❄️❄️❄️❄️
*RAUDHA PART 2*
❄️❄️❄️❄️
*EPISODE 15*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**Don girman Allah idan kin karanta kada ki wuce batareda kinyi sharhi ba, koda layi d'aya ne, please appreciate me if you have the heart*
........................... Alhaji tijjani yace bushasha kenan bazaka gane ba, wannan magana tamu sai mun had'u, yaushe zaka je kano, ehto gaskiya sai nan da sati biyu idan za, a kai lefen ABBANA sai naje.
Yawwa hakan ma yayi, gwara a had'un, za, a fi jin dad'in tattaunawa.
Shigowar ABBATI yasanya shi ajiye wayar, tareda fad'ad'a murmushin dake kan fuskarsa, ABBANA ango kenan sai wani haskawa kake wane farin wata meye sirrin ko za,a lasa min.
ABBATI ya zauna looking so exhausted yace kaifa dad akwai ka da son jin baki, see the way am suffering duk na wani tsofe kwana biyu, amma kace ina shining, uhmm i don't buy that!
Alhaji lawan yazo kusada shi ya zauna yace ABBANA kenan, bazaka yarda da abinda nake fad'a ba, sai ma an d'aura aurenka da wannan zuk'ek'iyar baturiyan yarinya, wacce zata maidoka tamkar sabon balarabe, kai da kanka sai ka kasa gane wanene kai wallahi.
Wannan karon murmushi yayi yace so dad what's the latest? Alhaji lawan ya d'an looking serious yace inshAllahu by Monday zamu tafi dubai nida kai da hajiya y'ar d'agwas muje mu kwaso wa amaryar ka kaya tagani tafad'a.
ABBATI ya d'an b'ata rai yace wacece kuma hajiya y'ar d'agwas? Alhaji lawan yayi dariya yace saninta bashine damuwar ka ba ABBANA, kasan ni mai jama,a ne, duk wacce buk'atar ta taso dole ne ayi da ita.
ABBATI ya tab'e baki, da gaske yasan babanshi mai jama,an ne, amma marasa kan gado da k'eya. domin most of the people dayake huld'a dasu yakan rasa a ina yake samo su, 90% d'insu babu dangin iya balle na baba, kai shi he is always wondering about their relatives, ko suna nan.
Domin shidai tunda ya taso yake ganin suna rayuwarsu shida babansa, da akwai wata y'aruwarsa datake yawan zuwa gidan nasu, to tunda ta rasu lokacin yanada shekaru goma sha hud'u, to shikenan bai kuma ganin wani ya nuna a matsayin nashi danginshi na jini ba.
Ko yace wa mahaifinsa yakai shi wajen danginsa, sai ya hau shi da fad'a wai shi bashi da wani dangi bayan hajiya data rasu, but indai mutanen waje ne, to fa babu kalar da bata zuwa gidansu, and most of them are scam, inji shi.
Lokacinda DEEN ya koma gida, acike ya taras da ita, ba kamar yanda yasaba taras wa ba.
Wasu y'an kyawawan yara ne maza su biyu da shekarun bazai wuce shida ba, nagani sun taho aguje sun rumgume shi da murnar su, kowanne na fad'in " kaabo" arakunrin(welcome uncle).
Ya d'aga su duka a lokaci guda yana fad'in "mowa dun lat ri o" taiwo' ka'inde (am so glad to see you taiwo da kainde)
Which means y'an biyu kenan da yaran yarbanci. ya isa ya zauna kusa da wata babban mata, wacce dagani kallo d'aya zakayi mata kasan jikak'k'iyar mai naira ce, wacce tasha wanka ta fito reras da ita cikin, gwal da zinare tundaga kunnuwanta har wuyanta da hannayenta, ga wani uba uban leshi daya amsa sunansa ta leshi ajikinta.
Ba wani kyau ne da ita ba na azo agani, illa farin fatar datake dashi wanda kana gani kasan artificial ce, ta jin dad'i da mayuka.
A ladabce ya gaisheta, ta amsa da fara,a sosai tana fad'in, DEEN ka gujemu kamar wasa, rabonka da gidana tun lokacinda umminka taxo daku abeakuta, kana teenager ka, saidai idan munzo nan mu had'u, kuma i heard that kana yawan shigowa lagos, laifi mukayi ne son?
Yayi murmushi yana wasa da hannun taiwo dake cikin nashi hannayen, yace not at all mom, is just that ayyuka ne suke mini yawa, i don't have time of my own.
YOU ARE READING
RAUDHA
General FictionThis is a story of a young innocence soul , an asian young girl whom destiny or coincidence brought to nigeria into the northern part of the country . what is her name, where is she from, who are her parents ,and why was she found in a middle of no...