Page 17&18

12 2 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

     *🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*

                        *NA*

                *HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga  shafin,mu na Bakandamiya dana  shudin rubutun nan_*

*_NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE DIN GAREKI BESTYNA, MAGATAKARDAR KAINUWA HAUWA'U SALISU WANNAN PAGE DIN NAKI NE KIYI YADDA KIKA GADAMA DASHI_*

17&18

Hafsatu sai da ta sha kukanta sosai,  Sannan ta mike dan gabatar da sallar isha'i,tsakar gidan ta fito ba kowa wajen da alama Inna Asibi tana d'akinta, in da suke aje buta ta je ta d'auka, band'aki ta shiga ta kama ruwa sannan ta fito, zaunawa ta yi bisa wani dutsi da suke zama in za su yi alwalla, shiru ta yi tana tunanin irin rayuwar da za ta yi nan gaba dama gurin Baba Yalwa ne take zuwa ta ji sanyi, amma yanzu ga shi yadda ta kasance babu Babar kusa da ita, wasu hawayen tausayin kanta ne suka k'waranyo daga cikin idanuwanta, sadda kanta ta yi bisa cinya ta fashe da wani wahalallan kuka,ita kanta ba ta san yaushe za ta daina wannan kukan ba, abin da kawai ta sa ni shi ne yanzu ita da kuka sun d'aura aure, ta dauki tsawon lokaci a zaune ta na wannan kukan, ba ta ji fitowar Inna Asibi ba sai dai saukar muryarta ta ji a bisa kanta, ko motsawa ba ta yi ba daga inda take ba, wata firgitattar  tsawa Inna Asibi ta daka mata wadda ta sa ta dagowa ba tare da ta shirya ba.

"Ke har kin yi girman da zan maki magana ki kasa ko dago kai ki kalleni,?" Inna Asibi ke fada tana bin Hafsatu da wani wulakantaccen kallo.

Girgiza kai Hafsatu ta yi cikin rawar jiki ta bude bakinta muryarta ko fita ba ta yi sosai, "ki yi hakuri Inna ban ji maganarki ba ne shiyasa amma ki yi hakuri. "

Takowa Inna Asibi ta yi har gaban Hafsatu, bin Hafsatu ta yi da kallo ta dad'e tana kallonta har sai da Hafsatu ta tsargu, "gaskiya ne dama ta ya za ki ji abin da nake fadi bayan kina ta wannan kukan saboda uwarki ta tafi ta bar ki ko. "

Girgiza kai Hafsatu ta yi cikin rawar murya ta ce "A'a Inna ba haka ba ne ina dai kukan sabo da ita ne kum..."

Kafin ta karasa Inna Asibi ta kai ma ta bugu ga bakinta har sai da yayi jini, " ke har kin isa ki rink'a tsaida ni kina gaya man wannan shirmen? "

"A'a Inna ki yi hakuri dan Allah" Hafsatu ta fad'a hawaye na kara bin kumatun ta.

Shiru Inna Asibi ta yi tana kallon Hafsatun, kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shiru, juyawa ta yi ta nufi d'akinta har ta kama labule za ta shige d'akin,kuma sai ta dakata tare da juyowa da fuskarta gurin Hafsatu, "ki yi ta zama nan gurin har in k'ara fitowa daga d'akin in tadda ki nan wallahi sai na yi maki bugun da za ki yi jinya, in kuma bin Yalwar za ki yi wuce ga hanya nan sai in ga karshen soyayya" tana gama fadin haka ta ida shigewa cikin d'akin tare da rufo kofar d'akin ta.

Dauke idanuwa Hafsatu ta yi ganin Innar ta shige d'akinta, Shiru Hafsatu ta yi tana juya kalaman Inna Asibi cikin zuciyarta, ganin zaman be da wani amfani ya sa ta jawo butar ruwanta ta yi alwalla, tana gamawa ta mike tsaye ta je ta rufe gidan, sannan ta dauke kwanon da Inna Asibi ta fiddo waje, sai sannan ta gane dalilin fitowar Innar, inda suke sanwa ta shiga ta kai kwanon sannan ta fita ta nufi d'akinta.

Wani yank'wanan nan abin sallah ne ta dauko ta shimfida ,amma duk da tsufanshi a tsabtace yake babu daud'a a jikinshi, sallar isha'i ta kabbara bayan ta gama kuma ta dad'e tana addu'a kafin ta yi shafa'i da wutiri, tana gamawa ta kwanta bisa yar tabarmar da take kwana bisa, ta dad'e tana tunanin yadda za ta yi rayuwa babu Baba Yalwa kusa da ita, wani tausayin kanta ya k'ara kama ta, ba ita ta kwanta ba sai da ta sha kukanta sosai, sannan bacci mai nauyi ya d'auketa.
   
         *******************
"Asiya! Asiya!! Asiya!!! wai ba ki ji duk wannan kiran da nake yi maki amma shiru ba amsa?" Wata dattijuwar Mata ce ke maganar.

Firgigit wadda aka kira da asiya tayi,cikin alamun tausayi ta ce"Yi hakuri Hajiya wallahi banji bane. "

Matar zama tayi bisa daya daga cikin kujerun falon tayi kafin ta k'ara fuskantar yar wadda ta kira da asiya, "dama ya za'ayi kiji ina kiranki bayan hankalinki baya tare dake Asiya. "

Murmushi Asiya tayi kawai ba ta ce komai ba, ganin haka yasa Matar fahimtar tunda tayi haka to ba maganar za ta k'ara yi ba, dan haka sai ta k'ara gyara zamanta tare da yin gyaran murya,"Asiya ni kuwa da zaki yadda da na baki shawara."

Dago kai Asiya tayi ta kalli wannan dattijuwar Matar sannan ta bude bakinta cikin sanyi murya tace,"Ki bani mana aike uwace agareni dan haka ina maraba da duk wani abu da zai fito daga gareki."

Murmushi ne Matar ta wadata fuskarta dashi,taji dad'in maganar Asiya sosai,shiyasa a ko da yaushe take k'ara son Asiya saboda biyayyar da take mata, gyaran murya tayi kafin tace"Asiya a baya kin tab'a tunanin a baya Allah zai baki haihuwa? "

Hawayen da take ta rik'o ne suka zubo bisa fuskarta, girgiza kai tayi alamar A'a, bata fuska dattijuwar tayi kafi tace"da baki nake yi maki magana dan haka dashi za ki bani amsa. "

Bude baki Asiya tayi cikin rawar murya tace"A'a ban tab'a tunanin Allah zai bani haihuwa a wannan lokacin ba saboda har na fidda rai da samunta. "

Murmushi Matar tayi kafin ta sake cewa"Asiya duk abin da za ki gani a duniya to daga Allah ne,  kuma Allah yana jarabtar bayinshi ta hanyoyi da dama, shin baki rok'on Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawar, shin baki ganin wannan damuwar da kike ciki zata iya janyo abubuwa da dama, ciki kuwa hada illa ga lafiyar jikinki, shin Asiya baki tausayin rayuwar da zamu shiga ta dalilin halin da kike ciki? "
 
Hawaye ne masu zafi suka rink'a zubowa saman fuskar asiya kamar an bude famfo, "Hajiya wallahi na yadda da k'addarar da Allah ya doraman abu daya ke damuna hajiya,idan na tuna ina kallo aka fitar man da d'iya amma ban da ikon amsar ta, wallahi naso ace mutuwa d'iyata tayi akan abin da yafaru, kullum tunanina shine a wane hali d'iyata take saboda ina ji a jikina d'iyata tana nan da ranta. "

Dafa kafadar Asiya dattijuwar tayi kafin tace"kiyi hakuri ki fauwala ma Allah lamarin ki shi zai dubek,yasan abin da yake nufi da faruwar wannan al'amarin Allah shi kadai yasan hikimarshi tayin haka, sai dai muyi Addu'ar ganin karshen abun lafiya. "

Jinjina kai Asiya tayi cikin alamun nuna gamsuwa da maganganun da Matar tayi mata"insha Allah hajiya zan yi kokari na kiyaye. "

Murmushi Matar tayi sannan tace"yauwa Asiya haka nake son ji daga gareki, ki kara hakuri nasan Allah shi kadai yasan ajiyar da yayi maki kuma zai yi maki sakamako na alkhairi. "

Murmushin karfin hali Asiya tayi kafin ta ce"Hajiya nasan ni dai sun riga da sun gama cutata sun hanani jin dumin jikin d'iyata sun hanani rayuwa da d'iyata Allah shi kadai zai yi man  sakayya a gurinsu."

Girgiza kai dattijuwar tayi kafin tace "kansu suka yi mawa koma meye duk wanda yayi da kyau zai ga da kyau ai a rayuwa, dan haka kada ki damu akwai Allah. "

Sun dad'e zaune Matar na k'ara yi ma Asiya nasiha da muhimmancin yadda da k'addara, sai da taga hankalin Asiya ya kwanta sannan ta tashi ta koma d'akinta, itama Asiyar na ta d'akin ta nufa.

Hussy Saniey.🥰

UƘUBAWhere stories live. Discover now