💔❄️❄️❤️
*RAUDHA PART 3*
💔❄️❄️❤️
*EPISODE 11*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*
*EMOTIONAL*
...................... D'akine mai matsakaicin girma, wanda ya k'unshi kayayyakin alatu na more rayuwa, kamar su carpet, tv manyan kujeru guda biyu sai wata y'ar matsakaicin katifa dake ajiye acan k'uryar d'akin.
Wata nurse ce nagani tanata faman harhad'a wasu magunguna acikin sirinji tana ja, sai kuma naga taje gaban wannan katifar ta juyeshi duka acikin ruwan drip d'in dake sak'ale jikin wata k'arfe dake gefen gadon.
Wasu naurori dake gefen gadon naga ta d'an tattab'a su, sannan ta gyara mata zaman oxygen d'in dake d'aure akan hancinta.
Bargon da aka lullub'eta dashi, wanda ya d'an yaye, ta gyara mata. a lokacin ne aka turo k'ofar d'akin. wani kafcecen k'atone mai kausassan murya irinta gardawa nagani, yace keee wai yane! zata farka kuwa?
Nurse d'in ta juyo tana kallonshi a razane, domin tsoratar da tayi da jin muryansa.
Kasa magana tayi har ya iso inda take jikinta ne yasoma rawa, k'arewa RAUDHA kallo yayi na y'an mintuna, sannan ya kalli nurse d'in da jajayen idonsa, data kasa had'a ido dashi.
Sai kuma ya fita da sauri yana tafe k'asa na yin k'ara gaf gaf kamar wani doki, tanaji yayi bangin k'ofar d'akin da k'arfi har saida gabanta ya fad'i, nurse d'in ta sighting relief, tareda zama gefen gadon tana dafe goshinta, da har yanzu tana cikin zullumi da tunanin dalilin da zaisa mutane su d'auko mace da ko awa uku mai kyau batayi da haihuwa ba akawota wajen da gardawa kamar wannan su zasuyi gadinta, wannan wani irin rashin imani ne.
Dayake babban murya gareshi tana ji yana waya da wani da batasan wanene ba.
Daga can b'angaren Alhaji bushasha da yayi samb'al da dogayen k'afafunsa asaman glass d'in center table. yana karkad'a su d'aya akan d'aya, ga kuma wasu tarin kud'i danaga yana kwashewa yana juyewa acikin wata y'ar bak'ar jaka.
Ko sallama baiyi ba ya shigo yana kwaroroton kiran sunan ALHAJI LAWAN, wanda tunda yaji shigowarsa ya kauda kai daga kallon wajen, yana mai cigaba da abinda yake gabansa.
Where is she? ABBATI ya fad'i cikeda tsananin b'acin ran da har saida jijiyoyin wuyarsa suka tattare waje guda tamkar ya had'iyi k'ota, bai amsa ba, kamar yanda ko d'agowa ma baiyi ba.
ABBATI ya kuma cikada haushin mahaifinsa, yasan duk wad'annnan abubuwan yana dad'a yinsu ne da gayya saboda shi, tundaga lokacin da yak'i yarda yacigaba da zama puppet d'insa,ta yanda zai cigaba da dad'a sanya sa a hanyar halaka.
Kafin ALHAJI LAWAN ya ankare kuwa, ABBATI yaje yayiwa damin wannan kud'in, b'arin makauniya, ya d'auki jakan ya wurgata acan kusada k'ofa duk kud'in suka tashi sama awatse.ya hau magana cikin fad'a.
Nagaji! Nagaji! da munanan halayenka, nagaji da yanda kake juya min rayuwa yanda kaga dama tamkar kasami wani waina, and now! she, ya d'anyi k'asa da murya yace, you're doing this to hurt me?
ALHAJI BUSHASHA ya d'ago kai a karo na farko tareda jingine bayansa jikin kujera, ya sanya hannu ya tallafe k'eyarsa. fuskarsa k'unshe da wata kwantacciyar fara,a mara ma,ana da tushe.
So it's true, you still loves her? ABBATI yayi masa wani irin kallo na amma ka Raina Mana wayo. saidai bai iya ce masa komai ba, takowa yayi ahankali ya d'aga bindigar dake gefensa ya saita shi a gefen kansa yace tell me where she is ko na fasa maka kwakwalwa.
ALHAJI LAWAN yayi murmushi tareda gyara zama yace ABBA ABBANA, kana tunanin burgarka zatayi aiki akaina ne, zaka iya kasheni amma babu abinda zai canza a dukkanin plan d'ina, yazama dole na tarwatsa rayuwar yaron nan kamar yanda yake k'ok'arin ganin ya downing d'ina, and you can't stop me, infact babu mai iya dakatar dani.
KAMU SEDANG MEMBACA
RAUDHA
Fiksi UmumThis is a story of a young innocence soul , an asian young girl whom destiny or coincidence brought to nigeria into the northern part of the country . what is her name, where is she from, who are her parents ,and why was she found in a middle of no...
