FITA 15

60 8 0
                                    

https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS

     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA GOMA SHA BIYAR

     Ba wai mamakin abin da, Nu'aiym ya mata take ba, a'a ta tsammaci jin fiye da haka daga gareshi, bata kuma tsammaci ganinsa a inda take ɗin ba.
    Kallon yanayin jikinta ta yi, tana ƙara kallon kan gadon da yanda ya hargitse ta yi, tana lumshe idanuwanta, Allah kaɗai ya san adadin ƙuncin da take ciki a yau ɗin.

     Tana zaunen taga curarriyar matar na tattare zanin gadon, tana kuma ganin lokacin da ta buɗe wata loka ta ɗauko wani farin zanin gado da ratsin purple a jikinsa ta sake shimfiɗawa a kan gadon.
   Sannan ta koma ta tattare kwanikan da ke gabanta, suma ta yi awun gaba da su.
   Bata jimaba ta dawo da moper da bokiti ta fara goge ɗakin "Madam, Na taimaka miki ki shiga toilet ne? Na kira Dakta Na'im yana nan zuwa." Ta mata maganar da harshen turanci.
   Kai ta girgiza mata, kana ta daddafa ta miƙe tsaye a kan ƙafafuwanta, tana bin bango, saboda jin wani azababben sarawar da kanta ya yi mata.
   Gefe guda kuma ga jirin da har a lokacin bai gama sakinta ba. Wata doguwar riga ta ɗauko mai launin purple da fararen fulawa a jikinta. Ta koma toilet ta ɗauraye jikinta sannan ta sa doguwar rigar. Lokacin da ta futo matar bata nan, hakan yasa ta zauna a kan gado tana maida numfashinta.
  Ko ba komai ta samun mutum guda da ta yi mata magana da girmamawa. Tana kuma tunanin adadin lokutan ƙuncin da zata sake ɗauka a tsawon rayuwar aurenta da Nu'aiym.

   Ƙwanƙwasa ƙofar da a ka yi yasa ta buɗe lumsassun idanuwanta, a hankali ta buɗe bakinta tana bada umarnin a shigo.
   Yanzun ma dai matar ce da har yanzu bata san sunanta ba "Dakta Na'im ya ƙaraso yana falo."
    Miƙewa ta yi, sai kuma jiri ya sake kayar da ita, haka kakkaurar matar ta ƙaraso cikin azama ta kamata suka fita, bata saketa ba sai da ta mata mazauni a kan kujerar da ke fuskantar Dakta Na'im ɗin.
  Baƙi ne sosai, yana da zagayayyen gashi a bakinsa, hancinsa gajere ne kamar inuwar magi, haka idanuwansa basu da girma, sai faffaɗan bakinsa da ya fi komai na halittun fuskarsa girma.
     "Barka da safiya, Mrs. Nu'aym." Ya faɗa yana kallonta da ƙananun idanuwansa.
   Sunan sai ya mata gingirim a kunnuwanta, tana jin rashin dacewarta da amsa sunan da ba shi da wani hurumi a gareta, kamar dai yanda take da tabbacin bata cancanta da kasancewa da sunan ba.
    "Me ke damunki?" Ya jefa mata tambayar da ta yi sanadin dawowarta cikin hayyacinta.
     "Ciwon ciki, sai kuma jiri haka?"
"Kwananki nawa rabonki da ki ci abinci?" Ya jefa mata maganar yana kallonta, kamar mai ƙirga kwanakin da ta shuɗe bata ci abincin ba.
    "Ba zan iya tunawa ba." Ta bashi amsa kai tsaye.
  Murmushi ya yi yana ɗan rubutu a kan wata takarda, daga bisani ya miƙe tsaye "Ki kula da kanki da lafiyarki. Shi ciki ba a masa shamaki da abincinsa, idan kika ce zaki horar da shi bisa wani abun da ba shi ya ƙaddara miki faruwarsa ba, ina mai tabbatar miki da zaki sha wahala sosai. Yanzu ki fara shan baƙin shayi daga bisani ki ci abinci kaɗan. ruwan shayin ya fi yawa a cikinki."
   Ya miƙe yana goya jakarsa a kafaɗarsa.
    "Zan je na siyo magani na kawo miki yanzu in sha Allah."
   Da ido ta bi shi har ya juya zai fice, sai kuma ya tsaya.
    "Mr. Ingoza!" Ya kira sunan da buɗaɗɗiyar muryarsa, wanda hakan yasa curarriyar matar ta fito da saurinta.
   "Ki bata baƙin shayi da abinci kaɗan ta ci."
     "Ok, Sir." Ta faɗa tana komawa kitchen ɗin shima ya fice a ɗakin gaba ɗaya.
   Mamakinta na fitowa waje da auna maganar baƙin likitan a ƙwaƙwalwarta, sam bata ga dacewarsa a zama likita ba, yana magana babu kulawa babu damuwa, kamar wani zazzafan Lakcara a jami'a. Sa'arsa ɗaya ya sameta a Faɗimatu ba lokacin da take amsa sunan Nabeela ba.
    Koma wa ya bashi aikin likitancin oho masa.
   "Madam, ga shi." Mr. Ingoza ta faɗa tana risinawa da miƙa mata kofin baƙin shayin.
    Bata son gwasale matar bakuma ta son ta ci gaba da kasancewa a yanda take, ta fahimci rayuwa na buƙatarta a raye, idan ta ce a haka zata hora kanta to tabbas zata wahala ne ba tare da ta mutu ba. Domin ta lura mutuwar na gujemata ne.
  Shayin ta kai bakinta duk da tsananin zafin da yake da shi, amma kuma sai ya taimakawa cikinta, tana jin yanda ya ke sauƙa yana sauƙaƙa ma wasu abubuwan da suka cure a wajen.
  A hankali ta ci gaba da sha har sai da ta shanye shi tas, sannan ta ɗan cakuli abincin da Mr. Ingoza ta gabatar mata. Bata sani ba ko daga bakinta ne, amma ko kaɗan bata jin ɗanɗanon daɗinsa a kan harshenta, ta dai ci shi ne kamar maɗaci, ta kuma ci ne dan ya taimaka mata ta tsaya da ƙafafuwanta.
    Ƙofar falon a ka ƙwanƙwasa, Mr. Ingoza ta je ta buɗe, Dakta Na'im ne, bai shigo ba, sai dai ya bawa Mr. Ingoza maganin da ke cikin baƙar ledar.
   "Akwai bayanan yanda za a sha su. Ki tsaya ki bata ta sha." Daga haka ya juya ya bar ɗakin.

      Kamar yadda ya buƙata, Mr. Ingoza ɗin ce dai da kanta ta tsaya ta bata maganin, sai da ta sha ta sannan ta bata waje.
  Zuwa lokacin ta ɗan ji wani zafi na sauƙowa tun daga samanta yana sauƙa ƙasanta. Shiru ta yi tana jingina a jikin kujerar falon, idanuwanta ja lumshe tana tunanin rayuwa da sauyin da ta kawo mata.

****

   Bayan mako biyu.

Zuwa lokacin jikinta ya wartsake ta kuma saba da Mr. Ingoza wanda ba koyaushe take zuwa gidan ba, idan ta zo kuma tana gama aiyukan da zata yi take tafiya.
   Har kuma lokacin bata ƙara haɗa idanu da Nu'aiym ba, bata sake ji daga gare shi ba. Duk da dai bata sa a rai ba dama, ta tsammaci ganin fiye da hakan daga gare shi.

     Tana jin shigarsa da fitarsa a motarsa da masu tsaron lafiyarsa, amma kuma bata taɓa kuskuren yarda hanya ta haɗasu tsakaninta da shi ba.
  Musamman idan ta tuna ranar ƙarshe da suka haɗu da shi da kuma mummunan kallon da ya mata a waccan ranar.
  "Kada ki ƙara kuskuren haɗa hanya da ni, koda a cikin mafarkin ki ne." Ya faɗa mata yana toshe hancinsa da kuma ɗage kansa.

   Ranar ta kalli kanta a Mudubi ya fi sau a ƙirga, ta kuma yi hawayen rashin sanin dalilin da ya sa yake toshe hancinsa idan ya ganta. Duk da a lokacin tana fama da ƙamshin turare ne.
    Miƙewa ta yi ta fito falon jin ƙaran ficewar motocinsa, dama sai ta ji fitarsa ne take fitowa ta ci abinci.
  Kamar koyaushe yauma abincinta na jere a daining ɗin, ta zauna ta ɗauki flat da zummar zuba abincin ta yi karo da farar takarda. Warware takardar ta yi, 'yar guntuwa ce bata da tsayi kamar yanda rubutun cikinta bai wuce layika uku ba.
 
   _'Abubuwan da suka zama tsanin zuwanki nan, suna ɗakina suna dakonki, ki ɗauka iya son ranki.'_

  _Nu'aiym_

Ta karanta saƙon ya fi sau a ƙirga, amma ta gagara fahimtar inda suka dosa, takardar ta shiga juyawa tana neman dalilin da yasa ta ke hannunta.
  Fasa cin abincin ta yi, ta miƙe ta fara tattaka benin, wannan shine karo na farko da ta takala matakalan benin tun zuwanta gidan.
  Zuciyarta ba daɗi sam, kamar yanda gaɓɓan jikinta basa jin daɗin, gabanta banda luguden faɗuwa ba abin da yake.
Ɗakin farko ta tura, sai bata ga komai ba, sai kayan wasan yara hakan yasa ta rufe ɗakin ta buɗe na kusa da shi, anan ta yi tozali da wani katafaren palo na alfarma da ya sha kayan alatu, komai da ke falon ja ne da ratsin baƙi a jikinsa, hakan yasa ta shiga ɗakin ta zama 'yar asalin ƙauye wajen kalle-kalle, a haka ta raina girman wajen, sai gashi akwai komai na mamakin da bata yi tsammaninsa ba, akwai ƙofofi guda uku a jere ta tsakiyar ta ƙurawa ido, kafin zuciyarta ta bata umarnin shiga.
  Kai tsaye ta nufi ɗakin ta tura, sassanyan turarensa ya mata maraba da shigowa, kafin ta zura ƙofarta, shi kuma saɓanin falon komai na cikinsa fari ne ƙal.
  Idonta ya mata tozali da faffaɗan gadon ɗakin wanda yake cike gam da kuɗi, daga kan 'yan dubu-dubu sai kuma daloli da suke zuzzube a ɗakin.
  Ƙarasawa ta yi tana dube-dube sai ta hango wata guntuwar takarda, ɗauka ta yi da sauri, ta warwareta.

    _'Idan basu wadace ki ba, akwai wasu a loka.'_

   Bata san yaushe ne hawaye ya gangaro a kwarmin idanuwanta ba. Sai dai ta yi nasarar sa hannunta ɗaya fa rufe bakinta, ɗaya hannun kuma tana dafe da ƙirjinta. Tana jin yanda zuciyarta ke barazanar son cirewa daga maliƙarta.
  Bata dai yi ƙasa a gwuiwa ba, ta buɗe lokar da take cike gam da kuɗaɗe, sai wata farar takarda da take reto a wajen.
    _'Arziƙi gadarsa muka yi, muna da tulinsa, kamar yanda muka yi nutso a cikinsa tun fil'azal. Shi yasa ba mu rabu da mutuntakarmu ba.'_
    Kanta ta buga a jikin lokar da ƙarfi tana fashewa da kuka, kafin ta juya a guje ta bar ɗakin......

🌷🌹🌷🌹🌷

Ƙawata ce! Paid book ne a kan N300 kacal, akwai free pages da za su biyo baya a gaba.
  Ga masu buƙatarsa za su iya turo kuɗin ta wannan accnt 👉3051894647 Hajara Ahmad Hussain polaris Bank. Su tura katin shedar biyansu ta wannan lambar 08030990232 ko +234 703 513 3148 Ga wadda basu da accnt kuma za su iya turo katin waya na mtn ta waɗannan lambobin.
  Ga 'yan Niger kuma za ku iya tura tura carte moov ta 400 zuwa ga number  +227 84 50 64 76

#KWTC
#NWA
#CMNTS, LIKE SHARE,
#GIRMAMAWA
#DABANNE.

  Oum-Nass

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now