FITA TA BIYU

103 11 1
                                    

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS
  
     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA BIYU.

  A hankali ta fara buɗe idanuwata, tana jin nauyin da ke kanta kamar ba a jikinta ya ke ba, tana jin kamar duniya a ka ɗauro a ka aza ta a bisa kanta.
  Idanuwata ta buɗe tana ganin dishi-dishi wadda yasa ta ƙara lumshe idanuwan  na ɗan lokaci, ta na kuma ƙara buɗe su a karo na biyu. Sai dai hasken fitilar da ya mata dirar mikiya a cikinsu ya tilasta mata sake rufe su.
   Ta ɗauki tsawon lokaci tana rufe da idanuwan nata, kafin kuma mafarkin da ta yi ya fara dawo mata a kanta.
  _'Mafarkin da na yi na Nabeeha ta kira ni ta mallaka min ragamar aikinta, kana ta damƙa min hannun mijinta da kuma son mu auri juna. A ƙarshe kuma jikin Nabeeha ya rikiɗe likitoci sun jata sun shigar da ita ɗakinta, wani kakkauran likita mai fuska kamar an naushi kunkuru ya ke sanar da mu mutuwar Nabeeha da ƙarin yi mana ta'aziyya.'_
  Murmushi ta yi wadda da alamun na takaici ne tana ƙara yin magana a zuciyarta 'Lallai na ƙara yadda ba abin da ya kai sheɗan gudana a jikin ɗan Adam. Ban da haka taya mafarkina zai haɗa min waɗannan abubuwan?'
  Hannu ta ɗaga da zummar sosa girata sai dai ta ji ya mata nauyi, nauyi na sosai da kuma jin wani abu kamar zare a jikinsa na binta.
  Hakan yasa ta buɗe idanuwata da sauri tana juyar da kanta, da kai kallonta ga hannun nata, sai dai abun da ya bata mamaki bai wuce ganin jonin ruwa a cikin hannunta ba.
Yana biyowa ta jikin zaren yana sauƙa a jikinta, a zabure ta miƙe zaune tana jujjuya kanta da kai kallonta ga ɗakin da ta ke.
   'Tabbas asibiti ne.' A asibiti take domin komai da ya danganci ɗakin na asibiti ne, amma mai ya kawota asibiti ita da take kwance a gida.
    Wani abu ne ya doka a kanta da ƙarfin gaske, zuciyarta kuma na bugawa da ƙarfi kamar zata faso daya ƙirjinta.
     Ƙofar da aka turo ne ya bata damar mayar da kallonta ga masu turo ƙofar Likita ne da wasu Nurse's guda biyu mata, bayansu kuma Anty Ummi ce fuskarta babu alamun fara'a idanuwanta sun jeme sun koɗe kai kace ta shekara guda tana kuka.
    "Alhamdulillah ta farka ai." Likitan ya faɗa da ɗan murmushi a kan fuskarsa, wadda kuma tana iya ganin murmushin a kan sauran Nurse's ɗin.
   "Dama ko bata farka ba zamu mayar da ita gida ne." Ta ji sautin muryar Anty Ummi na fita da kauri kamar indararon da ruwa ke zuba a cikinsa.
  Tana iya hango zallar tsanar ta a idanuwanta, da kuma takaicin da bata san ko na mene ne ba.
   "Alhamdulillah dai tunda ta farka ɗin. So zan ƙara dubata sai na ji idan akwai yiyuwar ku tafi tare da ita ɗin."
   Likitan ya faɗa yana ƙarasawa kusa da Nabeela yana kwantar da muryarsa da tambayarta ya jikin nata.
    "Yau kwana ɗaya kenan da yini guda kina cikin doguwar suma. Amma Alhmadulillah tun da yanzu kin farka. Ina fatan ba abin da ke miki ciwo a yanzu?"
    Ya yi maganar yana kallonta, sai dai ita bata cikin yanayin mai kyau, asalima tunaninta ya tafi ne can wata duniya da ban na rashin sanin inda zata je.
    "Kwana ɗaya da yini guda. Me ya faru da ni?" Ta jefawa likitan magana wadda ta lura tambayar da ta yi ta fusata ran Anty Ummi.
    "Dan Allah likita ka sallame mu, muna da abin yi mun bar mutane a waje ga kuma 'yan gaisuwa na zuwa."

    "Ƴan gaisuwa? Wa ake wa gaisuwar? Waye ya rasu?" Ta yi tambayar kamar zautacciya kafin kuma tunaninta ya wullata a duniyar da take tunanin mafarki ta yi.
  Hakan yasa ta miƙe tsaye jikinta har rawa yake ta fincike jonin ruwan da ke jikinta, jini ya biyo hannunta amma bata damu da jinin ba, kamar yadda bata ji zafin fizge allurar ba.
  Ta ƙarasa gaban Anty Ummi ta ɗora hannunta a kafaɗar Anty Ummi tana girgiza ta "Da gaske ne ba Mafarki na yi ba cewar Nabeeha ta mutu! Da gaske ne dama duk abin da ya faru a ranar ba mafarki ba ne Anty Ummi!" Ta gama maganar tana gunjin kuka ko ina a jikinta yana rawa, tana jin wani maƙaƙi da ɗaci na huda sassan jikinta, wani abu da ya tokare a wuyanta ya gaza faɗa mata.
      Sauƙar da hannayenta ƙasa Anty Ummi ta yi daga jikinta, tana jifanta da wani mummunan kallo, kallon da bashi da maraba dana ƙiyayya da tsana duk da ta kasance babbar yayarta da suka fito ciki ɗaya uwa ɗaya uba ɗaya.
   "Nabeeha ta mutu Nabeela! Ta tafi ta bar miki duniyar, sai dai kafin ta mutu ta bar miki komai da yake nata, ta bar miki komai da ya danganci rayuwarta ta duniya. Ina jin kunya da takaicin kaina da na zamo ɗaya daga cikin yayinki da kuke ciki ɗaya, ina neman wata ƴar ƙaramar ɓular da zan yi fatan ace na bi ta cikinta dan na goge kasancewarki jinina Nabeela.
   Ban taɓa tunanin a rayuwa wani na tsanar wani haka ba, da idan naji ana cewa wani na tsanar wani sai na ɗauka ƙarya ne.
  Sai gashi karo na farko a cikin rayuwata na ji na tsani mutum, mutum ɗin ma ke da kika kasance ƴar uwata." Ta gama maganar tana share hawayen da ke sauƙa a kan fuskarta wadda kuma kamar tana ƙara gudun su ne a kan fuskarta.
   Tana kallon Fuskar Nabeeha da duk wani faɗi tashin da ta sha yi a rayuwarsu. Ta kasa tsayar da hawayenta kamar yadda ta kasa tuno da kyawawan ranakun da suka haɗa kusancinta da ita.
    Kuka Nabeela ke yi tana matse ƙirjinta da take jin zafi na sauƙa a cikinsa, risinawa ta yi ƙasa ta fara dukan ƙasan tayil ɗin da ke malale  a ɗakin.
    "Wallahi da mutuwa na bada zaɓi a kan wadda zata ɗauka, wallahi da mun bada ke a madadin Nabeeha." Maganar Anty Ummi ta sake sauƙa a kan kunnuwan Nabeela wadda zuwa yanzu bata jin zafin maganar ta su, ita kanta tasan rayuwarta ta gimtse kamar yadda ta zo ƙarshe.

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now