RAUDHA 10

2 0 0
                                    

💔❄️❄️❤️
*RAUDHA PART 3*
     💔❄️❄️❤️
*EPISODE 10*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

........................... Yanda naga yanata faman kai komo atsakiyar falon sai faman huci yake had'e da kad'a kai dake nuna tsantsan tashin hankalin dayake ciki nasan da wani abu a k'asa. d'akin ya d'auki shiru tamkar babu wani mahaluk'in mai rai acikinsa sai shi.

But tsayuwa waje d'aya dayayi tareda nuna yatsar sa asaitin wani da nima sai yanzu nake ganinshi ya tabbatar min da ba shi kad'ai bane acikin d'akin kamar yanda nayi zato.

Duk laifinka ne barrister! duk kai ka janyo mana afkawa cikin wannan matsala da muke ciki.

BARRISTER dake zaune yanata faman kad'a k'afarsa d'aya dake saman d'ayan ranshi shima a dagule yace kai ALHAJI BUSHASHA ya kake magana kamar nine na sanya wad'annan yara su bibiyi rayuwar mu, naga dai d'anka shi ya fara shigar damu into this mess, daya nace akan wannan yarinyar da kaima ka goya masa baya, k'arshe kuma ta b'are zaka zo kana min kumfar baki.

ALHAJI LAWAN ya dad'a tunzura da kalamam BARRISTER yayi wani kukan kura ya d'aga shi can cak daga kan kujeran dayake zaune, dama BARRISTER ba wani aukin jiki ba, sai aukin tsayi da shegen baki.

Barrister kafi kowa sanin wanene ni, kasan yanda nakeyi ga duk wanda ya nemi tak'alata, ko kuma yayi k'ok'arin cin amanata. kar ka yarda kayi mak'iyi dani, kasan banda kyau.

Bushasha sake shi muyi magana, kaima JAZULI ka iya bakinka, ALHAJI LAWAN ya sake shi yana hararansa, ya juyo gefen wanda yayi magana ya zauna suna facing d'in juna, sai wani huci yake shi kad'ai.

Ungo nan kasha wannan, ko zakaji sanyi kafin muyi maganar. ya karb'i goran ruwan babu musu, ya kafa kai ya shanye tas, sannan yayi wurgi da goran acan gefe.

Komawa yayi ya jingine bayanshi ajikin kujeran, ya lumshe idonsa yana maida numfashi.

Na kira wannan ma,aikacin NDLEA d'in daya kama mana kayayyakinmu a hannun su reza, amma yak'i d'aukan wayana, sannan na kira ASP dasuka kwashe ma,aikatanmu na masana,antar giyar mu shima yak'i karb'an tayina, kar'she na koma ga custom d'in da aka had'a baki dasu wajen kama mana kayanmu dake shigowa da haramtacciyar hanya. sunce saidai naje nayi magana da ogansu, dana tambayesu dalilin yin hakan, sai suka ce shine mai ikon fad'a aji awajen, shike bada ikon ayi ko a bari, don haka saina je wajenshi.

Nikuma dana zauna, nayi amfani da y'ar k'aramar hankali na, sai na gano cewa, zallar siyasa ce, lumbu lumbu suke son yi mana domin gano ko mu su waye, don haka samun mafita ta wad'annnan gefe, yiwuwarsa k'alilan ce.

Yanzu tunanin danake shine ma,aikatan company mu da aka kama, yawancinsu, k'aramin kwakwalwa garesu, ina tsoron kada su ranting d'in mu out idan sukaji maza.

Wannan karon ALHAJI LAWAN ya bud'e idanunsa, da tuntuni bai bud'eta ba, sai kayi tunanin ma da baya jin komai da ake fad'a.

Kallon gefen da BARRISTER yake zaune, yanata faman hargitsa wasu takardu yayi, sannan ya dubi ALHAJI TIJJANI yace ban tunanin akwai wanda yasanmu acikinsu, kasan dukkanninsu JAZULI suka sani,kuma koda wanda yasanmu acikinsu basuda k'warin guiwar tonawa ALHAJI LAWAN BUSHASHA asiri, domin k'arfin ikona tafina matsiyatan nan masu kiran kansu da jami,an tsaro,kai ko shegen yaron nan naka daya jawo mana wannan asara, sai na kawar masa da dukkannin farin cikinsa, zan sanya shi cikin k'uncin da ko mak'iyinsa idan ya kallesa sai ya tausaya masa ba,a ja da BUSHASHA domin duk wanda yayi kuskuren shiga gonata
. wallahi sai naga bayanshi da kafatanin danginshi gabakid'aya.

ALHAJI TIJJANI ya gyara zama yayi y'ar danne danne awayarsa, bugu biyu aka d'auka, ya ake cikine agogo har yanzu baku baro asibitin bane?

Bansan me aka fad'a masa ba, naga ya kashe wayar yana mai jan doguwar tsaki, Alhaji lawan yace wai me agogon ya fad'i naga fuskar ka ta dad'a sauyawa.

RAUDHAWhere stories live. Discover now