💔❄️❤️❄️
*RAUDHA PART 3*
💔❄️❤️❄️
*EPISODE 4*
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**Not edited please 🙏*
*BARKA DA SALLAH TO YOU ALL*
................................ RAUDHA kwance tana rama baccin da bata samu damar yi ba a daren jiya, kasantuwar raba dare datayi tana kuka, duk da cewa HAJJA na jinta, sai bata kulata ba, saboda tasan halin RAUDHA da kafiya ga rashin hak'uri, idan ta biye mata awannan daren, k'arshe saidai su kwashi y'an kallo.RAUDHA da bata samu damar rintsawa ba, saida dare ya raba, shiyasa har yanzu da agogon bango yake nuna k'arfe bakwai saura tana kwance, HAJJA dake zauna saman darduman sallarta, sai faman zuba idanu take taga ta tashi amma shiru kake ji, wai malam yaci shirwa.
Mik'ewa tayi tana mita, ni dije! wai dama haka yarinyar nan ke kwanciya ta hangame baki tundaga silsilar dare har izuwa fitowan rana bata bar gado ba
Ta iso ta bubbugi k'afafunta da carbin hannunta, maza tashi kafin na tara miki jini a muk'amik'i.
RAUDHA ta tashi zaune tana mai mitsike wajen da carbin yasameta, tareda d'ora hamma akai akai.
HAJJA ta koma wajen zamanta tana fad'in, nidai kada ki cinye ni ato, wannan hamma ko mai shirin had'iyar giwa.
RAUDHA ta kuma jan bargo tayi kwanciyar ta, HAJJA ta kuma hayayyak'o mata tana fad'in idan bata tashi ba, saita kira me gadi ya dauketa cancak ya kawota gabanta, tayi mata d'an banzar duka, ta kuma biyata ladanta, tareda yi mata bayanin dalilin daya sanya ta har wannan lokacin bata tashi tayi sallah ba.
Bata cewa HAJJA uffan ba, ta tashi tayi shigewarta bathroom, domin tasan batada amsar baiwa HAJJA, and ko da tanada dashi ma amsar bazaiyi wa kowa dad'i ba, ballantana HAJJA da ba,ayi mata gwaninta.
Ay kuwa ahakan ma bata tsira ba, tana ji HAJJA na magana a keyarta, adai gama yimana feleken tsiyar,kwanan nan za, ayi mana maganin mutum, ehe!
Shigowar daddy yasanya ta yin shiru, tana mai fad'in, kai daya kamata ace kana can kwance kana bacci, me kake nema anan, yayi murmushi ya zauna a k'asa tareda cire hulan hood d'in dake kanshi.
Ya gaishe ta tareda fad'in ay ni tuni na watsake tun jiya, ganinki ma ya wadatar dani, ta tab'e baki tace kai biyu na hane ka da fadar magana zur zur kamar zawo, amma babu amfani.
Maganar HAJJA ta kuma bashi dariya har yana kyakyatawa yace kai HAJJA, ta juyo, ta harare shi tana fad'in ay kasan nasaba karya,tunda gadon gidanmu ne.
Yayi k'asa da murya, yunwa ce ta tashe ni, itama HAJJA saitayi k'asa da nata muryan, aw to da sai kayi magana tun farko, da tuni na sanya Jummai ta tuka maka tuwo da ajiyayyiyar miyar kukata da taji man shanu tayi zoy, ba,a baiwa yaro mai kuiya.
Ya d'an yamutsa fuska yace gaskiya yanzu nafi bukatar mai d'an ruwa ruwa mara nauyi, ballantana yanzu da banason timbi kwata kwata.
HAJJA ta kuma hararansa, saidai batace komai ba, Jummai ta kira, ta tambayeta me za,a samu na karin kumallo mai d'an ruwa ruwa, Jummai tace eh to, aunty hussaina ta sanya rose da Margaret soya chips da kwai, sai farfesun kayan ciki datace suyi.
HAJJA ta tab'e baki tace jeki Jummai, indai biyu ne zasuyi abinda yafi haka ma, shegen iyayi ne dasu, dama kullum bakinsu d'aya.
Shiyasa yanzu sam na dena ganin laifin wannan y'a, yo gado ba karambani ba.
Ta kalli gefen band'akin tana yamutsa fuska, ita kuma uwar me ya zaunar da ita acikin band'akin kuma oho?
*****
Ta katse wayar ta juyo tana murmushin da mai hankali yasan ba lallai yakai cikin zuciya ba, tace son i thought hutawa kace zakayi? what are you doing here?
YOU ARE READING
RAUDHA
General FictionThis is a story of a young innocence soul , an asian young girl whom destiny or coincidence brought to nigeria into the northern part of the country . what is her name, where is she from, who are her parents ,and why was she found in a middle of no...