FITA TA GOMA

51 9 0
                                    

https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS

     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA GOMA

  Cikin abin da bai wuce mintuna uku ba sai gata ta fito, ta fara ƙoƙarin shafa mai.
  Baki Momy ta buɗe tana kallonta fuskarta da gashinta duk kumfa ce, alamun ba ta tsaya ta yi wankan da nutsuwa ba. Yayin da jikinta ke ɓari kamar mazari.
  Riƙe hannunta Momy ta yi tana girgiza kanta "Ki tsaya ki nutsu Nabeela. Ki komai Toilet ɗin ki sake wanke jikinki, kumfa duk a gashinki, hatta fatar jikinki sheƙi take irin na wadda ya zoza sabulu bai kai ga wake shi ba."
   Hawaye ne ya gangaro a idanuwanta, hawayen da bata shirya sauƙarsa a kan idanuwan nata ba "Idan na tsaya Baba Adamu karya ni zai Momy. Ki bari zan goge da tawali."  
  Ta yi maganar tana goge jikinta da tawul ɗin, a gurguje ta mulka mai, wadda ya mata tabbara-tabbara saboda rashin tsantsame jikinta da bata yi ba da kyau.
  Dafe kai Momy ta yi, tana ƙara jin tausayin Nabeela na ratsa zuciyarta.
  Hannunta ta ruƙo ta jata har zuwa toilet ɗin ta ƙara haɗa mata sabon ruwan wanka.
   "Ki yi wanka mai kyau, ko kuma ni na miki da kaina." Momy ta faɗa tana fita a Toilet ɗin da ja mata ƙofa da rufewa.
   Kallon ruwan ta yi, yadda yake fitar da ƙamshi da kuma ɗumi a jikinsa. Hakan yasa hawaye gangarowa a kuncin idanunta.
  Bata da lokacin da zata ɓata kodan sanin Baba Adamu na zaune a falo yana jiranta, sunan wankan dai jeka na yi ka, amma ita kanta tasan ba wai ta yi sa ba ne yadda Momy ta buƙata.
  Mintuna biyar ta yi ta ƙara kwara ruwan a jikinta ta fito, da baki buɗe Momy take kallonta kafin ta yi magana ta yi saurin rigata yi.
   "Dan Allah Momy karki ce ban fita ba!" Ta yi maganar hawaye na gangarowa a kuncinta.
  Girgiza kai Momy ta yi sannan ta zaunar da ita ta fara goge mata jikinta a hankali.
   "Rayuwar aure aba ce mai cike da wahala da sarƙaƙiya, Nabeela. Ko da ace akwai soyayya a cikinta dole sai ka ɗauki mayafin haƙuri, ka haɗa da bargon juriya sannan kake iya zaman aure.
   Duk macen da kika ganta a gidan mijinta, tana zaune ne ƙarƙashin waɗan nan abubuwan guda biyu, amma ba wai tana zaune ne da abubuwan faranta rai na har abada ba. 
  A yanzu ƙaddara ta riga ta mallaka miki Nu'aym a matsayin mijinki, ina fatan za ki haɗa abubuwan nan guda biyu ki yi tarayya da su a wajen zamanku. Nasan komai da ke faruwa tsakaninki da shi, sai dai hakan ba zai sa a ce rayuwar zata ci gaba da tafiya da ku a kan hakan ba. Ki rufe tsohon kundin da ya haɗa ku a rayuwarku ta baya, ki kuma buɗe sabon rayuwa a matsayin sabon mutumin da kika sa ni a yanzu."
   Idanuwanta ta ɗago da suka gama yin ja kamar gauta, sun kuma kunbura sun ƙanƙance ainun.
    "Momy tarihi baya taɓa goguwa, koda ace na yi ƙoƙarin goge shi akwai dubbanin ramukan da suke cike taf a ƙwaƙwalwata da ba za su bani damar hakan ba.
   Akwai dubbanin mutanen da suke tsaye a da'ira dan tunasar da ni munanan aiyukana. Akwai wahala, akwai ƙunci Momy nasan ba zan taɓa iyawa ba."
    "Kin riga da kin iya Nabeela. Kawai za ki tuno ƙwarewarki ne a kan hakan." Momy ta yi saurin bata amsa tana sa hannu da goge mata hawayen fuskarta. Yayin da ta ke binta da kallo tana hasko babbar katoɓar da ta yiwa rayuwarta giɓi. Ta sani dauriya ce da kuma sadaukarwa kawai su Momy suke mata, wadda ko kaɗan bata cancanci hakan ba kamar yadda kowa ke faɗa. Kowan da ya kasance mai hankali da kuma fahimtar zahirin rayuwa.

   "Kin riga da kin yi kuka mai yawa. Ko da wannan hawayen naki da basa tsayawa sun cancanta su fanshi farin cikin ki."
    "Farin ciki!" Ta faɗi kalmar kamar mai son tuno wani abu a kanta. Kanta ta girgiza tana ƙoƙarin dafe ƙirjinta da take jin ya mata nauyi.
    Rigar mama Momy ke ƙoƙarin ɓalla mata hakan ya dawo da ita duniyar da take ciki a yanzu.
  "Zan iya, Momy." Ta faɗi maganar cikin jin kunya da kuma nauyin momy ɗin.
   "Maza sa."
Sawa ta yi tana ƙara sunkuyar da kanta daga kallon Momy, wadda fahimtar hakan yasa ta juya mata baya.
   "Ki hanzarta mu fita."
A gurguje ta sa kayan wadda ya kasance rantsattsen leshi ne kalar purple kalar da take mutuƙar so da ƙauna, kodan kasancewarta fara ce yasa hakan, ko kuma dan kasancewar tana mata kyau ne yasa take ƙaunarta a waccan lokacin.
  Amma a yau da zata sa sai taga ta mata duhu ƙwarai, kamar yadda take da tabbacin munin da zai mata a jikinta.

    "Wai, Nameer da ka barni zaune gingum a kan kujera tun ɗazu, hala so kake na kwana a nan wajen ba tare da mun je inda ya kamata mu je ba?" Sautin hargagin muryar Baba Adamu ta sauƙa a kunnenta.
  Tana kuma iya kin amsar da Dady ya bashi cikin sanyin murya "A'a Yaya yanzu za su fito. Ba na kira Momynsu.
   "Na bari." Baba Adamu ya faɗa yana ƙara haɗe ƙasusuwan fuskarsa da babu tsoka a cikinta sai fitina.
   "Ka jaddada mata cewar ba gumaka ta ajiye a kujera ba, ba kuma gadi ta ba mu kwangilar yi mata ba."
   Tun ma kafin ya rufe bakinsa suka fito, yana ganin Nabeela da kakkauran leshi a jikinta, wadda ko ba a sanar masa da kuɗinsa ba ya san ta lashe kuɗaɗe masu yawa.
    "Lallai, Ramlatu! Har wani kuɗi kika wani kashewa wannan abar? Tabbas zama da ku kaɗai zai iya ƙara gurɓata zuciyar gurɓatacce, ya yi ta cutarku yana dawowa kuna rarrashinsa."
Ya yi maganar yana ƙara buga tsaki, yana iya jin da yana da dama ba abin da zai hana ya lakaɗawa Nameer da matarsa Ramlatu duka.
  Saboda sune ummul aba'isin komai na lalatar da Nabeela ta yi a baya.

   Sanin Halin yasa Momy yin murmushi ta risinar da kanta ƙasa "Yaya ina kwana?"
Harararta ya yi yana amsawa da "Lafiya. Kamar zancen nawa bai da muhallin da za a amsa shi, shi yasa a ka ce min ina kwana kamar wadda ya kwana a murhu wuta na cinsa."
   "A'a yaya ba haka bane, naga lokaci na tafiya ne. Ina su Yaya Umma? Na ɗauka tare da su za a yi tafiyar."
   "A'a bama buƙatar tarkace a tafiya da sininniƙi, ni da Nameer ya wadatar."
  Ya kai kallonsa ga Nabeela da zuwa yanzu ta ƙara sautin kukanta, kukan da bata san ranar daina shi ba.
  'Da gaske ni za a kai gidan miji? Ni ɗaya tal ba tare da 'yan uwa ko dangina ba. Ni ɗaya tal sai iyayena maza guda biyu! Wayyo Allah na!' Ta yi maganar a ƙasan zuciyarta tana ƙara sautin kukanta.
    "To wuce mutafi kulɓa uwar ɓarna." Baba Adamu ya faɗa da tsawa, wadda yasa jikin Dady sanyi ya ruƙo hannunta.
  "Mu tafi Nabeela."
Juyowa ta yi tana kai kallonta ga Momy, wadda itama ɗin ita take kallo, hawaye ne ya yi ƙoƙarin zubowa a fuskar Momy saboda tausayin Nabeela.
  Hakan yasa ta yi saurin juya bayanta "Allah ya kaiku lafiya Nabeela." Ta faɗa tana shigewa ɗakinta.
   Tun daga harabar gidan take hango mutanen unguwar na leƙowa dan ganin zahiri, sai dai duk a cikinsu bata ga wani nata guda ɗaya ba.  Wanin da ya amsa sunan jininta da ya tsaga a jinin jikinta. Duk yawan zugar 'yan gidansu amma ko kazar da ake kiwo a gidan bata ga shiftawarta ba, har suka fice a cikin motar, ta dai yi sa'a ta hango Mowa fuskarta a daƙume kamar kowanne lokaci, tana iya ganin yadda take jujjuya mulmulallen hannuta da sigar son harɗe shi a ƙirjinta, amma saboda kaurinsa ya gagara haɗuwa waje ɗaya.

   Kuka ta sa mai sauti a lokacin da tayar motarsu ta harba a bakin layin, tana hango ƙofar gidansu da ƙaddara ta shata mata layi mai kauri a tsakaninta da ita. Ƙofar gidan da a baya take ƙoƙarin ɓoyeta da sunan gidansu, yau take fatan ace ta samu alfarmar zura koda ƙafarta guda ɗaya ce a cikinta.
  Sai dai ƙaddara ta riga fata, ƙaddarar da zata iya kiranta da sunan ƙirƙirarta ta yi dan gyara duniyarta.

    "Ko ki mana shiru ko kuma yanzu na miki abin da zai sa ki yin kukan da dalili."
  Sautin muryar Baba Adamu ta sake kwarara a dodon kunnenta kamar sauƙar ruwan dalma a cikinta.
   Muƙuttt! Ta haɗiyi wani yawu mai kauri da ya tokare a iya ƙirjinta, ya kuma maƙalar da fitar numfashinta cikin nutsuwa.
  
   Dutse suka nufa, inda suka wuce filin jirgin da zai sada su da garin Abuja kai tsaye.
    Jirginsu ya lula a sararin samaniya, yayin da rayuwar Nabeela ta fara lulawa izuwa mizanin uƙuba, munana ranakunta suka fara aunawa da rige-rigen cimmata....

  🌷🌹🌷🌹
Ƙawata ce! Paid book ne a kan N300 kacal, akwai free pages da za su biyo baya a gaba.
  Ga masu buƙatarsa za su iya turo kuɗin ta wannan accnt 👉3051894647 Hajara Ahmad Hussain polaris Bank. Su tura katin shedar biyansu ta wannan lambar 08030990232 ko +234 703 513 3148 Ga wadda basu da accnt kuma za su iya turo katin waya na mtn ta waɗannan lambobin.
  Ga 'yan Niger kuma za ku iya tura tura carte moov ta 400 zuwa ga number  +227 84 50 64 76

#KWTC
#NWA
#CMNTS, LIKE SHARE,
#GIRMAMAWA
#DABANNE.

  Oum-Nass

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now