Page 39&40

20 0 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan na kasa_*

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*

*PAGE 39&40*

Basu suka iso gidansu ba sai bayan sallar magrib har an fara alwalla isha'i,hon Alhaji ya yi maigadi ya buɗe gate,kasancewar glass ɗin motar mai duhu ne yasa har suka isa parking space Babu wanda ya lura da su Hafsatu da ke bayan mota a zaune, kasancewar ɓangaren Hajiya Asiya shi ne kusa da inda ake aje motoci ana tsayawa Hajiya Asiya ta fita da sauri ta buɗe ƙofar ɓangarenta, Hafsatu da Inna Asibi suka bi bayanta tana buɗewa suna shiga,shigarsu ta yi daidai da Hajiya Kaltume ta fito daga ɓangarenta tana kiran maigadi,ganin Alhaji a tsaye yasa ta nufar inda yake mamaki kwance akan fuskarta,cikin ranta take tunanin yaushe ya dawo toh? Tun kafin ta ƙaraso inda yake ta ce,"Abbansu yaushe ka dawo?"
Kallonta ya yi shi ma fuskarsa kadaran kadahan ya ce,"dawowar kenan masallaci na ke son zuwa shi yasa kika ganni nan a tsaye."
Daidai ta ida ƙarasawa a gabansa ta ce,"sannu da zuwa ina ka baro hakimar ita ko can Saudiyyar ka barota?"
Ta faɗa tana lalleƙa bayansa dan ganin inda Hajiya Asiya za ta fito,girgiza kai ya yi cikin ransa yana mamakin halin Hajiya Kaltume,bai son maganar ta yi nisa dan haka ya ce,"ta shiga ɓangarenta."
Taɓe baki ta yi ta juya ba tare da ta sake ce wa komai ba,bayanta ya bi da kallo yana mamakin halayyarta,jin an fara haramar ta da Sallah yasa shi sauri ya nufi masallaci,ko da ya dawo ɓangarensa ya wuce.
Hajiya Asiya kuwa tana shiga ɓangarenta duk ya yi ƙura,ita da Inna Asibi suka gyara ɓangaren fes,suna gamawa ta haɗa ma Inna Asibi ruwan wanka a ɗakin kusa da na ta, ɗakinta ta kai Hafsatu ita ma ruwan wankan ta haɗa mata,ganin duk sun shiga wanka yasa ta nufi kitchen ta ɗora masu indomie wadda ta ji busasshen kifi,falo ta kawo abincin tare da lemuka ta aje, ɗakin da Inna Asibi take ta nufa,a zaune ta iske Inna Asibi har ta canza kayan jikinta.
"Inna ki fito ga abinci can a falo ni wanka zan shiga."
Hajiya Asiya ta faɗa daga bakin ƙofa.
"Hajiya ni dai nan ma ya isheni ba sai na fito ba."
Inna Asibi ta faɗa kanta a ƙasa dan wata irin kunya ce ke damunta ganin gidan da Hafsatu ta fito,gaskiya Tasallah ta cuceta da ta sanya ta rinƙa muzguna ma Hafsatu.
"To bari Hafsatu ta fito sai ta kawo maki abincin nan ɗakin,ki daina damuwa Inna ni a haka ma ina godiya da kika riƙe man ɗiyata ba tare da rayuwarta ta lalace ba."
Hajiya Asiya na gama faɗin haka ta fita tare da jan ƙyauren ɗakin.
Ko da Hajiya Asiya ta shiga ɗakinta zaune ta iske Hafsatu akan sallaya,ganinta yasa Hafsatu miƙewa tsaye.
"Ki je falo akwai abinci na nan ki ɗiba ki kai ma Inna Asibi tana ɗakin da ke kusa da nan,bari na shiga wanka idan kin kai mata ke ma ki zauna ki ci abincin kafin na fito ina so mu yi magana da ke."
Ba ta jira jin abin da Hafsatu za ta faɗa ba kawai ta shige toilet,shiru Hafsatu ta yi har yanzu ita ganin abun take tamkar a Film wai wannan 'yar gayun matar ita ce mahaifiyarta, Allah mai iko ita da take rayuwa babu gata amma yau ita ce wai yau ta haɗu da iyayenta,daga yanayin unguwar da suka shigo kaɗai tasan iyayenta masu kuɗi ne, da wannan tunanin ta kai ma Inna Asibi abinci,sai nan nan Inna Asibi ke yi da ita,ba ta zauna ba ta koma falo ta zauna ta ci abincin ta ƙoshi,tana cikin tattare kayan da ke wurin aka kwankwaso ƙofar falon,wurin ta isa ta sha fama kafin ta samu nasarar buɗe ƙofar duk da jamlock kaɗai ne,wasu manyan mata ne har da maza guda biyu ta gani a tsaye,cikin farin ciki wata tsohuwa ta rungume Hafsatu dan ko ba a faɗa mata ba tasan wannan ita ce jikarta.
Ciki suka nufa kowa na son Hafsatu ta zauna a kusa da shi, Hafsatu dai tamkar hoto haka ta zama sai yadda aka juyata take yi,wata irin natsuwa ce ke shigarta,lalle Iyaye da dangi rahama  ne,fitowar Hajiya Asiya ta ida hautsina falon ganin danginta sun gaza haƙuri sun taho har da mahaifiyarta da bata taɓa zuwa gidanta ba amma yau sai ga shi tazo,nan ta zauna ta rinƙa basu labarin yadda komai ya kasance,har ɗakin da aka sauke Inna Asibi suka shiga suka rinƙa yi mata godiya tamkar bata cutar da Hafsatu ba dan su ko a haka ma sun gode,nan Hajiya Asiya ke sanar dasu gobe akwai meeting a can gidansu Alhaji, sai da dare ya yi sosai suka tafi,Hajiya Asiya da Hafsatu kuwa a ranar basu runtsa ba ko kaɗan suna ta labari.
                 *******************
Washe gari wurin ƙarfe goma na safiya hall ɗin ya cika kowa na mamakin abin da ya faru,duk lokacin da ka ga an yi irin wannan taron tabbas wani gagarumin abu ya faru,kowa fuskar shi cike da mamakin dalilin wannan taron,sai dai duk wanda ya tambayi wani amsa ɗaya ce shi ma bai sani ba.
Bayan an buɗe taro da addu'a,wata dattijiwu ce wadda a kiyasi ta haura shekara ɗari aka miƙa mata abun magana ta fara," da farko dai duk wanda ke cikin wurin nan yasan akwai wani gagarumin abu da ya faru dan haka ba komai ba ne ya faru illa dawowar ɗiyar Malam ƙarami (tana nufin Alhaji kasancewarsa ɗan fari a wurinta yasa ba ta kiran sunansa)wadda ya haifa tare da Asiya,wadda kowa ya ke tsammanin ta mutu saboda samun matsala ma har gwajin jini sai da aka yi wanda muka tabbatar da yarinyar jininmu ce wasu marasa imani suka ɗauketa a lokacin da aka haifeta, Hafsatu shigo cikin danginki kowa ya ganki."
Wata ƙofa aka buɗe Hafsatu ta shigo kanta a sunkuye,gaba ɗaya hall ɗin aka ɗauki kabbara saboda kamanninta kawai sun isa su sanar da kai gaskiya.
"Wallahi ƙarya kike ki ce kin dawo abin da ba zai yiwu ba kenan."
Hajiya Kaltume ta faɗa tare da jifa da kallabinta,gaba ɗaya kowa ya juyo yana kallonta da mamakin abin da take faɗi,tunkaro inda Hafsatu take tsaye ta yi tana faɗin.
"Wallahi kin yi ƙarya ki dawo boka ya faɗaman ke ba za ki taɓa dawowa ba."
Tana maganar tana jifa da kayan jikinta,kafin ta isa inda Hafsatu take maza suka rirriketa,nan fa tai ta tonon asiri na yadda ta shirya a sace Hafsatu,kafin mutanen da ke riƙe da ita su ankara kawai ta ficce a guje, bayanta aka bi da gudu cikin tsautsayi tana fita mota ta bi ta bisa kanta ko shurawa ba ta yi ba.
Nan fa wuri ya rikice yaranta suka rinƙa kuka da roƙon Hajiya Asiya akan ta yafe mata,bayan sadakar uku kowa ya watse.
Wata rana wata ƙanwar Hajiya Asiya ta tafi da Hafsatu gidanta za ta yi mata ƙwana biyu,bayan sun je ta aike ta makwabta Hafsatu na zuwa gidan nan fa ta iske Baba Yalwa a gidan nan suka rungume juna da murna,nan fa suka rinƙa ba juna labarin bayan saduwa,nan Baba Yalwa ke sanar da ita lalle matar da ta gani farkon dawowarsu nan unguwar mahaifiyarta ce,sun yi murna da ganin juna sosai.
Bayan wani lokaci Alhaji ya sai ma Inna Asibi gida ya bata kyauta,har ƙauye aka kaita taje ta yi banƙwana da mutane,a nan take jin labarin Tasallah ta haukace,wani irin tsoron Allah ya ƙara shigarta,dan abin da ya faru da ita ya zame mata ishara,kullum idan ta kalli kanta sai ta ga kamar ba ita ba saboda yanda jin daɗi ya zauna mata a jiki,kuma wannan duk ya faru akan yarinyar da ta muzguna wa.
Bayan dawowarsu da shekara biyu Hafsatu ta yi aure ta auri wani yaro ɗan ƙanen Babansu,idan ka ga Hafsatu a yanzu ba zaka taɓa tunanin ita ce Hafsatun ƙauye ba.

Alhamdullih.
Anan ne kawo ƙarshen wannan littafin kuskuren da nayi a ciki Allah ya yafeman.
08105217201

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 22, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

UƘUBAWhere stories live. Discover now