https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
ƘAWATA CE! 💕
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
©OUM-NASS
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
*Assalama alaikum.*
*_Alhamdulillah! Dukkan godiya ta tabbata ga Allah s.w.a wanda ya sake ƙara aranta mana rai da rayuwa da kuma lafiyar, kasancewa tare a yau. Ina miƙawa dukkanin ɗaukacin Al'ummar Musulmi barka da sallah! Ga masu bibiyar rubutuna da tsammanin jiran ji daga gareni ina miƙa tulin jinjina da yabo, da Girmamawa da kuma fatan alkhairi mai yawa. Ina fatan Allah ya amshi ibadunmu da muka yi a watan da ya gabata, ya kuma nuna mana wani lokacin idan muna raye, na gode sosai da jimirin bibiyar rubutuna._*
*GIRMAMAWA*FITA TA GOMA SHA BAKWAI
Ganin komai take yi kamar a mafarki ne, har a wannan lokacin da ma'aikatan bankin CBN suka zo gareta da kuma abin da ya faru a tsakaninsu, tana fatan ace ba gaske ba ne. Ba kuma zahiri ba ne. Sai dai idan ta haɗa da gushewar Nabeeha a cikin duniyar nan zata iya fahimtar rayuwa a matsayin aba marar adalci, kuskuren da ya zama ɗabi'a na Ɗan Adamtaka, shine barin dama ta kuskure ma, da kuma gaza ganin muhimmancin abin dake tsakanin ruƙonka har sai ya kuskure ma.
A yanzu da take rayuwa a muhallin da a baya ya amsa mallakin na Nabeeha, da kuma aikin da ke ta mata farmakin maye gurbinta, ya taru ya ƙara kassara zuciyarta da kuma tsinke duk wata walwalar da ke cikin rayuwarta.
Idan da a shekaru biyar ɗin da suka wuce a baya zana sanar da ita cewar zata faɗa hali irin wannan, to zata ƙaryata mai faɗar, idan ta kama zata iya tsinka mishi kyawawan marukan adawa da baƙin ciki.
Idonta ta buɗe a lokacin da ta ji wata ƙara mai ƙarfi na shirin ɓalle mata kunnuwanta, sai dai ga mamakinta ba bu wani abu da ke tasirantuwa da sautin amon da zai firgitata irin hakan.
Tsaye ta miƙe tsam a kan ƙafafuwanta tana gyara zaman farin gilashin dake saƙale a cikin idanuwanta.
Ta fara ajiye takunta mai sanyi da ya sanyaya fiye da lokacin ganiyar zamaninta, ta shige can ƙuryar ɗaki ta buɗe wata loka ta fito da wata baƙar jaka madaidaiciya. A bakin gado ta zauna ta zugeta ta fara zaro wayoyinta wanda kana musu kallo ɗaya xaka san sun lashe kuɗaɗe, wayoyin da abaya take ganin ba zata iya sa'a guda ba tare da sun kasance a cikin ruƙonta ba, sai gashi yanzu ta gagara fahimtar amfaninsu da kuma dalilan da yasa suka kasance a gareta.
Na'ura mai ƙwalƙwalwa ta zaro a cikin jakar wanda bayanta kuma akwai wasu takardu bila adadin, sai dai a yanzu ba sune burinta ba, a yanzu tana so ta cika alƙawarin data ɗaukarwa waɗancan mutanen, na zata aika musu da saƙo.
Kunnata ta yi ta shiga bincike a cikin email ɗin da saƙonni suka fara tururuwar zuwa, sai dai babu wani dake da alaƙa da waɗanda take tsammani, sai kuma wata ƙwalƙwalwarta mai amfani ta ankarar da ita cewar Nabeeha bata santa da wannan Email ɗin ba.
Ta tuna bayan rabuwarta da Nabeeha ta sauya komai da Nabeehan ta santa da shi, daga kan layukan waya zuwa account nata na social media, hatta email saida ta sauya wani.
Gilashin idonta ta ƙara gyarawa a kan fuskarta, bayan ta haɗiyi wani yawu mai kauri da ɗacin da ya tsaye mata a ƙirjinta, wanda takaicin kanta da kuma jin haushin Butulcin da ta yi a rayuwarta ya taru ya ƙara datse mata duk wata walwalarta.
Da sauri ta saka tsohon email ɗin nata nan take sai ga saƙonni sun fara tseren shigowa, saƙonni Nabeeha wanda babu adadi, saƙonnin da suke tsere da rige-rigen faɗawa cikin akwatinta, wanda suka haddasa mata bugawar ƙirjinta da ƙarfi.
Hannunta ya fara karkarwa da kuma ɗokantuwa da son ganin me ke saƙale a jikin saƙon Nabeeha?_Junuary 15th, 2016 'Wai ina kika shiga? Na kiraki har ba adadi, na je gida fiye da tsammani. Na kira Baba, na yi magana da Ammu. Amma babu ke.'_
Saƙon farko da ta buɗe kenan, wanda yasa ta furzar da iska mai zafi a maƙoshinta, ta sake buɗe wani saƙon.
_10 April, 2016 'Ina da damuwa sosai. Ina son na yi magana da ke ko sau ɗaya ce, dan Allah.'_ 😓
Ƙarshen saƙon ta haɗa mata da fuskar damuwa, wanda yasa Nabeela lumshe idanuwanta, ɗacin dake maƙoshinta ya ƙara dira a kunnenta. Wata damuwa Nabeeha zata shiga a shekarar farko ta aurenta? Tambayar da ta yiwa kanta tana jin kamar ta kashe kanta dan takaicin kanta da take ji.
Bata taɓa tunanin mutum zai iya adawa da kansa ba, bata taɓa tunanin mutum zai rayu da jin haushin kansa ba, kwatankwacin yanda take jin haushin kanta a yanzu._13 April, 2016. 'Ba ni da lafiya. Rashin lafiyata bai bani damuwa ba, kamar yanda rashinki ya ba ni. Ina jin rayuwata ta zo ƙarshe, Ina ƙoƙarin yaƙar ƙuncina, ina dariya idan na tuna ina yin abin da kike muradi. Dan Allah Nabeela, ko sau ɗaya ne ki kirani.'_
Ta karanta saƙon yafi a ƙirga, ta ja numfashi ta ja fasali, daga farkon rubutun ya tsoratata ƙwarai, daga ƙarshensa ya tsuma zuciyarta. Nabeeha na roƙonta ta kirata ko sau ɗaya ne a rayuwarta. Da ta ɗauka da tayi gaba zata manta baya, ashe ita bata san me ake nufi da manta bayan ba, ashe ta cika zuciyarta da ƙaunarta, bata taɓa mantawa da ita ba._17 April, 2016 'Likita yace min kin kusa zama Momma. Ina da cikin twins, za ki zo kafin na haihu, ko?'_ 😣
Jingina ta yi da jikin gadon tana shafa kanta da kuma sosa girarta guda ɗaya, daga idanuwanta tana hasashen yanayin Nabeeha a lokacin da take mata saƙon, tana jin zuciyarta na buɗewa da ƙaunar son ganinta a zahiri, sai dai ta makaro, ta kuskuro domin ta riga data mata nisa, nisa na har abada.
Daga nan sai saƙonnin suka yanke ta shiga neman su, saboda kowatarana akwai saƙon barka da safiyar da ta ajiye mata, akwai kuma na mukwana lafiya. Amma daga inda ta ce mata tana da juna biyu sai saƙonnin suka yanke.
Can sai gashi kamar an hankaɗo su suka fara shigowa a hankali.
_3th July, 2016. 'Da sanina naƙi turo miki saƙo, naga ko zaki damu da rashin jina 😊, Lolx. Na san fuskarki ta nuna damuwa, ina lafiya ni da babys, sai dai nasan tawa ta ɗan lokaci ce, za su rayu da ke har ƙarshen rayuwa.'_Da fari ta fara murmushi amma a ƙarshe sai hawaye ta tsumu a cikin idanuwanta, ba kawai tsokana ce ta turo mata ba, ba kawai maganar da zata faɗa mata ba ce, ta ɓoye mata tana da rashin lafiya, kamar yanda ta ambaci lafiyarta ta ɗan lokaci ce.
Rufe Computer ta yi ta fara kuka mai sauti, ga saƙonni Nabeeha jingim amma babu damar amsa mata, ga abin faɗa da yawa a ƙirjinta amma babu wanda za a yiwa maganar.
Ashe kuskurenmu kan iya caccakar rayuwar mu har ƙarshen rayuwa?
Dole akwai wani abu, akwai abin da ya kamata ace an faɗe shi.Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta da aka yi yasa ta yin saurin share hawayen fuskarta, ta gyara zaman gilashinta a cikin idanuwanta.
Ta miƙe ta buɗe ƙofar ta yi tozari da Mrs. Ngozi a jikin ƙofar da ƙwaton farantin dake ɗauke da kayan marmari.
"Madame barka da hutawa. Likita yace kada ana barinki babu abin motsa baki, waɗannan za su taimaka miki wajen ƙara ƙarfin jiki."Kai ta gyaɗa mata, tana futowa falon, Mrs. Ngozi na biye da ita da farantin kayan marmarin a hannunta har ta dire shi a gaban madaidaicin tebirin dake gaban kujerar da Nabeela ta zauna.
"Akwai wayoyina a kan gado, ko zaki taimaka ki ɗauko min?" Ta faɗa da muryarta mai taushi da sanyi, muryar da ita kanta take adawa da zamanta a matsayin tata ce.
Kai Mrs. Ngozi ta risina tana mai mata jinjina, ta shige ɗakin bata jimaba ta fito mata da wayoyin.
Kunnasu ta yi ta suka kawo haske sai kuma suka ɗauke saboda rashin cajin da ke tare da su.
"Ki sa min a caji, akwai charger ne?"
"Eh madame." Ta faɗa tana kwasarsu da jonasu a cajin nan take suka ɗauka.
Kallo ta kunna mata ta ajiye mata remote "Yawan tunani nasa damuwa, Madame."Kallonta Nabeeha ta yi, sai ta gyaɗa kanta, ta ɗauki remote ɗin, ba dan tasan me zata yin ba, sai dai dan ta ɗauka ta daddanna shi ko ta samu damar samun wani abun da zai sauya tunaninta.
Zuciyarta na cike taf da tunanin saƙonnin Nabeehan da bata buɗe ba, tana son karantawa amma tana tsoron yanda zata ci gaba da tsinewa kanta.
Ba zata iya jurewa zama a wajenba, tilas ta kada baki ta kira Mrs. Ngozi ta ɗauko mata computer ta.
Tana kawo mata ta shiga duba saƙonnin da suka ƙara fidda tarzomar ambaliyar ruwa a idanuwanta._30th June, 2020 'Ina kewarki sosai, na rasa wanda zanyi magana da shi. Likita ya tabbatar min cewar kwanaki da suka rage min basu da yawa. Amma ina fatan na ganki ko da sau ɗaya ne kafin na mutu. Ki yafe ni.'_
Da sauri ta sa hannunta a kan idanuwanta tana rufe su yana jin yanda numfashinta ke bugawa da ƙarfi, duniyar na juya mata komai na hargitewa a duniyarta....
🌹🌷🌹🌷
Ƙawata ce! Paid book ne a kan N300 kacal, akwai free pages da za su biyo baya a gaba.
Ga masu buƙatarsa za su iya turo kuɗin ta wannan accnt 👉3051894647 Hajara Ahmad Hussain polaris Bank. Su tura katin shedar biyansu ta wannan lambar 08030990232 ko +234 703 513 3148 Ga wadda basu da accnt kuma za su iya turo katin waya na mtn ta waɗannan lambobin.
Ga 'yan Niger kuma za ku iya tura tura carte moov ta 400 zuwa ga number +227 84 50 64 76#KWTC
#NWA
#CMNTS, LIKE SHARE,
#GIRMAMAWA
#DABANNE.
YOU ARE READING
ƘAWATA CE
ActionLabari ne akan ƙawaye biyu masu halayya ɗaya! Labarin sadaukarwa a inda bata kamata ba! Ƙauna marar algus! Yarda marar iyaka! Aminci marar gudana! Tafiyar hawainiya da rikiɗewarta! Idan kun fara zaku so jin tafiyarsa. "Ita kaɗai ce ƙawar da na tas...