FITA TA 20

130 10 3
                                    

https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS

_Assalama alaikum, barkanmu da kasancewa da ku, ina bada haƙurin rashin jina kwana biyu, hakan ya faru sakamakon wasu 'yan matsaloli da suka gifta. Da kuma ƙarancin rashin wutar da muke fama da ita, amma in sha Allah daga yau za a ninka post._

     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA ASHIRIN

   Shiru ta yi kamar mai nazarin su, kafin ta yi magana Yusuf Ali ya miƙo mata wani abu da aka nannaɗe da leda mai ƙyalƙyali.
   "Ga wannan madam, kayan aikin ki ne." Ya faɗa cikin harshen turanci wanda ya zame musu kamar ruwan iskar shaƙarsu, saboda yanda suka ƙare wajen yinsa.
   Karɓa ta yi ya risina cikin girmamawa "Muna jiranki a waje idan kin shirya, Madam."
  Daga haka ya mayar da kallonsa ga Merry Joseph ya ce "Mu je ko?" Risinawa ta yi ta yiwa Nabeela jinjina sannan ta bi bayansa suka tafi.

    Nabeela ta bi bayansu da kallo har zuwa lokacin da ƙofar palon nasu ta rufe ruff. Ta mayar da kallonta ga kayan da ke riƙe a hannunta, da ƙyar dai ta cira ƙafafuwanta ta juya zuwa ɗaki, ta zauna a bakin gado ta fara warware ledar da ta zagaye kwalin, daga nan ta buɗe ta ga kaya a jiki irin dai na ma'aikatan banki, farar riga 'yar ciki da kuma jacket ruwan toka da maratayin wuya sai siket itama ruwan toka, da kuma wani madaidaicin hijab fari.
   Sai wani kayan shima same wannan amma shi baƙi ne ba ash colour ba.
Idanuwanta ta lumshe tana jin wani abu na sauƙa a ƙirjinta har zuwa ƙafafuwanta, wani abun da ba tasan ya zata kwatanta shi a ranta b, saboda bai yi kama da farin ciki ba, kamar yanda bai haka hanya da ƙunci ba.
   Toilet ta faɗa ta yi wanka ta fito ta shirya, a cikin kayan aikin Ash colour ɗin, fuskarta fayau babu ko kwalli a idanuwanta, lokacin da ta ɗauki rigar saman I.D card nata ya faɗo, ta tsugunna ta ɗauka hoton da ke jiki ita ce, amma ta manta lokacin da aka ɗauki hoton, ita ce tana murmushi fuskarta kamar tana ganin wani abu, wani abu a wani shuɗaɗɗen lokaci. *FATIMA AMINU MU'AZU* Idanuwanta ya sauƙa a kan cikekken sunanta, sunan da yake liƙe a jikin kowata takardar shedar karatunta, sai kuma signuter nata da bata san shima a ina a ka same shi ba.
   Amma tananda tabbacin Nabeeha ta gama sanin komai da ya shafi rayuwarta, idan ta ce komai tana nufin komai ɗin da ita a karan kanta bata san shi ba.
    Ƙaran ƙararrawar palon ya ankarar da ita lokacin data ɗauka a shirin, hakan yasa ta zura fararen takalmanta ƙirar toms, da wata farar madaidaiciyar jakarta da ta rataya a kafaɗarta, tana daidaita zaman farin hijabinta a jikinta da kuma gilashin idanuwanta da suka zama farare suka ƙara ƙawata manyan idanuwanta masu haske, da damuwa ta ɗan fara mayar da su zuwa ƙananu matsakaita. Ta ɗauki wayarta ta riqe a cikin ruqonta, zuciyarta cike da wani fata, tana buƙatar ace ta sanar da wani nata wannan abun, amma kuma a yanzu bata da wanin da zata kira dan ta bashi labarin rayuwarta, Nabeeha kaɗai ke katse komai nata ta saurareta, ita ce take dakatar da duk wasu al'amuranta dan ta ji meke tafe da ita. Zata iya cewa tun kafin ta yi magana ma take karanto damuwarta.
  Amma yanzu babu ita, dangin da suke kewaye da duniyarta da abaya take ganin sun amsa sunan cunkus ɗakin tsumma suma sun yi nesa da ita, mijin da ta so tsarawa rayuwarta komai da shi a wani bagidajen tunaninta ya zama maƙiyi a gareta, maƙiyin da bai ƙi a bashi wuƙa ya sassara mata ba, inda za a ce kisa halak ne.
   Hawaye ya taru a idanuwanta ta yi saurin gogewa da tushi ta daidaita zaman gilashin idonta, a hankali ta ɗauki turare mai rangwamen ƙamshi ta sa a jikinta, ta fito, tana jinta fayau, tana jin kamar iska zata iya cicciɓeta ta kada ita ƙasa.
    Ta tuna ko a daren jiya ta so yiwa Nu'aiym magana a kan aikinta, ba so ba ma ta yi, ta kwatanta yi masa magana duk da a baya ta faɗa masa ya bata amsa mai zafi.
   Sai dai a daren jiyan ya bata amsar da ta ƙara karya mata wasu tsammanin nata a kansa ta kuma ƙara ture al'amuransa ta ajiye su a gefe.
    _"Burin Nabeeha ne wannan, ina girmama komai da take so, idan aka ɗauke ke da kika xama baƙar sa'a a gareta, da kuma zame mata kaska wanda har sai da kika tsotse mata jininta saboda kambun maitar da kika daɗe da amsa. Ki yi duk abin kike son yi, ki kuma tara kuɗaɗen da zai kankarewa danginku tambarin talauci har ƙarshen rayuwa. Amma ki guji haɗa hanyarki da tawa."_
  Maganar da ya faɗa mata da ta kwana tana juyi da juyata, ta kuma kasa gogeta a kwanyar kanta, har kuma a yanxun da take tafiya a kan ƙafafuwanta dan ta isa ga aikin.
  Ta so ƙwarai ta haƙura da aikin kodan ta nunawa Nu'aiym aikin ba shi zai cire mata talauci ba balle danginta, duk ta daɗe da kuskurewa da kuma barin dama, idan ta yi la'akari da ita ce da hannunta ta siyawa iyayenta kowanne tozarci da kuma cin mutuncin da take gani a wajensa.
   Iyayenta babu ruwansu da rayuwarta asalima sun sha kai ruwa rana a kan alƙiblar da ta daidaita ganinta da kuma son isa gareta.
Inama zata iya dawo da jiya yau, inama zata iya sauya akalar ƙaddara, da ta taro jiya ta koma yau, da ta goge kowanne baƙin fantin son duniyar data lilliɓawa kanta.
   Amma kuma a duk waɗannan ƙalubalen rayuwar da take fuskanta tana hango idanuwan Nabeeha a kanta, tana hango lokacin da take roƙonta akan ta sa hannu a takardu, ta kuma yi mata alƙawari, fatan Nabeeha na ƙarshe da kuma burinta, wanda yanzu yake gaf da kashe mata rayuwarta, yake tsoratar da ita daga rayuwar duniyar.
   Wani abu mai ƙarfin gaske ya gifta a idanuwanta ɗauke da hoton Nabeehan "_Za ki iya komai n sani, za ki iya fiye da abun da kowa yake so."_ Sautin muryar Nabeeha ta dir a kunnuwanta da kuma ƙarfafa mata gwuiwarta a kan yin aikinta.
   _"Ina tare da ke. Ki kirani a lokacin da kike son ganina, zan zo gareki kafin tunaninki ya yanke."_
  Ta buɗe baki zata yi magana kafin ta ce wani abu ƙaran ƙararrawar falon ta sake kaɗawa, ta kai idanuwanta da dawo da su inda take ganin Nabeeha taga wayam babu ita, babu dalilin wanzuwarta.
  Zuciyarta sai ta kaɗa da ƙarfi, cike da shakku da tsoron a kan anya bata haukace ba? Domin idan ba hauka ba ta ya zata ga Nabeeha har kuma ta mata magana tana mata alƙawarin yi mata komai?
   Kai ta girgiza tana aro dauriyarta da ta mata saura ta fice a ɗakinta, ta buɗe ƙofar.
  Yusuf Ali ta gani da Merry Joseph suka bayyana.
"Barka da fitowa Ma'am" Suka faɗa cikin haɗin baki, yayin da Merry ta miƙa hannu da son riƙe mata jakarta, ta girgiza mata kai.
  "Basshi, Na gode." Ta faɗa da sanyin murya.
  Yusuf Ali ya shige gaba, yayin da Merry ke take mata baya, tana mata baya, idanuwanta ya mata tozali da wata mota baƙa sabuwa dal sai sheƙi take.
  Tana ganin lokacin da Yusuf Ali ya buɗe murfin baya yana risina mata, da Bissmillah ɗauke a bakinta ta shiga motar, sanyi masuburbuɗar sanyaya motar ya mata maraba haɗe da ƙamshin Air freshner dake ciki, ta jingina da kanta baya ta lumshe idanuwanta.
  Tunaninta na wurgata wata duniyar tunanin, a shekarun baya da take bin duk motar da ta gani da gudu tana shafa bayanta.
  A wancan lokacin gani take idan ta shafa motar to kamar ta dangwalo arziƙi ne, wata rana zata iya shafo nata.
   Ƙaran da wayarta ta yi da shigowar saƙo yasa ta buɗe idanuwanta ta kalli wayar daƙon kamfanin layin MTN ne da suka shahara wajen yinsa a kowata rana ba tare da sun manta ba.
   Lokacin da motarsu ta isa ga tamfatsasttsen bankin na CBN idanuwanta suka so raina fata, ta raina burinta da kuma ƙaryata kanta na son taka wasu matsayi na rayuwa da take kan yinsu a baya, a lokacin da idanuwanta suka sauƙa a kan manyan  mutanen da suke jujjuya bankin, manyan mutanen da a jaridu da gidan TV kaɗai take iya ganinsu, sai gashi yau sune tsaye suna dakon jiranta, sai taji jikinta ya ɗauki rawa ƙafafuwanta sun fara kaɗawa kamar iskar bazara na sauƙa a jikinta ne kaɗai.
   Har zuwa lokacin da motarsu ta daidaita tsayuwa, Yusuf Ali ya buɗe mata murfin motar, mutanen da 'yan jaridu suka yo caa a kanta suna fara ɗaukan takunta da kuma isarta.
   Ta rufe ido ta fara karanta addu'ar da duk ta zo bakinta, tana neman nutsuwarta da taimakon Ubangiji a kan ya iya mata.
   Sai dai ta gagara fitowa har sai da taji an ruƙo hannunta gam an jata, wanda hakan yasa ta buɗe idanuwanta da ƙarfi domin ganin wake da wannan ƙarfi, idanuwanta kaɗai ta gani da kuma sauƙar murmushi a kan laɓɓanta.
    _"Na ce ki kirani zan zo ai."_
"Nabeeha!!" Ta faɗa da tsanani mamaki, sai dai bata sake magana ba, har sai da ta dirar da ita a tsakiyar mutanen da suke mata marabanda zuwa.
   Ta shiga ƙaƙalo murmushi da haɗiye yawu mai kauri a maƙoshinta, suna miƙa mata furen maraba yayin da take mayar da shi ga Merry idanuwanta na kallon inda Nabeeha da ke kusa da ita, kusa mafi kusanci sosai wanda take jin kamar kafaɗunsu na gugar na juna ne.
   Tana tunanin kodai Nabeeha na raye? Ko kuma dai wani abu ne ke faruwa da kanta?
    "Wani farin ciki kike ji a yanxu da kika tsinkayi kanki a wannan matsayin?" Tambayar wani ɗan jarida ta sauƙa a kunnenta, ta kalli yanda camera's suke ta walƙiya a kanta da kuma idanuwan mutane.
   So take ta ce bata farin ciki, domin ko ga fuskarta idan an laluma an san babu shi sam, amma sai ta ji bakinta ya taɗe murmushi na kuskure mata, wanda ya xo ne a lokacin da idanuwanta ke mata gizon ganin Nabeeha na mata murmushi, ta yi ƙoƙarin mayar mata da martani tana buɗa bakinta a hankali da faɗin.
   "Alhamdulillah ala kullu halin." Maganar da ta zo a kan gaɓa da kuma karɓuwa ga 'yan jarida, kafin kuma ya sake magana Governor na CBN ya tare su.
   "Mu je ki ga office ɗinki." Ya faɗa da harshen turanci suka bi bayanta ɗuu da sauran ma'aikatan wajen idonta sai dai tuni an dakatar da 'yan jaridun su kuma suka nufi can ƙololuwar da taimakawar na'urar dake cicciɓar mutum da hutar da shi daga taka matakalan beni.
   Wani ƙaton office dake ɗauke da wata haɗaɗɗiyar office suka shiga, a kan teburin akwai wani ɗan madaidaicin abun liƙa sunan da aka yiwa sunanta wani tambari kamar da ruwan zinare.
   *Fatima Aminu Mu'azu*
   _Director of currency operations_
Ta ƙwalalo ido tana kallon matsayin da ta taka wanda mafarkinta da son duniyarta bai taɓa kawo mata shi ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 13, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now