RAUDHA 13

24 0 0
                                    

💔❄️❄️❤️
*RAUDHA PART 3
💔 ❄️❄️💔
*EPISODE 13*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAM NOOR*

*The Union*
.......................... Lokacinda DEEN ya dawo abuja bayan ya bar RAUDHA a asibiti, direct gidansu ya nufa, saboda kiran da baffa yayi masa na gaggawa gidan shiru ba kamar yanda yasaba zuwa yasamu ba
baiga ma'aikaci ko d'aya ba, DEEN yayi ta mamaki da zullumin ina suka shiga.

Har zai hau stairs yaji muryan mutane a kitchen, haka kawai yaji yana sha'awar lek'awa, mamakine ya kamashi ganin SUDAIS da SAFNA d'aure da apron sai faman kachal chala kitchen d'in suke, SAFNA ce ajikin gas tana sieving d'in wake. shi kuma SUDAIS na faman yanka albasa a choppimg board, sai hawaye yake yana dire k'afafu, SAFNA natayi masa dariya wai ragon namiji da hakan MEENA zata aureka duk ka sakwarkwance saboda yankan albasa. ya ajiye wuk'an ya juyo yana had'e rai, lallai sai yau na gane ba kya k'aunata SAFNA
ke! kinsan waye MEENA kuwa awajena, kullum burina nasamu angel d'in dazai tayani shawo kanta mu sasanta muyi aure, na rasa, and here you are again badmouthing me with badluck. ki ban haushi insa Yaya ABBAS nemo wata wallahi

SAFNA ta dokesa da ludayin hannunta, mugu to aniya bi aniya, SUDAIS ya dafe wajen ya fara kukan k'arya ganin DEEN tsaye a bakin k'ofa yana kallonsu. ya k'araso kusa dashi yana fad'in, yaya DEEN kaga SAFNA zata nakasa ni tun kafin na samu damar shawo kan my darling MEENA koh! DEEN yaja kunnensa d'aya yana fad'in so this small boy har ka fara soyayya da gaske? SUDAIS ya d'anyi k'ara yace yaya DEEN ay na wuci yaro, am almost 30 now and meyasa za,a bar SAFNA tana soyayyarta ni kuma sai ayita ce min yaro.DEEN ya sake sa ya kalli SAFNA yace where are the staff? SAFNA daba sabawa tayi da shiga kicin d'in sosai ba, duk tagama laushi ta kama k'ugu tace wayyo bayana, na gaji. SUDAIS ya hau dariya yace ay yanzu gidannan bamu da staff ko d'aya, baffa duk ya koresu, wai bai yarda da ko d'aya ba yanzu, saboda tunanin ko UMMI ta brainwashing d'insu. gashi yak'i yarda mu nemo wasu, yanzu dai kowa shi zai dinga yiwa kansa hidima, dama cook ne babban matsalar ya kalli SAFNA ya kuma tuntsirewa da dariya, BAFFA ya appointing mana new chief chef in the house, SAFNA yaya DEEN fa yana jin yunwa.

SAFNA ta b'ata rai, ta juya taci gaba da aikinta tana fad'in kaci gaba da abinda kaga dama, lokacinka ne SUDAIS, inace nice ke girkin, i would see to it babu abinda kasamu.

SUDAIS ya rik'o rigar DEEN da harya juya zai tafi, yaya DEEN kaji ta koh! yaya DEEN, wallahi SAFNA akwai rashin godiyar ALLAH nan fa yanzu nagama tausayinta harda yanka mata albasa, shine wai ni zata hana abinci. DEEN yace idan ta hanaka ma is not a big deal ay, as you said you are man enough to fend for yourself, so go and hustle, there are lot's of restaurant here in abuja.

SUDAIS ya b'ata rai yabi bayan DEEN da kallo, kafin ya juyo ga SAFNA da tayi masa gwalo, ya cire apron d'in jikinsa ya wurgeta dashi a fuska ya fice daga kitchen d'in yana fad'in mayya! sai ki cinye abincin ke kad'ai in zaki iya. ta kuma yi masa gwalo, oho dai.

Zaune akan darduma yasamu baffa, ya gaishesa kamar yanda yasaba, fuska sake ya amsa masa, har yana zolayarsa wai ya kamar shima yaje ya tarene acan kanon, kodai shima kayan shi za,a had'a masa.

DEEN yayi murmushin da ake cewa tafi kuka ciwo, yayi k'asa da kai batareda yace komai ba, baffa ya yayi murmushi sannan ya gyara zama yayi gyaran murya yace ya jikin Khadeejan DEEN yayi shiru yana tunanin wacece ma khadeeja? baffa ya kuma murmusawa domin ya gane DEEN d'in bai fahimcesa ba. lallai babana kanason HAJJA taci taran ka, sunan takwaran nata guda kake mantawa, DEEN ya d'an sosa kai, cikeda jin nauyi yace BAFFA naji ka kori ma'aikatan gidannan? baffa yace abinda hajiya tayi min yasa ban yarda da kowa ba na gidannan, tunda ta iya wannan makircin tsawon shekaru babu wanda ya ganota, suma tana iya siyansu su cigaba da yi mana zagon k'asa, kaga kenan anyi ba,ayi ba.

DEEN yayi shiru, azuciyarsa yana gano gaskiya a maganar baffa, UMMI fa? DEEN ya kuma tambaya, baffa ya b'ata rai yace na sauwak'e mata ta tafi, tareda ma,aikatan ta, na k'wace komai na dayake hannunta, hatta kyaututtukan gidajen danayi nata na kwace abina, taje can garinsu taci gaba cin tuwon amalarsu. DEEN yayi shiru kamar bazaiyi magana ba, sai kuma yace amma baffa hukuncin nan baiyi tsauri dayawa ba, baffa yace babana kenan ay ni idan ba don twins d'inka sun rok'eni ba, i woukd rather she rot in prison, da saina fi samun peace of mind. matarnan ta cuceni, matuk'ar cutarwa, tasanya na tsani SAUDAT matar kirki tsawon shekaru ina jin k'yamar abinda tayi acikin raina, kullum na tuno da yanda na ganta da shi sainayi danasanin aurenta, baiwar ALLAH kuwa ashe batasan komai ba, yanzu bansan yazanyi na shawo kan SAUDAT ta yafe min ba, domin cutar danayi mata tayi yawa, nima na biyewa b'acin rai na kasa binciken lamarin, sai yanzu na gano kaso saba'in cikin d'ari na abinda ya faru laifina ne. yanzu bansan yazanyi na gyara b'arnata na tsawon shekaru baa.

RAUDHAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt