RAUDHA 5

5 0 0
                                        

💔❄️❤️❄️
      *RAUDHA PART 3*
         💔❄️💔❄️
*EPISODE 5*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*BARKA DA SALLAH*
*Not edited*
........................ Washe gari ranar daya kasance ranar dinner, ranar da kuma zata tare. ciki da wajen gidansu a cike yake da mutane.

RAUDHA amarya ansha kyau, duk da cewa da k'yar ta yadda akayi mata, tun abunda ya faru jiya, yau ta tashi musu a murd'e komai akace tayi saita ce bazatayi ba, idan kuma zatayin, na Gan daa zatayi, wato nason ranta.

B'angaren DEEN kuwa, baccin tayi masa wahala kwarai da gaske, banda juye juye yana tattauna harshensa, k'a
Kar'ashe dai yayiwa kanshi fad'a ya tashi  yayi alwala, haka ya raba dare yana ibada, har saida aka kira sallar farko.

Yayi alwala yayi sallah, yakoma yayi kwanciyarsa, baisan ya dad'e yana bacci ba saidaya farka yaji gidan ya kacame da hayaniya.

Yayi ta jan tsaki akai akai, ganin an takura masa, ya tsani hayaniya, gashi duk da cewa ya dad'e yana baccin amma da ciwon kai ya tashi.

Ya nufi bayan gida yana tangad'i, sai yaji ana buga k'ofar d'akin sa, da kamar zai share, sai kuma yaga rashin dacewar hakan.

Mamaki ne ya kamashi bayan ya bud'e k'ofar ganin SUDAIS da ABBAS atsaye.

Big bro! ko baka ganemu bane? SUDAIS ya fad'i ganin DEEN yayi tsaye yana k'are musu kallo, ABBAS yayi shigewarsa ciki yana fad'in kaidai idan zaka shigo, ka shigo wannan daga gani baya cikin rightful sense d'insa.

DEEN ya kama hannun SUDAIS suka shigo ciki yana fad'in, don't mind him bro, I'm so happy to see you, yaushe kazo? kuma kaida waye?

SUDAIS yace isowar mu kenan nida UMMI da SAFNA, DEEN ya tapping d'in bayansa yace good move!

ABBAS daya mik'e saman sofa ko booth d'in k'afarsa bai cire ba yace good damn bastard! i being calling you yesterday, amma kake ta declining calls na, ashe har kafara enjoying kanka, don't tell me tunda kazo kana faman squeezing d'in y'ar mutane ne.

SUDAIS yayi uhmm uhmm, DEEN kuma yace daf da kan ABBAS ya take masa guiwar k'afa yace ko me nayi da matata wannan ba ruwanka bane, idan kayi zuciya kayi auren kaima idiot!

ABBAS ya tashi zaune yana rik'e da k'afar don ba k'aramin zafi yakeyi masa ba, shege! kacigaba da sauke fushinka akanmu, insha Allahu, kanwarmu saita sanya kayi mata tsallen kwad'i.

DEEN dai bai kulashi ba, SUDAIS kuma yayita dariya, dama ba yau yasaba ganin dramar y'an uwanshi ba.

UMMI  an basu separate room, yayinda SAFNA na can d'akin HAJJA, HAJJA na zuba mata zance.

Dama an had'u ne da an dace, SAFNA ma ba baya ba wajen zuba zance, idan ka shigo ka ganta da HAJJA tamkar sun dad'e da sanin juna, shigowar Aunty SAUDAT ne ya katse musu hirar.

Aunty SAUDAT tabita da kallo kamar yanda itama take kallonta. kallon farko suke yiwa junansu, ita SAFNA tana hango kamannin SUDAIS awajen Aunty SAUDAT yayinda ita kuma take ganin kaminnin mahaifunsu awajen SAFNA, duk da cewa da yawa wad'anda suka san Aunty SAUDAT d'in suna fad'in SAFNA tafi kama da mamanta,yayinda wasu keyi mata kallon mai jini biyu ajikinta, wato ta wani b'angaren tana kama da Aunty SAUDAT, sannan ta wani b'angaren tana kama da baffansu.

Momy! SAFNA ta fad'a tareda tashi ta rumgume ta, for the first time zuciyar Aunty SAUDAT yayi rauni, for the first time tayi danasanin barin y'ay'anta jarirai batareda ta waiwayesu ba na tsawon shekaru.

Kece momyn mu koh? SAFNA ta fad'i tana mai k'ank'ame Aunty SAUDAT tamkar wata y'ar yaye.

Aunty SAUDAT bata iya bata amsa ba, banda kuka daya kwace mata, ta k'ank'ame SAFNA itama yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri tamkar zai fito waje.

RAUDHADove le storie prendono vita. Scoprilo ora