💔❄️❤️❄️
*RAUDHA PART 3*
💔❄️❤️❄️
*EPISODE 6*
*STORY & WRITTEN*
*By*
*MAMAN NOOR*
*Not edited*
*BARKA DA SALLAH*
...................... Washegari da wuri ta tashi saboda baccin datayi da wuri, mamaki ne yakamata ganinta acikin d'akinta, ta mitsike ido trying to remember what happened yesterday.
Wanka taje tayi, ganin b'ata lokaci ne tunanin Deen da abinda zai iya aikatawa, abinda tasani shine batada lokacin shi ato.
Yau kam wankar k'ananun kayanta tayi, wato shigar doguwar blue jeans da farar riga, bata sanya dankwali ba kamar yanda tasaba, sai band kawai tasaka tareda sako sumarta ta tsakiyar sa, duk da cewa bata da tsayin suma but tsantsi da kalarsa wanda ya kasance yellow ya dad'a haskata, Alhamdulillah tayi kyau sosai.
D'akinta ta gyara ta share, kafin tafara jin cikinta na k'ugin yunwa, tashafa cikin da hannu, tana mamakin abinda yasanyata jin yunwa, itada sai tayi kwana biyu bataci wani abin kirki ba acikinta, sannan ga uwar kazar da akayi mata d'uren dole dashi jiya.
Ta fito sad'ap d'ap kamar b'arauniya tana dube dube, sai addua take kada Allah ya had'ata da wannan fitinannen.
Saida tazo tsakiyar d'akin saita tsaya cak, hannunta acikin bakinta, ko ina kicin d'in yake ma oho?
Yau dai tayi kasalandar bubbud'e labulayen falon, na farkon wanda ta fara shiga dak'ine amman kayayyakin ciki basuyi kamada d'akin daza,a zauna aikinsa ba, wato kamar store yake amma tarin kwalaye ne acikin
Ta janyo k'ofar ta kulle, tareda yin gaba, ta bud'e d'akin dake gefenta na na dama opposite wancan
Shima a hankali ta bud'e without making a single noise. wannan kam dak'i ne, d'akin ma ba k'arami ba, da kamar bazata shiga, me ya canza mata ra,ayi ne oho🤷
Tafi minti biyu a tsaye, tana k'arewa d'akin kallo, ta girgiza kai, ammafa d'akin nan yayi kyau, kamar ma yaso yafi nawa, ko dai nan zan dawo ne, gaskiya daddy nasona d'akuna dayawa duk ni kad'ai, taje kusada gadon
Wow! an Italian bed, ta zumb'ura baki, but na d'akina kamar ba Italian bace, gaskiya nafison wannan, tayi supa ta kwanta harda wani lumshe ido, i would just sleep anjima sainaje nayi girkin.
K'arar bud'e k'ofa ya sanya ta tashi ta bud'e idanuwanta tas a wajen kof'a tana kallo
DEEN da fitowar shi kenan daga wanka d'aure da towel ga kuma wata k'arama dayake shashare ruwan sumarsa da ita, baiyi zaton tana d'akin ba, tunda yasan shi kad'ai ne a d'akinsa.
Don haka yana isa wardrobe d'insa ya ciro boxers d'insa, RAUDHA da tayi mutuwar zaune tunda taga DEEN ta kasa ko motsi, zuciyarta banda bugu fat fat babu abinda yakeyi, wanda tarasa dalilin da duk lokacin da zatayi arba da Deen sai taji bugun zuciya, yanzu don Allah me ya kawota d'akinshi? itada take neman hanyar guje masa ko ta halin k'ak'a but here she is like a fool, ta kawo kanta.
Unfortunate to her ta hango Deen na k'ok'arin sake towel d'insa k'asa, ay kuwa ta daka tsalle tareda ihu, na shiga uku mamina, b'atan hanyace wallahi nayi gamo batareda niyya ba, wayyo batanan na biyo ba.
harta fice daga d'akin idanuwanta na rufe k'am k'am,ta bangaje shi tayi waje a d'ari hartana buge k'afa ajikin kof'a.
Ganinta dayayi a d'akin, da wani ihunta bai sanya shi jin ko d'ar ba, baima damu da wani kwaroroton datakeyi ba, mamakinsa shine mai yakawo ta cikin d'akin sa, ko dai wani abun takeso? ya kad'a kai tareda cigaba da abunda yake, azuciyarsa kuwa cewa yake,
this girl won't seem to be amazing him, she's a real defination of drama a queen.
Bayan ya gama shiryawa cikin shigar kananar kaya kamar yanda yasaba, ya fito direct d'akin ta ya nufa saidai a kulle yasamu, wanda ke nuna rufewa tayi.
Key naga ya dauk'o daga d'akinsa, yazo ya bud'e, a kwance yasameta tana waya, sai turo baki take, ko me ake ce mata oho, folding hanneyansa yayi a k'irji yana k'are mata kallo.
ESTÁS LEYENDO
RAUDHA
Ficción GeneralThis is a story of a young innocence soul , an asian young girl whom destiny or coincidence brought to nigeria into the northern part of the country . what is her name, where is she from, who are her parents ,and why was she found in a middle of no...
