RAUDHA 8

1 0 0
                                    

❄️💔❄️❤️
      *RAUDHA PART 3*
        ❄️💔❄️❤️
*EPISODE 8*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

........................ Wak'ar RIHANNA the "Blinding lights" kawai ke tashi MEENA da AFNAN  ke ta tik'ar rawarsu bayan sun duba jamb result d'insu, kowacce taci above 200.

HAJJA dake ta k'ok'arin ganinta gyangyad'a sun hanata, ta fito rik'e da sandarta tana fad'in ni DIJE na birad'a da birbid'add'un yaran nan, yara sam basu san tarbiyya ba, yau zanga mai rabani daku agidannan.

Ke AFNANUWA! zonan gidannawa ne yazama kamar wajenda aka yankewa shed'an cibi. HAJJA ta fad'i tana mai lek'en d'akin, dukkanninsu babu wanda ya jita, sun k'ure sautin kid'an tamkar wani gidan gala.

Hakanne ya baiwa HAJJA danar k'arasowa batareda sun sani ba sai jin sauk'ar sanda suke ako ina, takan mai uwa da wabi. kowa ya fara cecen kanshi.

Bayan sun kashe ne AFNAN ta rik'e guiwar hannu kamar zatayi kuka tace HAJJA wai so kike ki nakasa ni agidannan kafin aurena. mutum da girmansa da hankalinsa sai ayita dukansa kamar wani d'an yaye.

HAJJA ta nuna ta da sandar hannunta, kiyi min shiru ko na dad'a miki wannan harsai naga hannun yana lilo, yara suna girma suna cin kai. duk cikinku babu wacce bazan iya kamawa na turmusa ba, ko uwarku ce yau tayi laifi kwakkwad'e ta zanyi. ballantana ku ni nama gaji da ciyar da gardawan mata irinku, iyayenku suzo suyi muku aure, kona badaku sadaka a masallaci kawai na huta.

Ta juya ta fice tana cigaba da fad'in, wannan fara mai siffar matan aljanun ma kad'ai ta isa ta kirawo min shaid'anu, basai kun addabeni da kid'e kid'en banza dana wofi ba.

Ke JUMMAI! yi maza kije d'akin yarannan ki kwaso min wad'annan gangunan shaid'an d'in. JUMMAI tabi umarnin HAJJA taje d'akin su AFNAN dasuka kuma kunna wak'arsu kamar basu aka gama yiwa kashedi ba, saidai yanzu sun rage sautin kid'an

JUMMAI tayi tayi dasu suka k'i bari ta kwashe speakun d'akin, AFNAN harda cewa ko HAJJA ce tazo da kanta bata isa mu bari ta kwashe ba, kuma babu abinda zata iya, abar mana abinmu atoh

JUMMAI ta isar da sak'on su ga HAJJA, wacce tayi k'wafa tareda fad'in bari uwarku tadawo gidannan yau, naga uban daya tsaya muku, saina sa an d'aura muku aure gobe goben nan, banzan halinku yasa duk baku sa,ar aure, yanzu ga takwara can gidan wancan sangamin, Allah kad'ai yasan irin izayar datake sha ahannun shi, tunda tabar gidannan watanni samada bakwai ne ko tara, JUMMAI dake kusada ita tana jera kula asaman tebur tace HAJJA wata hud'u ne! ke JUMMAI kiji tsoron Allah, yazakice wata hud'u bayan ana lissafin kusan shekara kenan daya tafi da y'ar mutane babu ko labari, babu zuwa babu aike, bamusani bama ko tana raye ko a mace sai Allah, ta k'arashe tana matsar kwalla.

JUMMAI tace HAJJA ay kuwa DEEN mutumin kirkine bazai tab'a bari wani abu ya tab'a RAUDHA ba.

Ke da,Allah rufe min baki, na lura gabad'aya kin fara zama munafuka, sam baki tareda ni yanzu, waima awani k'aulin kikasan cewa DEENU mutumin kirki ne, soja ne fa, gashi jinin ubansa gareshi, Allah yasa basuje sun maida yarinya baiwa ba. bana tantama izuwa yanzu RAUDHA tadawo kwarangwal tsabar lalacewa. Allah sarki baiwar Allah tuntuni nake godon wannan uwatata takaini wajenta naganta, amma tak'i sai waina ni take kamar funkaso, ta share d'an guntun hawayen dake idonta tareda kwalb'e majina tace cikin sanyin murya.

JUMMAI zo muyi sirri, JUMMAI ta matso kusa kamar yanda ta umurta, yawwa JUMMAI kinaji na, zan baki kud'i kiyi k'ok'ari ki nemo mana yardadden driver dazai kaimu chata tundaga nan kano har habuja, amma kada kowa JUMMAI tace amma HAJJA? ke da, Allah banason terere da waine waine idan bazaki ba, saina nemi mai kaini can atoh!

JUMMAI dai tace to, amma azuciyarta tana tunanin yanda zatabi ta b'ullowa HAJJA , su wanye lafiya batareda sun tafi wani waje ba.

Sallamar da akeyi ne ya d'auki hankalinsu gabad'aya, suka maida kallonsu bakin k'ofar shigowa.

RAUDHAWhere stories live. Discover now