*بسم الله الرحمن الرحيم*
*🩸🩸🩸UƘUBA🩸🩸🩸*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_Dumin shiga shafin,mu na Bakandamiya dana shudin rubutun nan_*
7&8
Tsaye ta tadda Hafsatu tana jiran tsammanin irin azabar da zata sha a daren yau,ko zama hafsatu kasa yi tayi tun bayan fitar Inna waje,ganin shigowar ta a guje yasa gaban Hafsatu wata dama tasan akwai dirama yau cikin gidan, kafin ta dawo daga tunanin da ta tafi kawai sai jitai Inna ta kai mata wata wawar shakara ga wuya, rufe ta tayi da duka ta ko ina.
Wata bulala ta jawo ta dinga dukan Hafsatu da ita, ihu take yi da iyakar karfin ta, dan neman taimako amma babu wanda yayi yunkurin shigowa gidan, saboda kowa na tsoron masifar Inna Asibi, dan bata ragama kowa cikin kauyen.Bulalar katsewa tayi dan haka ta yadda ta, wani katon icce ta dauko ta cigaba da dukan Hafsatu dashi.
Tun tana yunkurin kwatar kanta harta hakura,iccen ma sai daya kare kafin ta yadda guntun, wani katon icce ne Inna ta dauko ta cigaba da dukan Hafsatu dashi,dukan ta tayi har ta gaji dan kanta, zuwa lokacin kuwa Hafsatu ta galabaita ko motsi bata iyawa, Inna yada guntun iccen dake hannun ta tayi, kai tsaye bakin tukunyar ruwan shan su ta nufa, kofi ta ciko da ruwa mai sanyi ta juyo gurin da tabar Hafsatu kwance, tana zuwa kofin ta daga ta sheka mata su ga jikin ta, ko motsawa Hafsatu bata yi ba, Inna ganin taki motsawa yasa ta kara komawa ta debo wasu ruwan ta zuba mata, motsawa tayi amma ta kasa mikewa, ganin ta tashi yasa Inna kama hanyar dakin ta, tana shigewa ta rufo kofar dakin bata kara bi ta kan Hafsatu ba.
Yunkurin mikewa tayi tsaye amma ta kasa dole ta koma ta kwanta, bata san iya adadin lokuttan da ta dauka anan ba, ta dade sosai a gurin ga wata mahaukaciyar yunwa da take ji, rabon ta da abinci tun tuwon data ci da safe, gashi yanzu har tara na dare ta wuce, ganin yunwa na neman halaka ta ya sanya ta dinga rarrafawa zuwa inda suke sanwa, amma duk iya dubawar ta babu komai na ci gurin.
Hanyar kofar gida ta nufa nan ma babu mutane, duk kowa ya shige gidan shi, kasancewar lokacin sanyi ne, da rarrafen ta shiga wani gida dake makwabtan su, babu wani gida dake tsakaninsu.
Da rarrafen ta ida shiga cikin gidan, da sallama ta shiga gidan duk da muryar ta bata fita sosai, wata tsohuwa ta tadda zaune, tana ganin shigowar ta, tsohuwar ta mike tsaye tana rawar jiki.
"Sannu Hafsatu Allah yabi maki hakkin ki, kiyi hakuri wata rana sai labari. "
Murmushin karfin hali Hafsatu tayi, kai da gani dai kasan Murmushin iyakar shi ga fatar baki, kama mata Kafada matar tayi ta taimaka mata ta mike tsaye.
Bakin tabarma ta kaita ta zaunar da ita, kewaye ta nufa ta dauko bokiti ruwa ta zuba na zafi ta surka da na sanyi, dai-dai yadda zataji dadin wanka.
Dawowa tayi ta taimaka mata ta kaita kewaye, fitowa matar tayi ta bar Hafsatu dan tayi wanka, Hafsatu na kuka tana wanka, sai data gasa jikin ta sosai kafin ta fito daga kewayen.
Zaune ta tadda matar da kwanon abinci gaban ta, zama tayi gefen ta bata ce komai ba, itama matar bata yimata magana ba sai dai ta turo mata kwanon gaban ta, babu musu ta dauki kwanon tuwon masara ne fari kal da Miyar kuka sai kamshin man shanu yake, bissimilla tayi tare da saka hannu cikin kwanon, hannu baka hannu kwarya ta dinga cin tuwon, sai data gama cinye tuwon gaba daya sannan ta sha ruwa.
Zuru matar tayi tana kallon yadda take cin abincin, gaba daya kallon tausayi take mata, "ki tashi ki koma Hafsatu kada taga baki nan. "
"To shikenan baba yalwa, " ta fada tana mikewa tsaye, bin ta baba yalwa tayi da kallo mai dauke da zallar tausayi, da tana da iko da bazata bar Hafsatu ta koma gidan chan ba, amma ya zatayi bata da wannan ikon dole ta kyale ta.
Hafsatu tana fita daga gidan ta nufi gidan su, har lokacin babu kowa tsakar gidan, dan haka itama dakinta ta koma ta kwanta.
Hussy Saniey🥰
YOU ARE READING
UƘUBA
PrzygodoweLabarin wata yarinyane mai suna Hafsatu wadda ta tashi a hannun mariƙiyarta sanadiyar tsintar ta da aka yi inda ta sha wahalar rayuwa sosai kafin daga baya ta hɗu da iyayenta