FITA TA ƊAYA

159 14 1
                                    

ƘAWATA CE!

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS
  
     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH S W. A MAI KOWA MAI KOMAI, INA FATAN ALLAH YA SANYA ALKHAIRAI ACIKIN ABABAN DA SUKA HAƊA MU.
   Wannan karon ma gani na dawo muku da wani sabon labari wanda ya sha ban-ban da labaran da na saba kawo muku.
   Wata ƙila salon da ke cikinsa yayi dace da wani abu na sashen rayuwar ku, wata ƙila kuma ababen cikinsa ya baku takaici da kuma ban haushi.
  Lallai duk abin da kuka ga a cikin labarin Arashi ne da kuma kwaikwayo na rayuwar da ke faruwa.
 
    GIRMAMAWA

FITA TA ƊAYA

  ABUJA, NIGERIA.

  A hankali ta ke fito da wasu takaddu tana duba su, sannan ta mayar da kallonta ga mutane biyun da suke tsaye a kanta, mace da namiji.
  Murmushi ta yi tana lumshe idanuwanta da kuma ciza bakinta, hakan ke nuna tana cikin tsananin ciwo ne.
   "Ko zaka taimaka min da takardun can a loka Nu'aym?" Bai jira ta ƙarasa ba ya buɗe durowar ya futo da wasu takardu a cikin ambulan ɗinsu ya miƙa mota.
  Fuskarsa akwai damuwa sosai, kamar yanda itama ɗayar ta ta fuskar take cike da damuwa.
    Karɓa ta yi sannan ta ɗauki biro ta sa hannu a jikinsu.
   Da hannu ta yima ɗaya macen alama akan ta matso, matsowa ta tayi sannan ta miƙa mata da nuna mata jikin takardun "Kisa hannu anan."

Kallonta ta yi sai ta tsinci kanta da kasa sa hannun, idanuwanta sun cika da hawaye taf, kafin ta yi magana hawayen sun samu damar gangaro akan kyakkyawar fuskarta.
   "Me yasa zaki yi haka? Kin bani komi na rayuwarki Nabeeha! Ban taɓa kallon abu da sigar sha'awa ko birgewa ba ya kuskure min, muddum ya kasance naki ne! Sai dai wannan ban taɓa masa kallon sha'awar ba, ban taɓa jin cewar zan same shi! ba nawa ba ne Nabeeha! Baya cikin ababen da zaki iya sadaukar min da su. Wannan naki ne! Gwagwarmayar da kika sha, da faɗi-tashi dan ki same shi ne! Ya yi girma a tare da ni ace kin sadaukar min da shi.
  Ba zan iya amsar wannan ba Nabeeha! Bani da ƙwarewa da gogayya akan mallakarsa." Hawayen da ke kan fuskarta ya ci ƙarfinta, maganarta ta sarƙe sosai.
   Murmushi Nabeeha ta yi, tana lumshe idanuwanta da kuma ciza bakinta, wanda ke nuna tsananin ciwon da ta ke ji a jikinta.
    "Wannan ma naki ne Nabeela! Ban taɓa ganin abin da na mallaka a matsayin nawa ba face na mu, ni da ke. Ko wata rana ina yin aiki da tsammanin jira daga gare ki, ko zaki zo gare ni dan ki amshi wannan aikin!"
  Murmushi ta yi wanda da ganinsa na na ciwo ne da takaici, tana ƙara yamutsa fuskarta "Ko wata rana idan naga an kira wayana, ko nayi baƙuwa sai na tsammaci ke ce kika zo dan ki nuna ƙaunar nasarar da muka samu. Amma hakan ya gagara, ban ganki ba ban kuma ji daga gareki ba, duk inda ya kamata ace na samu labarinki sai ace bakya nan.
  Lallai rayuwar duniya 'yar ƙarama ce Nabeela, kamar yanda mutanen cikinta suke ƙananu da kuma manyan burika a cikinta. Burikan da ba su fiya  cika ba har sai lokaci ya ƙure musu, waɗan da suke samun cikar burin nasu kuma basu da yawa a duniya, kaɗan ne masu nasara da samun damar cika shi.
  Ni bana farin ciki akan ɗaukakar da na so ace ke ce a kanta!  Bana jin daɗin duniyar da na samu kaina a cikinta a yayin da ƘAWATA ta yi nesa da ni! Duk inda na juya ina ganin dubbanin mutanen da suke girmama ni da kuma nuna soyayyarsu a kaina, sai dai ni banji cewar su ɗin masoya na ba ne. Ina jin kawai suna bin ɗaukakar da take tare da ni ne! A yayin da ƙawar da muka taso ciki ɗaya ta guje ni saboda ɗaukakar."
  Hawaye ne ya gangaro akan fuskarta, hawayen da take jin raɗaɗi da zugin sa na taso mata tun daga ƙasan zuciyarta, zafinsa na kwanciya akan kyakkyawan kuncinta.
 
   Ita kanta Nabeela kuka ne ya ci ƙarfinta, kukan da ta manta yaushe rabonta da ta yi irinsa? Kukan da ta kasa bari ya sauƙar da hawayenta har sai da sautinsa ya futo ya ke amsa amo a jikin ɗakin.
   Shi kansa matashin Saurayin da yake tsaye kasa jurewa ya yi saida hawaye ya sauƙa akan fuskarsa, yana kuma rufe bakinsa da tafukan hannayensa.
   Ba zai iya tuna adadin lokacin da take ambatar sunan Nabeela ba a rayuwarta. Kamar yanda ba zai iya tuna lokutan da ya hanata magana akanta ba. Bai san cewa ƙaunar da take mata ta kai haka ba, kamar yanda bai taɓa tunanin tana gwagwarmaya a cikin dubbanin mutanen da suke da ikon faɗa a ji ba ne saboda ƘAWARTA kawai!
  Idonsa ya lumshe wasu hawayen suna sauƙa akan kyakkyawar fuskarsa. Yana jin inama zai iya dawo da jiya yau! Inama zai iya juya hannun agogo ya koma ba ya, da babu abin da zai hana shi cika ko wani buri na ta. Da bai dage akan ƙara nesanta su da junansu ba, da ya barta ta ci gaba da kula da Nabeela, da kuma bata duk abin da take da iko a kansa. Sai dai babu dama, wannan damar an barta, kamar yanda aka bar kari tun ran tubani.

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now