*بسم الله الرحمن الرحيم*
*🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_Dumin shiga shafin,mu na Bakandamiya dana shudin rubutun nan_*
3&4
Kiran sallar farko ta farka, saboda dama lokacin ta saba tashi daga bacci, tana tashi mikewa tayi taje ta dauro alwalla ta dawo dakin tai nafilolin da suka zame mata jiki, ba ita ta tashi ba daga gurin sai da gama sallar asuba, mikewa tayi taje ta fara sharar tsakar gidan, tana gamawa ta dora ruwan kokon da Inna Asibi ke siyarwa, har lokacin babu kowa a tsakar gidan, dama ta saba har ta gama aikin ta babu wanda ke tashi.
Tana gama dama kokon ta dauko sauran tuwon jiya ta dumama shi, kwano ta dauko ta dibi wanda zata ci, in ba haka ba babu rabon ta cikin tuwon, daki tai saurin shigewa ta fara cin tuwon cikin sauri kada Inna Asibi ta fito ta tadda tana cin tuwon, cikin sa'a kuwa tana gamawa ta wanke kwanon kenan sai ga hakimar sannan ta tashi daga baccin.
Karema tsakar gidan kallo tayi daga bisani kuma ta sauke kan Hafsatu data sunkuyar da kanta kasa, ta dade tana nazartar halin da Hafsatun ke ciki, bataga komai ba amma dan neman rigima sai da tace.
"Yau kuma ko arzikin gaisuwar banda shi a gidan nan? " ta karasa tana mai kai ma Hafsatu rankwashi tsakiyar kai.
Dafe gurin Hafsatu tayi hawaye na zuba daga fuskar ta, "Au wannan dan bugun yasaki kuka aikuwa wallahi sai jikin ki ya gayamaki " cewar Inna Asibi.
Wani icce ne ta dauko kafin Hafsatu ta ankara har ta fara zuba mata shi a jiki ta ko ina, rugawa tayi da gudu zuwa dakin ta, amma duk da haka Inna Asibi bata kyaleta ba sai data bita har chan ta zane mata jiki sosai, sai data tabbatar ta bugu kafin ta yadda iccen ta fito daga cikin dakin.
Buta ta dauka ta nufi bandaki,bata dade da shiga ba sai gashi ta fito kafar ta duk jirwayen fitsarin da tayi, ruwan butar ta gumtsa ta dauraye bakin ta, kafin ta dauraye fuskar ta da kafafun ta, daki ta koma ta chanza zanen jikin ta.
Gurin kokon ta dawo ta buda bokitin da kokon yake tayi, fari kal kokon saboda yaji gasara yai kyau, tana zama aka fara shigowa saye, a haka akai ta shigowa har sai da kokon ya kare tas har ana nema.
Ganin anata neman kokon yasa ta jin haushin kudin da ake shigowa dasu ana fita kuma dasu, dan haka tabi Hafsatu dakin ta, kwance ta tadda ta har baccin wahala ya fara daukar ta, "Ke munafuka yar gadon bakin ciki tashi, " Inna Asibi ta fada tare da shurin kafar Hafsatu.
Bude idanuwan ta Hafsatu tayi da suka kumbura tayi, a hankali ta mike zaune tana bin Inna da kallo, "Bari kallo na shegiya mai idonuwan yan ruwa" inji Inna Asibi.
Babu musu ta sauke idanuwan ta kasa, dan gudun haduwa da wata cutar da Innar zata gana mata, "ki tashi maza kije kasuwa ki sawoman gero in kin tafi kada kiyi sauri ki dawo ki tsaya yawon iskancin da kike yi" Innar ta fada tare da kai ma Hafsatu mari a fuska.
Hawaye ne suka fara wanke fuskar Hafsatu, "Eyye dan wannan marin kadai yasa kike man kuka zan fa ci ubanki sakarai kai. "
Girgiza kai Hafsatu tayi "kiyi...hakuri Inna ban...karawa, " kafin ta rufe baki Inna ta kai mata bugu a bakin, saurin dafe gurin Hafsatu tayi tana hade kukan dake niyyar taso mata.
Sai da Inna Asibi ta gama zaluntar ta kafin ta kirgo kudin ta bata, dan cuta ma hana ta kudin mota tayi sai cewa tayi ai ba nisa ta dauko bisa kai, a haka Hafsatu ta dauki hanyar kasuwar, tana tafe tana kuka babu abinda ya jamata Wannan halin sai iyayen ta, da basu yadda ta ba da duk bata fuskanci wannan halin ba.
Duk da wani lokaci bata ganin laifin Inna Asibi, tafi ganin laifin iyayen ta da suka yadda ta, kilama dagaske ita shegiya ce kamar yadda Innar ke gayamata, amma koda ita shegiya ce ai ba laifin ta bane da zasu yadata basu yi tunanin halin da zata taso ciki bane.
A haka har ta isa kasuwar geron ta siya, Allah ya taimake ta tasamu ragin naira hamsin da ita tayi kudin mota, ana sauke ta kan hanyar da zata sadata da cikin garin su aka ajeta, dama nan mota ke ajewa sai ka ida isa da kafafuwan ka, masu gata kuwa bisa jakki ko amalan ke ake kai masu kayan har gida.
Rana ta take tsaka lokacin aka sauke ta, ga hanyar ba mai binta in rana tayi saboda akwai masu taren hanya, kamar karta bi hanyar amma hakanan dai tayi shahadar bin hanyar da geron ta bisa kai, aikuwa sai data raba tafiyar tsakiya bata ankara ba kawai sai dai taga mutane sun zagayeta.
Gaban ta yai mummunar faduwa saboda tasan yau karyar ta takare yau, zagayeta sukayi suna babbaka mata wata mahaukaciyar dariya, bata san sadda ta yadda geron dake bisa kan ta ba, kafin babban cikin su ya fara magana cikin muryar shi da babu dadin sauraro"Gaskiya yau dawa tayi nama, " ya fada yana mai lasar wawakeken bakin shi wanda gashi yai ma kawanya.
"Dan Allah kuyi hakuri kada ku cutar dani wallahi ni marainiya ce, " ta fada tana mai durkusawa kasa tana rokon su dasu tausaya mata.
Wata uwar dariya suka babbake da ita gaba dayan su"Gaskiya daga oga sai ni wannan yar shila haka gaskiya zamu huta yau, " cewar daya daga cikin su yana kara karemata kallo.
"Kai ku kai mani ita daki, " inji wanda da alama shine ogan su, kuka ta fashe dashi tana rokon su suyi hakuri amma ko jinta basu yi, kafin ta ankara ma har wani yayi sama da ita, cikin dajin suka nausa da ita babu abinda kake ji sai sautin kukan ta.
Ganin zata tara masu mutane ne yasa suka kulle mata baki, sai da sukai tafiya mai nisa kafin su zo bakin wata bukka,nan aka shigar da ita cikin bukkar, yunkurawa tayi dan ta ruga wani yasa kafa ya tadota komawa tayi ta fadi kasa rigijib.
Fitowa suka yi sannan ogan ya nufi hanyar shiga bukkar, har ya kusa shiga bukkar ya juyo inda suke, "ku samoman ruwan wanka kafin in fito kuma ku tafi gaba daya. "
Yana fada bai tsaya komai ba yasaka kai cikin bukkar, Hafsatu ya tadda zaune sai sharbar kuka take yi, murmushi yai mata mai kama da yana kuka, " Kar ki damu kan ki yammata danayi zan barki ki tafi. "
Ya fada yana mai bin jikin ta da kallon sha'awa, kara nannade jikin ta tayi da hijab din ta, "dan Allah kada ka cutar dani wallahi ni marainiya ce. "
Dariya ya kara babbakewa da ita kafin yace, "Yarinya hutawa kawai zanyi dake zan maki taimako daya shine in hana yarana hutawa dake. "
Ya fada yana mai kama kafadun ta, gocewa tayi daga rikon da yayi mata, kara kamota yayi ta sake gocewa, daure fuska yayi " bari ganin ina tausayin ki wallahi zan daure ki kuma inyi abinda nagadama dake, dan tunda kika shigo nan babu wanda ya isa ya fidda ki batare dana dandani zumar kiba. "
Ya fada yana kara kai mata damka, nan ma ta sake gocewa, wasa-wasa karamar magana ta zama babba dan guje-guje suka kamayi ita dashi cikin bukkar, har Allah ya bashi sa'a ya samu damar kamata, ganin taki bashi hadin kai yasa shi, dauke ta da mari wanda yai sanadiyar tsayawar jin ta na yan dakiku.
Kokowa ta sarke tsakaninsu inda har yai nasarar yaga mata gaban riga kirjin ta waje, ganin kirjin ta waje fa yasa ya kara gigicewa yana son kai ta kasa, ya kuwa samu nasarar kai ta kasa, ya danne ta yadda bata iya wani motsi, sai kokari yake domin ya samu damar kwance daurin zanen jikin ta, kuka take har muryar ta bata fita ko kadan, tama sadakar ya samu nasara kanta, gab ya kusa ida kwance zanen Allah yasa ta ga wata sanda saitin kan shi, motsi tai tayi har ta zunguro ta daga inda aka ajeta, aikuwa kafin ya ankara yaji abu bisa kan shi.
Ganin haka yasa ta sakar mashi wani mahaukacin cizo a kirji, aikuwa jin wannan azabar guda biyu lokaci daya yasa shi daga ta ba tare daya sani ba, kara ya saki wadda tai sanadiyar ankarar da yaran shi abinda ke faruwa, bukkar suka nufo cikin sauri kafin su karaso, har Hafsatu ta dauko wannan sandar ta labe bakin kofar, suna sanyo kai ciki ta sakar ma na farkon ita bisa kai, dafe kan yayi tare da fasa kara ya fadi kasa.
Da wani mahaukacin gudu ta fita daga cikin bukkar, bayan ta dayan yabi da gudu, a haka su kai ta gudu har tayi tintibe da wani kututturen icce ta fadi, shima gabanta ya ja tunga yana maida numfashi.
Hussy Saniey🥰
YOU ARE READING
UƘUBA
AdventureLabarin wata yarinyane mai suna Hafsatu wadda ta tashi a hannun mariƙiyarta sanadiyar tsintar ta da aka yi inda ta sha wahalar rayuwa sosai kafin daga baya ta hɗu da iyayenta