RAUDHA 7

14 1 1
                                    


💔❄️❤️❄️
      *RAUDHA PART 3*
         💔❄️❤️❄️

*EPISODE 7*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*MAMAN NOOR*

.......................... Washegari RAUDHA na gani kwance a d'aki ita kad'ai tana bacci, sai wajen tara saura, kafin ta tashi, zama tayi tana mitsike idanu ganin yanda gari ya washe yayi haske batareda tasani ba. duk da cewa tayi sallar asuba d'azu da DEEN ya tasheta.

Tuno da batun Deen yasanya ta fashe da kuka tareda dirowa daga saman gado, sai gata ta kuma zubewa sharaf tamkar an watso ta, saboda yanda k'afarta ta kasa rik'eta.

Da rarrafe ta isa jikin k'ofar, ta murd'a tana cigaba da sharara kukanta tareda yab'o duk maganar dayazo bakinta, mugu, azzalumi, macuci, he betrays me, cheated me, and wronged me, ta bigi k'ofar da hannu da goshi, mugu i hate him, i hate him with passion.
tana gama kukanta ta bud'e kofar tana rararafe da niyyar ta wai lallai yau sai ta tafi auren ay badole bane atoh

To saidai tana fita tayi kicib',us da DEEN wanda shigowarsa kenan bayan dawowarsa daga wajen aiki.

Jakar hannunsa ya baiwa P A sa, shikuma da tun shigowar sa idanuwansa yake kanta ya iso har inda take zaune ta kasa motsawa don ganinshi da tayi.

Baice mata ko ci kanki ba, ya d'agata cancak ya bud'e k'ofa ya shigar da ita cikin d'aki, RAUDHA tayi ta wuntsil wuntsil da k'afafu tareda debe masa albarka, ita kawai ya sauketa k'asa

DEEN dai ko ajikinsa, baima nuna yaji abinda take ta fad'i ba,

Cikin bathtube na wanka taji an direta tayi tsalle tareda da kwalla uban k'ara zata fice daga cikin abun wanka wanda ruwan zafine dam acikinsa.

ya kamo kafad'unta ya maidata tareda fincike botiran gaban farar long sleeve d'in tareda wurgi da ita a gefe, dama itace  zalla ajikinta wacce daga gani kasan tashi ce.

RAUDHA ta sanya hannu ta k'ank'ame k'irjinta  tacigaba da rera kukanta wanda take jin a yanzu yafi komai yi mata dadi, bai kulata ba kamar yanda naga kamar ya fara ignoring dinta ne, saida tayi kukan ta tagaji, har saida ruwan yayi sanyi sannan ta tashi ta daura towel daya tareda lulluba dayan,tayi mamakin ganin yanda ta dad'a watsakewa tana iya tafiya.

Turus taja ta tsaya ganinshi da tayi zaune abakin gado yana danna wayarsa, ta hararesa tareda juyawa da sauri zata koma bayangida, don,t even try! you know what am capable of, cak ta tsaya tamkar an dasata tanajin zuciyarta nayi mata d'aci ji take datana da dama datazo inda yake zaune ta dannesa har sai ya kasa tashi, bata ko kalli inda yake ba taje gaban mirrow, mai ta fara shafawa tanayi tana hararansa ta mirrow, dubeshi kamar wani kamili mutumin kirki awaje amma cikin zuciyarsa bak'ik'irin, mugu kawai mai kan kwakwa.

What! taji ya fad'i yana kallonta, nine mai kan kwakwan? ta gwalo idanu tana kallon shi ta mirrow, ta kama bakinta da hannu wayyo dama a fili ta fad'a?

Sai kuma ta murgud'a baki azuciyarta tace an fad'a d'in k'arya akayi, k'aton kai gareshi, suma ce ke rufa masa asiri ay.

Unexpected taji an juya kujeran datake zaune, ya tsuguna daidai tsayinta tareda d'ago hab'arta ya k'ureta da idanuwan shi da ke kashe jikin mai kallo

Yatsan hannusa yasanya yana wasa dashi tun daga saman fuskarta har ya sauko saman wuyarta, RAUDHA ta kankame jiki tareda takurewa waje guda, jin yanda hannunsa ke sauk'a izuwaga kan k'irjinta, tayi saurin sanya hannu ta k'ank'ame towel d'in, ta kalleshi da idanuwanta da suka soma tara kwalla, yaya please kayi hak'uri ka barni haka nagaji, ya rik'e hannunta data rik'e towel d'in dashi yana dad'a k'ureta da lumsassun idanunsa. yayi k'asa da murya yace, da gaske kin fara karaya? i thought you are still strong and bold. ta fashe  da marayan kuka  tace nifa bada kai nayi maganata ba, i was just talking to myself.

RAUDHAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant