FITA TA HUƊU

61 7 1
                                    

245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS

  
     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA HUƊU

  Da gudu ta dawo ɗakin data bar Nabeela ta tadda tana inda ta barta a kwance bata numfashi.
   Ruwa ta ɗauko mai sanyi ta yayafa mata  amma kuma shiru, da alamu numfashinta ya yi nisan zango.
  Ita kaɗai ta ke safa da marwa a ɗakin, kanta ya cushe da al'amarin da ke faruwa da Nabeela.
  Ta san shaƙuwar da ke tsakanin yaran, tasan Nabeela na son Nabeeha so na gaske, kamar yadda suka yi muguwar shaƙuwa da junansu, duk da sun rabu a lokutan baya, hakan ba yana nufin sun yi rabuwa ta har abada ba ne.
  Hawaye ne ya sake gangarowa a kan fuskarta a lokacin da ta ke ɗora idanuwanta a akan Nabeela da bata numfashi. Tana tuna wani lokaci a baya idan da ace Nabeeha na raye to tabbas da tana kusa da ita a kwance itama.
  _'Ubangiji baya barin wani dan wani. Yau babu Nabeeha a duniya, ga Nabeela a cikin wani hali. Ya Allah kar ka jarrabe ni da abin da ba zan iya ɗauka ba.'_ Ita kaɗai ta ke maganar hawaye ba gangarowa a kan idanuwanta.
  Kafin daga bisani ta ɗauki wayarsa ta fara jujjuyata, dasa wa zata kira ta yi, daga ƙarshe dai ta kira wayar babban yayan Nabeeha.
  Tun kafin ya yi magana ta fara magana "Malik ka zo da kayan aikin ka, ka duba Nabeela. Bata numfashi."
  Daga ɗaya ɓangaren shima Malik ɗin ya amsa a ruɗe, yana tashi daga wajen zaman makokin.
  Kai tsaye ɓangarensa ya wuce a gidan mutane na ta masa ta'aziyya kai kawai yake gyaɗa musu, da sassarfa yake tafiya, ya ɗauko ɗan ƙaramin akwatin agajin gaggawa ya haura sama, inda Momy ta sanar da shi.
  Sai da ya ƙwanƙwasa ƙofar Momy ta bashi izinin shiga kana ya shiga, ya sameta ta rafka tagumi.
   "Yauwa Malik. Dan Allah ka taimaka min kada na sake rasa Nabeela itama."
   Kai ya gyaɗa da ƙyar ya buɗe bakinsa saboda yadda yake masa nauyi "Ki kwantar da hankalinki Momy in sha Allah zata samu lafiya."
  Sai da ya yi mugun ƙoƙari kafin ya faɗi hakan, idanuwansa sun ciko da ruwa, ganin Nabeela a kwance.
  Wani shuɗaɗɗen fafayin rayuwarsu na faɗo masa.
   
**
Flash Back

   _A guje suka fito yana biye da su yana kiran sunan su 'Idan har na zo na same ku sai jikin ku ya gaya muku.'_  
    _Babu wadda ya saurara masa, asalima kamar yana zuga su ne 'Sai Momy ta gani, dama kana ta damun mu da Jann mun zata za mu ganta kamar ɗawisu ashe ashe!' Nabeeha ta faɗa tana kwashewa da dariya._
   _Nabeela na tayata dariyar tana kai mata hannu suka tafa 'Jann' Ke dama kina jin sunan kin san injin malkaɗe za a gani.' Nabeela ta faɗa a lokacin tana kwashewa da dariya itama._
    _Cikin jin haushi ya nufe su zai dake su, Momy ta tare shi tana ƙoƙarin ƙunshe dariyarta "Kai haba da girmanka sai ka taɓa min yara, Malik. Mene ne dan suna yaban Jannat ɗin naka, tun da kai kana da kyau ai shikenan ba sai ta yi ba itama. Ni dai suruka mai kyakkyawan hali na ke so, wadda zata kula min da 'yan matana."_
   _Yana iya tuna lokacin da kunya ta sa shi ya juya da sauri, yana kuma jin ihunsu a bayan Momy suna gwalonsa._

    ****
Hawayen da ya cika idanuwansa ya yi saurin sharewa 'Hikimar Ubangiji na da girma, tana kuma da yawa. Banda haka ko a mafarkinsa bai taɓa tunanin mutuwa zata ɗauke musu Nabeeha ba. A lokacin da duk mafarkan rayuwarta suka cika.' A daddafe ya sawa Nabeela jonin ruwa sannan ya fice a ɗakin bayan ya sanarwa Momy ta kwantar da hankalinta, zata dawo daidai.
  Ta yi suma ne saboda firgici da tashin hankalin da take ciki.
   Shi kansa yasan shaƙuwar da ke tsakanin Nabeela da Nabeeha abu ne mai ɗaga hankali mutuwar ɗayansu, amma kuma al'amarin Allah komai ya yi daidai ne.

    *****
BAYAN SA'A GOMA.

   A hankali take buɗe idanuwanta, tana jin nauyin da kanta ya yi har a lokacin bai ragu ba.
  Idanuwanta ta sake lumshe sai kuma ta ji bugawar agogon da ke ɗakin yana ƙidaya lokacin da suke ciki, ƙarfe uku na dare.
  Hakan ya sa ta tattara duk kuzarin da take tunanin tana da shi, ta miƙe, tana ganin jonin ruwan da ke jikinta, wadda ya kusa ƙarewa.
   Idanuwanta ta lumshe tana son sake yin wani sabon tunani, sai dai babu komai a kanta, duk abin da take son tinanowa ta kasa tunawa. Asalima kanta ne ya mata dimm tana jin wani ƙaran abu kamar an kaɗa ƙararrawa yana bugawa a cikin kan nata.
   'Me ke faruwa da ni?' Ta tambayi kanta, kafin ta kai kallonta a tsakiyar ɗakin da yake cike da haske kamar rana.
   Ɗakin ta shiga ƙarewa kallo tana nazarin ko ina ne, har idanuwanta ya sauƙa a kan hotonsu ita da Nabeeha suna maƙale da juna suna dariya.
    Ƙuri ta yiwa hoton tana ƙara ɗora idanuwanta a kan Nabeeha kamar mai karanto yanayin da suke ciki a lokacin.
  A hankali ta tashi a kan ƙafafuwanta tana jin suna rawa kamar ba za su iya ɗaukan ta ba, da ƙyar ta tattara kuzarin da ke jikinta ta cire allurar ƙarin ruwan, jini ya gangaro ta hannunta, sai dai bata ji a jikinta jinin na sauƙa ta hannunta ba, kamar yadda bata ji zafin zare allurar ba.
  Da ƙyar ta isa gaban hoton nasu tana ɗora idanuwanta a kan Nabeeha.
  "Har yanzu na gaza yarda cewar kin tafi kin barni Nabeeha! Har yanzu gani nake ba gaske ba ne! Me yasa sai a wannan lokacin?" Ta yi maganar tana ɗaukan hoton da ƙanƙame shi a ƙirjinsa, tana fashewa da kuka.
     "Ban san me yasa mutuwa ta tsallake ni a karo na biyu ba? Ban san me ya rage min a duniyar nan ba da har yanzu nake raye? Ashe abubuwan da na aikata ba su isa su kashe rayuwata ba? Kaicho! Kaichona!" Ta ƙara fashewa da kuka tana jin inama ace numfashinta ya yi fitar burzu ya bar ƙirjinta.

     Turo ƙofar da aka yi da kuma maganar Momy da ta sauƙa a kunnuwanta ya sa kukanta ya ƙara tsanannta "Subhanallah! Nabeela ya daga farkawa sai kuka kuma?"
  Momy ta ƙaraso tana ɗagata da rungumeta.
  "Kuka baya taɓa zama sauƙi ga matsala Nabeela. Wadda ya mutu ya riga ya mutu, baya buƙatar komai da soyayya daga garemu face yi masa addu'a. 
  Nabeeha ta tafi ta barmu, amma bata bar mu ba har sai da ta tabbatar mana cewar zaki maye mana gurbita, za ki rayu fiye da ita, zaki zama abu biyu a cikin ɗaya.
  A yanzu kukan ki na tada min hankali Nabeela, ina jin tsoron kada wani ciwon ya kamaki kema ki sake tafiya ki bar mu.
  Yau kwanaki uku da mutuwar Nabeeha amma babu abin da kika ci a cikinki, baki bawa zuciyarki da kanki damar nutsuwa kin samu zaman ta'aziyyarta ba. Baki mata addu'a ba ko da sau ɗaya.
  Wannan ita ce soyayyar da kike mata? Wannan shine ƙawancen na ku?"
  Kai Nabeela ta girgiza hawaye na gangarowa a idanuwanta.
   "A'a Momy zan mata, yanzu zan mata, ina son ta Momy!" Ta na maganar tana maimaitawa tana girgiza kanta.
  Ruƙo hannunta Momy ta yi "Ki fara cin abinci kafin nan?"
   Kai ta girgiza har a lokacin hawaye na gangarowa a idanuwanta "Ba zan iya ci ba Momy. Kada Nabeeha ta yi fushi da ni. Ki bari na mata addu'ar!"
  Ta yi maganar tana langaɓar da kanta, hawaye na zubo mata a idonta.
  Tausayi ne ya kama Momy, tana jin hawaye na taruwa a idanuwanta dole ta sakar mata hannun tana ganin yadda take tafiya kamar mai koyo.
  Har ta shige toilet ta ɗauro alola ta shimfiɗa abin sallah.
  Lokar kayan su da Nabeeha ta buɗe ta ɗauko Hijab ta tada sallah.
  Ita kanta bata san raka'a nawa ta yi ba, balle Momy da take zaune tana ganinta, tausayinta duk ya gama cika mata zuciya.
  
   Kasa jurewa ta yi ta koma kitchen ta haɗo mata shayi mai kauri da indomie, ta nufo ɗakin nata, tana ganinta zaune a kan abin sallah hannunta a sama tana addu'a hawaye na bin fiskarta, sai shessheƙar kuka ta ke...

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now