawa cikin ɗakinta ta ɗauko sabuwar tabarma ta shimfiɗa mata,zama Hajiya Asiya ta yi tana ta kallon tsakar gidan cikin ranta tana tunanin yanzu a cikin wannan gidan wanda marabarsa da kango kaɗan ne ƴarta ta rayu a ciki,Muryar Inna Asibi ta katse mata tunani.
"Ina wuni Hajiya!"
"Lafiya lau Alhamdullih mun sameku lafiya?"
Hajiya Asiya ta faɗa tana bin gidan da kallo ta ƙagara ta ga ta inda ƴarta za ta fito.
"Lafiya lau Hajiya."
Inna Asibi ta amsa tare da mamakin daga ina baƙuwar nan take,tunawa da Inna Asibi ta yi ba ta kawo ruwa ba yasa ta ƙwalama Hafsatu kira,jin ta yi kiran sau biyar babu amsa yasa ta nufar ɗakin Hafsatu tana ce wa,"Hala wannan ƙadararren baccin kike shi yasa ina ta kira baki amsa ba?" Turus ta yi ganin Hafsatu ba ta ɗakin ga ɗakin a ɗan harmutse kamar an ɗauki wasu kayan,gabanta ya yi wata muguwar faɗuwa saboda wani tunani da ya ɗarsu a ranta,cikin sauri ta ida shiga ɗakin nan ta tabbatar Hafsatu guduwa ta yi, ƙara ta saki tare da yanke jiki ta faɗi, ƙarar da ta saki da faɗuwar yasa Hajiya Asiya biyota da gudu,ganin ta kwance a sume yasa Hajiya Asiya fita da gudu tana kururuwar neman ɗauki,nan fa mutane suka shiga gidan da gudu,fiddo Inna Asibi aka yi daga cikin ɗakin,kan tabarma aka kwantar da ita tare da yayyafa mata ruwa,ajiyar zuciya ta sauke tare da buɗe idanuwanta,ganin mutane zagaye da ita yasa ta tuna abin da ya faru kuka ta fashe da shi tare da ce wa,"Tasallah kin cuceni ga shi kin sanya Hafsatu ta gudu,na shiga ukku ni Asibi dan Allah ku nemo man Hafsatu wallahi ina sonta sosai,Tasallah ta sanyani na rinƙa gana mata azaba wai dan ta rinƙa jin tsorona in ba haka ba wata rana sai ta kasheni,yanzu kuma ta ce na tsare Hafsatu sai ta auri ɗanta shi ne Hafsatu ta gudu dan Allah ku nemo man ita ku ba ta haƙuri wallahi ba zan aura mata shi ba wayyo Allah na shiga ukku ina kika shige Hafsatu!!"
Salati mutanen wurin suka ɗauka tare da tir da halin Inna Asibi,wani tsoho ya ce,"yanzu Asibi yarinyar nan duk haƙurinta sai da kika kaita bango ta gudu? Allah ya sadata da iyayenta a tafiyar da ta yi,tun da kin gaza riƙe amanar da Malam ya bar maki."
Tsohon ya ƙarasa maganar tare da share ƙwallar da ta tarar masa a idanuwa.
"Allah ya sakama Hafsatu cutar da kika rinƙa yi mata,ita kuma Allah ya haɗa ta da iyayenta."
Wani mutumi ya faɗa tare da fita daga gidan,kuka Inna Asibi ke ta yi ta ce,"wallahi ba laifina bane Tasallah ta ce duk ɗan da aka tsinto idan ya girma ya ji ba kai ka haifeshi ba to kasheka yake shi yasa na rinƙa dukan Hafsatu amma wallahi ina sonta sosai dan Allah ku nemo man ita!"
"Wai kina nufin ɗiyata ta gudu saboda azabar da kike gana mata? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kin kasheni wallahi!"
Hajiya Asiya ta yi maganar cikin tashin hankali,ta buɗe baki ta sake magana juwa ta ƙwasheta ta yar,gaba ɗaya kanta aka yi dan bata taimako,mutane na mamakin maganar da ta yi yanzu,idan sun ji dai-dai tana nufin Hafsatu ɗiyarta ce.Hussy Saniey.🥰
YOU ARE READING
UƘUBA
AdventureLabarin wata yarinyane mai suna Hafsatu wadda ta tashi a hannun mariƙiyarta sanadiyar tsintar ta da aka yi inda ta sha wahalar rayuwa sosai kafin daga baya ta hɗu da iyayenta