https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
ƘAWATA CE! 💕
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
©OUM-NASS
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
FITA TA TAKWAS
"Adadin wani lokaci zaki ɗauka kina faɗar kalma ɗaya Nabeela? Har zuwa wani lokaci zaki ɗauka kina zubar da hawaye a kan fuskarki? Ashe ba zaki sawa zuciyarki salama da haƙuri a kan rashinta ba?" Momy ta faɗa tana furzar da huci a fuskarta.
Zuwa yanzu ta fara ƙosawa da kukan Nabeela, kamar yadda ta ƙosa da yadda take ƙoƙarin raunata mata zuciyarta.
Nabeeha ta bar duniyar, ta san kuma sun yi rashi babba, rashin da ba za su mayar da gurbinsa ba har abada. Sai dai kuma yawan kukan kamar butulcewa ni'imar Allah ne, kamar yin kokawa ne da ƙaddara a kan abin da ta zaɓar maka na rayuwarka.
"Har abada Momy! Tsawon har abada zan ci gaba da kuka a kan mutuwar Nabeeha. Saboda nasan har abada ba zan samu madadinta ba, ba zan samu mai sona da gasken gaske kamarta ba."
Kallonta Momy ta yi, sai kuma ta girgiza kanta tana jan ƙafafuwanta da shigewa ta bar mata wajen, ta sani idan har ta ci gaba da tsayawa a gaban Nabeela to itama zata yi abin kunya ne.Fitarta ɗakin ya bawa Nabeela damar ƙara rungume yaran, tana jin a yanzu su kaɗai ne abin da suka zama ƙauna a gareta, su kaɗai ne za su zame mata inuwar gajimare a rayuwarta a yanzu, zata cika zuciyarsu da ƙauna, zata kuma tsaya musu fiye da yadda Ishaq ya tsayawa Khadijatu a cikin Inuwar gajimare.
Bata san adadin lokacin da ta ɗauka a hakan ba, sai dai ta ji numfashin yaran na sauƙa a kan kafaɗarta a hankali, sun kuma daina yin ƙananun surutun da suke yi. Hakan yasa ta ɗago su taga sun koma luuu saboda baccin da ya ɗauke su.
Murmushi ta yi wadda ya haddasa lotsawar kumatunta, jerarrun haƙoranta da suke ɗauke da siririyar ushirya suka bayyana. Sai bayan ta yi murmushin kuma ta fara tambayar kanta 'Ashe zan iya sake murmushi?'
Sai kuma ta girgiza kanta 'Wannan ba rayuwata ba ce, ta Nabeeha ce da ta bani sadakarta!' Ta yi maganar tana ɗaukan yaran dukansu ta kwantar da su a kan gadonsu.
Sai kuma ta ji ba zata iya tafiya ta barsu ba, hakan yasa ta kwanta a gabansu tana kallonsu tana ƙura musu ido kamar idan ta ƙifta idanuwanta zata ga basa kusa da ita.
Ta daɗe tana jin labarin ƙawaye da kuma cin amanar ƙawance da ake yi a duniya. Kamar yadda ta daɗe tana jin tambarin butulci me yawa a tare da ƙawaye, kamar dai yadda ta gina tubalin tata rayuwar da son kai, son ababen ƙawa, son morewa rayuwa da jin daɗi. A ƙarshe kuma sai Ubangiji ya cika mata burinta, ya bata fiye da abubuwan da ta yi tunanin mallakarsu, ya bata abin da bata taɓa hasashen mallakarsa a cikin ƙuntacacciyar rayuwar da ta taso daga cikinta ba.
Amma duk hakan bai wadace ba har sai da ta samu Ƙawar da ta zame mata komai na rayuwa, ta bata komai ɗin da tun kafin ta ce tana so.
'Shin ta ina zata fara? Me yasa Nabeeha ta mutu ta barta ba tare da ta ga canjin da ta yi ba? Me yasa ƙwaƙwalwarta bata taɓa yin tunani mai kyau a kan rayuwar Nabeeha ba? Me yasa bata kwatanta bata ko kaɗan ba ne daga cikin abubuwa masu kyau da ta mallaka a duniyarta ba? Inama ace zata iya dawo da hannun agogo baya, inama dai ace zata iya dawo da jiyansu zuwa yau ɗin su, to da ta zamewa Nabeeha fiye da yadda Aziza ta zamewa Nimrah a cikin rayuwar ƙawancensu. Da ta sadaukar da fiye da sadaukarwar da Azizaty ta yi ga Nimrah a cikin Alhubbu Dayyi'an. Da ta tsaya mata da kyakkyawar tsayawa na kokawa a kan rayuwarsu har kuma zuwa mallakar ababen birgewar da ke gareta. Sai dai ta kuskuro, kamar yadda ta makaro.'
Sabon kuka ta saki a hankali tana ɗora hannunta a kan yaran da take jin kamar su kaɗai ne suka rage mata a duniya, yaran da take ganin su ne za su zame mata tsanin da zata taka ta isa ga Nabeeha.
A hankali sautin kukanta ya ke tashi tana jin kanta na jujjuya mata, duhu na ƙoƙarin sake mamaye zuciyarta.
Kafin ta ankara ta ji sauƙar wani hannu mai taushi da laushi a kuncinta, hannun da ta ji sanyinsa har a tsakiyar zuciyarta, ya fara share mata hawayen da ke sauƙa a kan kuncin nata.
Da sauri ta kai kallonta ga inda hannun ya ke Aafiya ta gani tana goge mata hawayen kan fuskarta.
"Maama ba kyau kuka." Ta faɗa tana girgiza mata kanta.
"Momma ta ce Maama bata kuka, kullum-Kullum daliya kike. Me yasa kike kuka kuma? Ko kin daina Daliyar?" Yarinyar ta faɗa tana kwaɓe fuskarta kamar itama zata yi kukan.
YOU ARE READING
ƘAWATA CE
ActionLabari ne akan ƙawaye biyu masu halayya ɗaya! Labarin sadaukarwa a inda bata kamata ba! Ƙauna marar algus! Yarda marar iyaka! Aminci marar gudana! Tafiyar hawainiya da rikiɗewarta! Idan kun fara zaku so jin tafiyarsa. "Ita kaɗai ce ƙawar da na tas...