💔❄️❄️❤️
*RAUDHA part 3*
💔❄️❄️❤️
*EPISODE 3*
*STORY*
&
* WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**The unexpected guests 2*
............................ Bai direta a ko ina ba sai saman gadon su, wanda yana ajiyeta ya dalla Mata harara sannan yace kada ki bari na kuma kamaki, kin fita da irin wad'annan shigar, idan bahaka ba.Ta hayayyak'o masa cikin masifa, idan ba hakaba, sai me? me zakayi? nace me zaka iya yi?
Ya sanya hannu ya ficike rigar dake jikinta, wacce tashi d'aya ta tsage gida biyu duk kuwa da quality datake dashi, tamkar wacce ta dad'e tana shan ruwa.
Kan ta kaiga ankarewa, ya janyo ta da k'arfi ya had'e bakinsu waje d'aya.
Tsananin firgici da tsoro ya hanata yin kwakkwaran motsi, sai rarraba ido takeyi kafin ta fara k'ok'arin kwatan kanta.
Da kanshi ya janye jikin sa daga nata tareda mik'ewa tsaye yana wani had'e giran sama da k'asa, tareda kuma yin k'ank'an da idanuwansa da suka soma canza launi,ya kauda kai ganin cewa her physical body is tempting him, tunda daga ita sai bireziya ne ya saura ajikinta.
Yace kiyi k'ok'arin gwada yin hakan nan gaba, ni kuma zan nuna miki k'arshen rashin kunya, note this in your mind cewa zan iya yin fiyeda wannan ma, ako ina, koyaushe akuma gaban kowanene.
RAUDHA da takaicin abinda yayi ke cinta, ga kuma zafin dataji fatar bakinta na mata, yasanya ta fashewa da kuka tareda fad'in Allah ya isa min mugu kawai.
Harya kai bakin k'ofa zai fita ya tsaya cak tareda juyowa, arayuwarsa ya tsani ace masa Allah ya isa. domin shi akullum ya tsani ace shiya cuci wani, harta kai ga ya barshi da Allah.
Duk da cewa awannan lokacin tana jinta amatsayin wani guruwa, kanta na hayaki, but saida taji tsoron ganin idanuwansa da yanda take dad'a rinewa zuwa wata kalar, jijiyoyin jikinsa kuwa duk sun bi jiki sun fito rud'u rud'u dasu, tun daga kafad'unsa har izuwa saman kanshi.
Da k'yar ta iya hadiyar tarin yawun daya taru mata acikin lokaci k'ank'ani , ita da kanta ta soma tausayin kanta tareda hango irin situation d'in dazata shiga idan har wannan gabjejen daya doso ta, ya kaiga isowa inda take.
HASSAN!taji amon sautin muryar su daga falon ya tashi da wannan sunan daya kasance wani jigo ne babba agareta,wanda ko yaushe, ko a ina idan aka ambata, saita ji wani iri, idanu da kunne ta kuma bud'ewa tamkar mai tsammanin isowar wani sak'on gaggawa gareta, yayinda ta mance da gogan data tak'alo da fad'a har yake k'ok'arin cimmar mata batareda ta ankare ba.
Mammy! it's daddy, it's truly our daddy, he's alive! abinda kunnen ta ya kuma jiye mata kenan wanda ita da kanta batasan lokacinda tayi wani wawan tsalle ta dire k'asa hartana hankad'e DEEN batareda tasan ta aikata hakan ba.
Shi kanshi baisan dalilin daya sanya shi bata hanya ba, asalima gyara tsayuwar sa yayi tareda bin bayanta da kallo harta fice daga cikin d'akin.
Ya sanya tafin hannunshi ya shafo goshinshi har izuwa kanshi, trying to control himself, ya d'ago yana kallon k'ofar d'akin, tamkar mai jiran dawowarta, duk kuwa da cewa yasan abune mai kamar wuya ta dawo cikin d'akin, idanuwanshi ne ya kaiga wani y'ar k'aramar frame d'in hoton ta a manne jikin bango, daga ita sai wata y'ar short gown ja, sai wata bakar hula, wacce gabanta yayi kama da band sanye akanta, a tsaye take tana dariya, amma ko kad'an babu alamar tasan an d'auki wannan hoton, domin daga yanayin tsayuwar fuskarta da kuma yanda ta wani mik'e yatsun hannunta biyu ta juya su suna kallon k'asa (alamun fuck you).
Ga wanda yasanta, ya kuma san yasan halinta yana ganin hoton halinta irinta rikici, da neman fitina takeyi da wani ko wata yarinya
D'auka yayi tareda share d'an guntun k'uran dake kan hoton, k'urawa hoton idanu yayi tamkar yasamu wani sabon interesting abun, but definitely to him she's always new, with new new characters to display.
YOU ARE READING
RAUDHA
General FictionThis is a story of a young innocence soul , an asian young girl whom destiny or coincidence brought to nigeria into the northern part of the country . what is her name, where is she from, who are her parents ,and why was she found in a middle of no...