https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
ƘAWATA CE! 💕
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
©OUM-NASS
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
_Assalama alaikum masoyana, 'yan uwana, masu haƙurin bibiyar rubutuna. 😄 Bayan tsawon kwanaki da jinkirin da aka samu na dakatawa, yau Allah yayi dawowata, mun kammala exam. Ina fatan addu'arku, ina kuma jinjina muku wajen dakon jirana. Ina girmamaku har a ƙasan zuciyata._
FITA TA GOMA SHA ƊAYA
Tasha Addu'a da fatan Allah ya bata mijin aure na bugawa a jarida. Miji na kece raini wadda ya mallaki komai na rayuwa, daga kan Kyau zuwa dukiya da Ilimi.
Shi yasa a farkon rayuwarta ta ji cewa, Nu'aiym da ita ya dace ba da Nabeeha ba. Ta so kasancewa tasa ta ƙarfin tuwon da take da shi, da kuma dabarunta.
Ashe ita ke haukanta da kuma jahiltar rayuwa, da ta yi haƙuri da ba ta ɓata komai ba, ƙila da yanzu ba wannan zancen ake ga. Ƙila da yanzu ta samu gatan rakiya na 'yan uwa. Ƙila da yanzu tana ci gaba da rayuwarta kamar sakakkiyar tsuntsuwa.
Ƙila kuma da tana tare da Nabeehanta, da tana mata hirarta mai daɗi, da tana ƙarfafa mata gwuiwa a kan rayuwa.
Amma wannan duk zai ƙare ne a cikin ma'aunan mafarkinta, kamar dai yadda zai ci gaba da kasancewa nadama har ƙarshen rayuwarta.Wani ranƙwashin da aka zabga mata a tsakiyar kanta yayi sanadiyar dawo da ita duniyar tunanin jiyanta, ɗaga idanuwanta da tayi da kuma yin arba da fusacacciyar fuskar, Baba Adamu, su suka ƙara yawaita bugawar numfashinta.
"Kina sane da cewar Jirgin nan ba na, Aminu ba ne, da zai ci gaba da jiran har ki gama karanta wasiƙar jakinki ki dawo duniya.
Haka kuma mu ba shashashun da zamu tsaya muna ta faman yin magana ɗaya da kuna ankarar da ke ba."
Kai ta gyaɗa hawaye na gangarowa a idanuwanta.
"Kuka kam yanzu kika fara yinsa, Nabeela. Za kuma ki ci gaba da yinsa har zuwa ƙarshen rayuwarki. Ba fata nake miki ba, amma dai ki adana hawayenki dan ni bani da imanin da zan tsaya ina lallashinki.
Tashi mu tafi ko na zazzabga miki mari!" Ya ƙarasa maganar a tsawace wadda tasa Nabeela tashi da hanxari har tana ƙoƙarin kifewa.
Ta fito a jirgin ba tare da ta ƙara tunanin akwai wani abun da ya dace ta tsaya ta ɗauka ba.
Ƙwafa Baba Adamu ya yi yana janyo jakar kayanta shi kansa yana jin tausayinta, yana jin kamar ya ci gaba da lallashinta.
Amma kuma, Nabeela zuma ce dole sai da wuta, idan yace zai rarrasheta shima to babu shakka zata ci gaba da tsintar furenta ne yanda ranta yake so.
Yana ganin yadda, Nameer ke mata magana yana dafa kanta da riƙe hannunta, da alamu dai rarrashinta yake yi. Yana girmama, Nameer har a zuciyarsa, kamar yadda yake girmama ƙarfin imaninsa da sadaukarwarsa.
Mutane irinsa a duniyar nan basu da yawa, zai iya cewa ma bai gansu ba, bai kuma yi karo da su ba.
Tsaki ya buga a lokacin da ya ƙaraso kusa da su "Gulmata kuke yi ne, Nameer? Nasan ai ba a son ranka na taho rakiyar ba, babu kuma yadda za ka yi da ni. Domin idan a ka ci gaba da haɗa, Nabeela da mutane irinka imaninta zai ƙara dulmiya, ya kasance taba samu komai ba sai shagala."Dariya Dady ya yi yana shafa kansa "Wane mu da gulmar, Babban Yaya? Ina dai ƙara dannarta ne da bata haƙuri, ban san ka ƙaraso wajen ba."
"Dama ina zaka san na zo." Baba Adamu ya faɗa yana zabga harara da shigewa bayan motar wanda dama tuni Nabeela ta shige ciki.
Shima Dady shiga ya yi gaba, direban da, Nu'aiym ya turo musu ya ja motar suka lula a tsajiyar titi.Kai tsaye unguwar Asokoro ya wuce da su, tun daga yanayin tsarin unguwar zaka san unguwa ce ta ganggan masu hannu da shunu, waɗanda suka yada haƙarƙarinsu a cikin nairori. Gidaje na alfarma aka yi ta wucewa da su, har aka zo wani tamfatsattsen gida da ita.
Wanda shigarta gidan ya haddasa mata bugawar zuciya, gidan da ko a mafarkinta bata yi tsammanin zata sa ƙafafuwanta a cikinsa ba. Duk da tana buri, tana fata, amma nata taɓa hasashen cikar burin nata ba, bata taɓa tunanin xata mallaki fiye da abin da ta so mallakarsa a baya ba. Shin hakan sa'ar rayuwa ne gareta ko kuma dai ɗaurin talala Allah ya ke mata?
"Sai ki fito ko!" Saurin muryar Baba Adamu ta daki kunnenta, wanda hakan yasa ta dawo daga duniyar tunanin data lula.
Bismillah ta yi, tana zuro da ƙafafuwanta a hankali, ta ajiye su a shimfiɗaɗɗiyar tsakar gidan, ƙamshin furanni na yiwa hancinta maraba da zuwa. Kafin haɗaɗɗen turarensa da ta laƙancin ɗanɗanosa ya buso cikin ƙofofin hancin nata.Tana jin yanda sautin nutsattsiyar muryarsa mai sauƙa da amo da sanyi ke fitowa a jeri suna dukan kunnuwanta.
"Sannunku da zuwa Dady. Ban san ku zaku zo ba ai, da ni da kaina zan je na ɗauko ku." Ya faɗa yana risinawa har ƙasa da gaida su.
Baba Adamu da ke cika yana batsewa ya fara wangale bakinsa yana dariya "Ba komai, hakan ma ka yi ƙoƙari, abin da tilasta ma aka yi ba dan kana so ba. Tunda dai shi, Namir ɗin shi yayi amansa, ai lashewa ya zame masa dole." Ya faɗa yana riƙe hannun Nu'aym ɗin gam.
Shikam jikinsa yayi sanyi ƙwarai, kamar dai yadda yake cike da jin nauyin Baba Adamun. Sashen zuciyarsa na ƙara ɗago da wani zuzzurfan mikin da yayiwa zuciyarsa ƙababa ba. Yana kuma iya hango girman rashin adalci da karar da surukin nasa ya masa, bai bari ya ji da raɗaɗin rashin matarsa, abar begensa ba ya liƙa masa baƙar kadara.
Tabbas Nabeela baƙar kadara ce a gareshi, fiye da hakan zai iya kiranta, idan ya danganta ta da yanda ta zame masa tamkar tauraruwa mai wutsiya a zamantakewarsa da Nabeeha. Ƙila badan ta kutsa cikin rayuwarsa ba, da har abada zai ci gaba da kasancewa da Nabeehansa ne."Muje ko ɗana." Maganar Baba Adamun ta dira a kunnuwansa yana ƙara damƙe hannayensa da masa jagora kamar dai shine mammalakin gidan.
Bayan zamansu a luntsumemmiyar kujerar da ke zagaye a katafaren falon. Afafawo kukun Nu'aym ya gabatar musu da abinci da ruwa.
Sai dai daga ciki babu wanda suka taɓa, illa dai Baba Adamun da ya sake gyara zamansa, yana fuskantar Nu'aiym da ke zaune a ƙasa, kansa a sunkuye cike da girmamasu."Da fari dai ina mai baka haƙuri, Nu'aiym a kan rashin adalcin da aka yi ma. Rashin adalcin yima kutse a cikin rayuwarka, rashin adalcin aura ma yarinyar da baka so, rashin adalcin barin zuciyarka ta gama alhinin mutuwar matarka."
Ya yi shiru yana jan numfashi da sauqe ajiyar zuciya.
"A kan hakan ina baka haƙuri ƙwarai da gaske. Saboda da ace ina nan to ina tabbatar maka ba zan bari hakan ta faru ba, duk da na ji uban naku yana cewa wasiyyar Marigayiya Khadijatu ce ya cika mata, bisa amincewarka. Amma kuma ni koda ace Khadijatun zata min fatalwa ne ba zan bari a ƙulla wannan al'amarinba.
Amma ba komai, komai yana hannunka, idan har ka ji ba zaka iya ba, kana da zaɓin warware igiyar auren, mu kuma a kan hakan ba zamu ma kallon marar adalcin ba, saboda dama can zaren ba a ƙulla shi a kan adalcin ba."Ɗago kansa Nu'aiym ya yi yana kallon Baba Adamu, yana jin kowacce maganarsa kamar sauƙar ruwan ƙanƙara ne a zuciyarsa, yana jin wannan dama ce babba a gareshi, damar da zai iya sahalewa Nabeela fita daga rayuwarsa har abada.
Domin baya jin zai iya jurar koda maƙwaftaka ce da ita, koda hanya ɗaya baya maraba da haɗawa da ita. Kai inda ace ka zai ga alamun ta bi hanyar ne to kuwa zai ƙare rayuwarsa har abada ba tare da ya tatsa ta cikinta ba. Balle kuma su kasance a gida ɗaya a waje ɗaya.Tabbas ba zai bari damar nan ta wuce shi ba. Hakan ya sa ya buɗe bakinsa cikin jin daɗi da sauqaqa bashi damar da mahaifinta ya bashi "Baba ni kaina bana s..."
Maganarsa ta riƙe sanadin wani hasken da ya gilma a idanuwansa, wani sauti mai amo da rauni na shiga kunnuwansa.....
🌷🌹🌷🌹🌷🌹🌹🌷
Afwan afwan. Ku ƙara haƙuri.
YOU ARE READING
ƘAWATA CE
ActionLabari ne akan ƙawaye biyu masu halayya ɗaya! Labarin sadaukarwa a inda bata kamata ba! Ƙauna marar algus! Yarda marar iyaka! Aminci marar gudana! Tafiyar hawainiya da rikiɗewarta! Idan kun fara zaku so jin tafiyarsa. "Ita kaɗai ce ƙawar da na tas...