https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
ƘAWATA CE! 💕
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
©OUM-NASS
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
FITA TA TARA
"Dady dan Allah ku yi haƙuri ku raba auren nan, idan na je gidan Nu'aym na ci amanar Nabeeha. Idan kuka kaini gidan nima mutuwa zan yi, dan Allah Dady kar ku kai ni." Ta ƙarasa maganar tana ƙara rushewa da sabon kukan baƙin ciki.
"Da can da kika ce kina son sa baki yi tunanin cin amanar ba sai a yanzu a bayan babu ranta? Ko kuwa dai lokacin da kike neman hanyar ganinsa da raba tsakaninsa da Nabeeha ba ki yi tunanin mutuwar ba sai a yanzu?"
A razane ta ɗago da kanta sama ganin Baba Adamu zaune ya hakimce a kan kujera, mutumin da suke mutuƙar tsoro da shakkarsa a danginsu, mutumin da yake da zafin rai da ruƙo a kan duk wani abu da ka aikata masa.
Toma ya akayi bata san da wanzuwarsa a wajen ba? Bata ji alamun yana wajen ba.
Dady ne ya girgiza kansa "A'a Yaya wannan maganar babu ita a wannan muhallin. Dan Allah a yi haƙuri a daina tuna baya, bayan da ta kasance marar kyau wadda take ɗauke da ƙuruciya a tare da ita.""Baya kam dole a tunata Nameer! Dole tarihin sheɗancin Nabeela ba zai taɓa goguwa da sauyawa ba. Ka bar ganinta a haka tana kuka, ba abar tausayi ba ce, sam ni banga ta inda ta cancanta da sadaukarwar da Nabeeha ta mata ba.
Wallahi da ace ina nan a ka ƙulla auren can da babu yadda za a yi a ɗaura shi, koda ace Nabeeha zata mun fatalwa ne na ƙin cika mata alƙawarinta. Da kuma ace ina nan a lokacin da ta ke ta ƙulla-ƙullan barwa Nabeela komai nata da na tsaya a gabansu na yayyaga musu takardun sharaɗin da suka cika."
Ya ƙarasa maganar yana ƙwafa sannan ya mayar da kallonsa ga Nabeela da a yanzu sautin kukan nata ya ragu sai ajiyar zuciya take. A yayin da sautin maganarsa ke zame mata kamar tafasasshen ruwa ake watsa mata a sassan jikinta.
"Ta shi ki bamu waje, algungumar munafukai. Kuma ki tattara duk wani abu da kika san naki ne a waje ɗaya. Gobe da yardar Allah zaku tattara ku tafi, idan ya so idan kin so ki yayyanka Nu'aym ɗin ki sa shi a tukunya ki raɓaɓɓaka shi sai ki cinye. Ƙarshen soyayya kenan."
A zabure ta miƙe ta yi hanyar waje tana jin ƙafafuwanta kamar basa tafiyar da ya kamata a ce suna yi.
"Dubeta da ƙafafuwa kamar na zabuwa." Baba Adamu ya sake faɗa yana ƙwafa."Yaya ban so ka mata a haka ba, a yanzu Nabeela abin tausayi ce, duk abin da ta aikata a baya ta yi shi ne cikin ƙuruciya. Mutuwar Nabeeha ta girgiza rayuwarta. Dan Allah yaya kar ku bi da ita da zafi, ku bar mu za mu iya komai da ya danganci rayuwarta."
"Da wannan kyakkyawar zuciyar ta ku kuka ɓata Nabeela, kuka ɗorar da ita a kan abin da ba nata ba, har ta manta mafarin da ta taso a cikinsa, Nameer. Na fika sanin wacece Nabeela saboda na zauna da ita tun a tsumman goyonta, ba zan ce baka santa ba, saboda fuskokin da take da su masu yawan gaske ne.
Wataƙila ta shimfiɗa mafi kyau a cikin baƙar fuskar da take shimfiɗa mana.
Kai uba ne na gari, da kake bawa yaranka dama a kan duk wani abu da suke so, saɓanin ni na da na zama barkono a cikin dangi."
Miƙewa ya yi tsaye yana kai kallonsa ga Abba yana ƙara doka masa harara "Kai, Aminu ta shi mu tafi." Ya yi maganar da ɗan faɗa-faɗa.
Hakan yasa Abba ya miƙe yana miƙawa Dady hannu "Mun gode sosai da kyautatawa, sai goben idan Allah ya amince mana."
Kai Dady ya jinjina yana ƙara jijjiga hannensu da suke sarƙe da juna. Wani lokacin yakan yi mamaki a bisa sanyin halin Abban Nabeela, yakan kuma girmama ƙarfin iko da buwaya na Ubangiji, da ya sanya Baba Adamu a matsayin yayansa da suka fito ciki ɗaya, kamar dai yadda yake mamakin banbancin ɗabi'ar Nabeela da tasa da ya kasance uba a gareta.
"Na gode, Amin." Ya faɗa yana sakin hannunsa, saboda baya taɓa kiran sunansa Aminu sai dai ya ce masa Amin.
Baba Adamun ma hannu ya miƙa masa baya Dady ya miƙe tsaye da zummar yi musu rakiya.
"Ka yi haƙuri fa Nameer, ba ina ganin gazawarka ba ne a kan abin da ya faru da Nabeela ba ne a yau. A'a ina ganin rashin cancantar ta ne na samun miji kamar Nu'aym, duk da abubuwan da ta aikata a baya."
YOU ARE READING
ƘAWATA CE
ActionLabari ne akan ƙawaye biyu masu halayya ɗaya! Labarin sadaukarwa a inda bata kamata ba! Ƙauna marar algus! Yarda marar iyaka! Aminci marar gudana! Tafiyar hawainiya da rikiɗewarta! Idan kun fara zaku so jin tafiyarsa. "Ita kaɗai ce ƙawar da na tas...