💔❄️❄️❤️
*RAUDHA PART 3
💔❄️❄️❤️
*EPISODE 13*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*......................... Shirye shiryen biki ya kankama, ta kowanne b'angare kowa nata faman ganin yayi iyakan k'ok'arin sa don ganin a fita kunyar jama, a.
Amare SAFNA da MEENA suma dai ba,a barsu a baya ba, duk da cewa MEENA na baya baya da batun, acewarta ita dai har yanzu zuciyarta bata aminta da auren ba.
Wai tana tsoron auren SUDAIS yazo ya wulak'anta ta kamar yanda Yaya DEEN yake wulak'anta RAUDHA yanzu. shiyasa bayan har yanzu SUDAIS ya kasa gane kanta, shi tsoronsa ma kada ta canza ra,ayi tasa a fasa auren, dama ta fad'a masa ranar da aka shirya auren yasanya wa ranshi bata aminta da batun auren ba, tana iya fasawa akowanne lokaci.
Gefen su HAJJA kuma, tana nan ita da RAUDHA da ta dauk'i damuwar duniya ta d'orawa kanta, gabad'aya duk ta rame, kullum kuka da magiyar a hana Yaya DEEN k'ara aure.
Saidai da alamu korafinta baya karb'uwa , duk gidan babu mai goyon bayanta sai HAJJA, ita kam ta kafa ta tsare ala lallai sai sun maka DEEN a kotu.
Sau biyu tana aiken AFNAN wai taje ta karb'o sammaci a babban kotun cikin garin, AFNAN bata musu, saidai ko sau d'aya bata tab'a zuwa ba, saidai tayi ta mata k'aryan taje sunce a jira za,aji sak'o.
RAUDHA kam bata dauk'i hakan da HAJJAn keyi ba, amatsayin wani mataki ba, kullum kwana take tana tashi da tunanin hanyar dazata bi ta warzaga batun auren Yaya DEEN, there's no how zata bari ayi wannan aure, wato d'an gwal ya aureta by fire by force, ya rabata da dukkanin jin dad'in ta, and then boom! he wants to be happy alone, how selfish of him.
Gashi tunda ya tafi almost a month ko sau d'aya bai kuma dawowa ba, saidai yayi kira shima awayan AUNTY SAUDAT ne zata baiwa MEENA ta kawo wai yanason yaji muryan baby shi.
Most of the time RAUDHA kan kori MEENA ne da wayar tayi ta masifar wai za,a tashi yaro yana bacci.
Akwai ranar da tazo da wayar bata saka shi a hold ba, kuma yana handsfree, sai yaji tana masifar a maida wayar, salon gulma wai baby ne za,ayi waya dashi tsabar son asani, to bama so, yaje can ya k'arata shida zombie amaryansa.
DEEN yayi dariya har kana iya jin sautinsa ya fito, she's not a zombie oo my jealous uwar gida, she's a very beautiful princess, ay kuwa RAUDHA tamkar jira take ta hau shouting cikeda masifa ta cikin wayar, i said it, and i would say it again, she's a zombie! zombie! zombie! and mind you am not jealous, ni bandamu bama ko zakayi aure ko me zakayi, it's your own cup of tea, all i know shine i won't let you be happy by getting another wife, kamar yanda ka hanani jin dad'in auren masoyi na, haka nima zan hanaka auren wacce kake so,that is the only thing that would make me happy, naga duk munyi biyu babu, you get it.
Tana gama fad'ar haka ta danna red button ta kashe wayar sanna ta nunawa MEENA k'ofa, ki mayar wa AUNTY wayarta, kada ki kuma kawo min don zan iya fasa shi a goshinki.
MEENA tace haba Aunty RAUDHA, ni yanzu ya kikeson naje nacewa Aunty bazan kuma kawo miki waya ba, kinsan i can't do that, RAUDHA ta ture ta waje da k'arfi tana fad'in wannan kuma damuwarki ne ba tawa ba, oya go! go out of my room.
Haka RAUDHA tazama masifaffiyar dole, abu ba na fad'a ba zata maidashi fad'a, komai hasala ta yakeyi, ta maida kowa na gidan enemy ta, hatta HAJJA dake goya mata baya, bata tsira ba.
Lokacinda ta cika wata biyu da haihuwa, hakan yayi daidai da sauran ranakun bikin kwana biyar, gida har ya fara cikada bak'i, na birni dana k'auye.
Itadai RAUDHA ko kallo basu isheta ba,idan taga AFNAN ta shigo tana rawan kai, da bada labarin anata kaza da kaza saboda bikin cewa takeyi nidai yanzu agidannan banida mai sona, kowa ya wanke fuska yana rawan k'afa akan auren karere, auren cin amana.
YOU ARE READING
RAUDHA
General FictionThis is a story of a young innocence soul , an asian young girl whom destiny or coincidence brought to nigeria into the northern part of the country . what is her name, where is she from, who are her parents ,and why was she found in a middle of no...