💔❄️❄️❄️💘
*RAUDHA PART 3*
💔 ❄️❄️❄️💘
*EPISODE 1**STORY & WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*
*The shocker*
............................ A gajiye yake, shiyasa ko da ya shigo cikin gidan bai bi ta kan kowa ba yayi wucewarsa direct zuwa d'akinsa, ruwa ya watsa sannan yayi sallah, kishingid'a yayi akan gado, tareda kashe wayoyinsa domin yasan tabbas kuwa, yau kiran dazai sha kam saita Allah.
Ya dad'e yana bacci kafin Allah yasa ya farka, lokacin k'arfe hud'u da kusan rabi .
Yana idar da sallar la, asar, fridge ya bud'e fridge dake, jin cikinsa ta fara kukan neman agaji, ba wani abun kirki yasamu ba, aciki sai fruits apple da kuma strawberries dake ajiye a step d'in sama na fridge d'in, wanda dagani bai dad'e da aka ajiye su ba aciki.
Dawowa yayi ya zauna yasoma ci tamkar wanda akayiwa dole, yana kuma kallon k'wallo da akeyi wacce, kallon second kad'an yayi mata, sannan ya dau remote d'in TV yana mai jan doguwar tsaki.
Canza tashan yayi zuwa ga tashar yin labarai, baidamu da yanda kid'an fara shirin yakeda amo, wanda hakan ya cike wajen da k'ara da sauti ba. bansan dalilin shi na yin ko oho da kid'e kid'en nasu mara dad'in ji ba, k'ilan ko don yanada son kallon tashoshin labarai ne oho?
Goran ruwa ya kafa a bakinsa yanasha, daidai kuma lokacinda yaji abinda yajanyo attention d'insa gabad'aya ga kallon allon tv, batareda goran tabar bakinsa ba.
Breaking news! abinda idonshi yasoma arba dashi kenan.
"There was a chaos, suspense, fear in the eyes of people living around sharad'a area, one of the most prominent area in the city of kano, today the unexpected and unbelievable that one could have never imagined has happened, this is the first time most people have ever seen such in their entire life"
Nuno yanda sojojin dasuka je wajen d'aurin auren akayi, yanda sukayiwa wajen k'awanya da yanda sukayi tayiwa su Alhaji lawan, da Alhaji tijjani jan ido, tare kuma da yanda mutanen dake wajen gurin keta faman rarraba idanu cikeda tsoro.
Dan jaridar yaci gaba da magana kamar haka!
"I know you all have seen those images and video footage we had just flash on your screen's, you must be wondering what, and who are those clips for? hmmm my humble people, we too are still shocked about,such maligned incident, to cut the story short, people are still in shock of who those people are? some said they are real armed soldiers whom they might be drunk and did not know their direction, or are being influenced by someone, and some said they are frauds and bullies, cycling the whole city in order to scare people, while some said they are terrorist whom might bring an attack, and causes fear and chaos to the community people.
We surely are in dilemma, cos we don't know which one of them is telling the truth and who's lying, but all we know that, a committee is set for an investigation, and inshAllahu when the time comes, we shall update you on our findings, this is live news reporting, from yours as always, NEWS REPORTER, ZARA,U SHAFI'U, GLOBAL TV NEWS"
Duk wannan dogon bayanin, datayi tundaga farawarta harta gama DEEN bai cire ido daga kan madubi tv ba, asalima tunda ya kurb'i ruwa, sip d'in farko, bai had'iye ba, sai lokacinda ta idar da batun ta, shima ya had'iye tasa ruwan, yana wani b'ata rai tamkar wacce ta ambaci sunansa.
Jin ta kuma d'auko wani report d'in, daya shafi batun auren kuma, akan ko yanzu yaya yarinyar da akayiwa auren dolen zata karb'i batun.
Tsaki yaja tareda ajiye goran dake hannunsa sannan ya d'auki remote ya kashe tv gabad'aya yana mai fad'in, useless TV reporters, the love gossiping alot.
YOU ARE READING
RAUDHA
General FictionThis is a story of a young innocence soul , an asian young girl whom destiny or coincidence brought to nigeria into the northern part of the country . what is her name, where is she from, who are her parents ,and why was she found in a middle of no...