FITA TA 19

46 7 1
                                    

https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS

     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA GOMA SHA TARA

    Bata san adadin lokacin da ta ɗauka tsaye a wajenba, amma zata iya cewa ta share fiye da sa'o'i uku tsaye tana bin ƙofar da Nu'aiym yabi da yaran.
   Tsugunnawa ta yi a kan ƙafafuwanta tana riskar kuka, kukan da take da tabbacin yanzu ta fara yinsa, za kuma ta ƙarar da rayuwarta ne cikin yinsa. Domin babu wanda zai bata kalma ɗaya na haƙuri balle ya ɓata lokacin lallashinta.

    To amma kuma a matsayinta na musulma zata yi ta kuka ne tana aibata kanta a kan abin da na zata iya dawo da shi baya ba? Wannan wata tambaya ce da sashen zuciyarta mai ƙwarin gwuiwar ya tunatar da ita.
   "Ki tashi ki miƙa lammuranki ga Allah." Wata mummunan zuciyarta ta shawarceta da shawara mafi kyau.
   Hakan yasa ta miƙe da ƙyar kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta nufi ɗakinta, ta faɗa toilet ta ɗauro alwala, ta shimfiɗa abin sallah da zura hijabi a jikinta.

    Zata iya cewa ta daɗe bata samu nutsuwar ruhi a tare da ita ba kamar yanda ta samu a yanzu da take sallahr, ta haƙiƙancewa kanta da yin imani a kan Ubangiji na jinta, zai amsa roƙonta zai yafe mata laifukanta zai kawo mata sauƙi a kan halin da take ciki.
   Ta yi tsayuwa mai tsayi ba tare da ƙafafuwanta sun gajiya ba, bata ga nisan dare da lokacin data ɗaauka ba, domin a yanzu daren ya zame mata kamar wani abokin tattauna damuwarta ne, tun bayan rasuwar Nabeeha bata ƙara rufe idanuwanta da sunan bacci da dare ba, koda ya kasance gwani wajen iya sace mutane amma a gareta ya gaza sosai, satarsa ta zama tamkar babu, tamkar shahararsa dai ta ƙare ne.
   Gaba ɗayaa Addu'arta a kan Nabeeha ta ƙare, tana nema mata rahamar Ubangiji, tana kuka a lokacin da ta ɗagaa hannunta sama, tana kuka mai sauti a duk lokacin da ta tuna tana yiwa Nabeeha addu'a ne da bata raye.
    Idan ta haɗa rayuwarta data Nabeeha zata ga a komai na rayuwa Nabeehan ce gaba da ita, tana fatan har a yanzu ya zamana ta samu dace da rabo da gidan Aljannah, wanda take da yaƙinin zata zaamu, kyakkyawan halinta ya isa ya mata jagorar shigar da ita Aljannah.
  To itafa, me ma ta yi a rayuwar? Wani abun alkhairi guda ɗaya ta aikata ga rayuwarta? Hana iyayenta kwanciyar hankali ko kuwa dai butulci da cin amanar da ta yiwa mutanen da suna yarda da ita?
  Inama dai rayuwa zata bata dama ɗaya tak, damar da zata dawo mata da Nabeeha kodan ta nemi yafiyarta. Sai dai kamar yanda ta sani ne tun ƙuruciya ba a mutuwa a dawo.
  Bata saan ta share tsawon lokaci ba sai da ta ji liman na iƙamar shiga sallah, hakan yasa ta kalli agogon bangon ɗakin taga ƙarfe biyar da minti goma na asuba.
Lallai lokaci bai da wahala, idanuwanta kuwa a soye suke ƙyam kamar soyayyiyar gyaɗa babu alamun jin bacci a tattare da ita.
Koda ta idar da sallahr ma haka ta ɗauki alƙur'ani ta fara karatu, muryarta na fita a hankali da rawar murya, tana ƙara girmama ƙarfi da buwaya na Ubangiji da hikimarsa, tana cikin karatun tana tuna shekarun data shafe rabonta da ta ɗauki Alqur'anin ta karanta, da ba dan kar ta yi ƙarya ba da sai tace tun lokacin da ta ke biyayya ga duniya, take ganin karanta ya kai tsaiko itama, tana kuma ganin daidai take da warkin kowa a zamanance da kuma tsabobin dake riƙe a lalitarta. Duk da a  lokacin burinta na ga abin da ke gabanta, tana son ta taka wata muhimmiyar rawa ne fiye da wanda take takawar, tana son sunanta ya zagaye duniya kowa ya santa a matsayin hamshaƙiyar attajira ba wai ɗiyar malam Aminu Mu'azu ba.

  Hasken da garin yayi da kuma bugawar agogonta zuwa ƙarfe shida, yasa ta dakatar da karatun da take ta yi addu'a ta shafa.
  Da hijabi a jikinta ta fito falon kai tsaye ta nufi hanyar da zata sadata da kitchen ɗin gidan, yau ɗaya tana so ta shiga taga halin da kitchen ɗin yake ciki, ba zata bari yaran Nabeeha su ci jagwalgwalen arne ba, da hannunta zata girka ta bashi umarnin jerawa ɗin.
   Sai dai kuma bata san me suke so ba, kamar yanda bata san wani abu na musamman da suka fi ƙauna ba. Amma dai zata yi abin da take gani yana da sauqin yi.
  Lokacin da ta shiga ta tadda kukunsu na ta hada-hadar haɗa girki har ya fere dankali zai fara soyawa, ganinta ya sa ya miƙe yana risinawa.
  "Good morning Ma'am." Ya faɗa cikin ladabi. 
  Kai ta jinjina tana amsa masa da yaren nasa da tambayarsa mai zai girka.
  Kamar koyaushe zai soya dankalin turawa da ƙwai sai shayi. Kai ta girgiza masa.
   "Yau dai kam na hutarka, amma zaka taimaka min da wasu aiyukan." Ta faɗa da harshen turanci hakan yasa ya risina cikin girmama ya bata wajen.
  Ta buɗe firjin dake kitchen ɗin taga akwai komai da take buƙata, ta ɗauki dogon lokaci tana nazarin abin da zata girka daga bisani ta yanke shawarar a kan zata girka:

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now