FITA TA 18

37 6 1
                                    

https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS

     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA GOMA SHA TAKWAS

  Girgizatan da Mrs. Mgozi tayi da kuma kiran sunanta ya taimaka wajen dawo da nutsuwarta, wanda sai da ta kai ruwa rana kafin idanuwanta su iya gane mata, Mrs Ngozi.
    Kallonta take kamar tana karanto zuciyarta a fuskat Mrs Ngozi ɗin.
  "Madame, zan je gida na dawo, an kira ni mamana ba lafiya."
  Ido Nabeela ta lumshe tana buɗe su da ɗorasu a kanta, kalmar Mamana da ta ambata ya cilla tunaninta zuwa Jigawa.
   Ba zata iya tuna yaushe rabon da su yi magana da tata maman ba. Kamar yanda ba zata iya tuna yaushe sukayi magana mai daɗi da ita ba, idan ba zata ƙaryata kanta ba zata iya cewa tun lokacin da komai ya kwaɓe mata, tun lokacin da ta fita a rayuwar Nabeeha, wanda mamanta ke ƙoƙarin ankarar da ita babban kuskuren da take shirin aikatawa. Sai dai a gareta kamar Ammu na hakan ne saboda ganin dukiyar Nabeeha, ta manta cewa Ammu ko zata mutu bata da kuɗi idan ta ba ta qin amsa take yi.
   "Madame, ina magana." Muryar Mrs. Ngozi ɗin ta sake dira a kunnenta kamar sauƙar guduma a kan ƙarfe.
   "Ki je, Allah ya bata lafiya. Ina gaidata." Ta samu bakinta da faɗar kalmomin.
  Haka yasa Mrs Ngozi risinawa tana mata godiya, daga haka ta fita tana mata bankwana.

       Bankwanan ko zata dawo a yau ɗin ko kuma yanda hali yayi ya danganta dai da yanda taga yanayin mahaifiyar ta ta.
   Itama miƙewa tayi tsaye ta ɗauki wayarta ta kunnata ganin ta samu caji.
  Contact ta shiga ta fara bin sunaye, tana jin yanda gabanta ke dokawa da ƙarfi, kan sunan Ammu ta tsaya, tana kallon yanda harrufan sunan ke ƙara girma a idanuwanta tana kuma iya jin yanda suke hautsina duk wata nutsuwar dake tare da ita. Sai da ta aro duk wata dauriyar da take da ita a baya sannan ta danna kiran.
  Shigar kiran na tafiya da harbawar zuciyarta, har sai da kiran ya katse ba a ɗauka ba, bata fasa ba ta sake kira yana gaf da katsewa aka ɗaga.
   "Assalama alaikum." Sautin muryar Ammu ya fita da amo, amon da ya ƙara harba zuciyarta, jikinta ya ɗauki rawa kamar tana ganinta.
  "Salama alaikum." Ammu ɗin ta sake faɗa daga cikin wayar.
  "To kuma ya ba a magana, ko kuma dai Service ne bai da kyau. Idan wanda ya kira yana jina to ni bana jin komai." Ammu ta faɗa tana ƙoƙarin sauƙe wayar, jin hakan yasa Nabeelan yin magana da muryarta mai rawa.
  "Dan Allah, Ammu ki yafe min!" Ta yi maganar tana fashewa da kuka.
  A lokacin Ammu ta buɗe idanuwanta daga can, tana sauƙe wayar a kannenta tana dubawa.
  Daga bisani ta mayar da ita "Tun yanzu? Ba dai har kin gaji ba, Nabeela?" Ta faɗa tana murmushi mai girma a kan kuncinta.
   Hakan yasa Nabeela zubewa a kan ƙafafuwanta tana ƙara sautin kukanta.
  "Ammu, Bana son komai ba. A yanzu rayuwata nake son dawowa, wannan ba rayuwata ba ce Ammu. Komai da nake da shi baya min daɗi, zafin ya haɗe min biyu, Ammu dan Allah ki yafe min ko na daina jin ƙuncin da nake ji."
   "Ai ƙunci yanzu kika fara ɗanɗana shi, Nabeela. Wannan ɗin dai ita ce rayuwar taki, wanda kika zaɓa kike so, kike kuma ganin muna miki adawa da zamowarki a cikinta. Ki karɓa daga abin da kika gadarwa kanki. Kada ki ƙara kirana daga yau, idan ba haka ba zan ajiye kalmar tsinuwar da naso yi miki tun a waccan lokacin." Daga haka ta yanke wayarta, ƙaran ɗit ɗit ɗit  na dira a kunnen Nabeela.
  Wayar ta bi da kuka tana ƙara fashewa da kuka, kuka mai sauti da amo.
 
    "Ya Allah ka sassauta min, ka rangwanta min badan halina ba, badan zunubaina ba, badan kuskuren da na aikata a baya ba." Ta ƙara fashewa da kuka mai sauti tana buga tafukan hannayenta a kan tiles ɗin da ke malale a ɗakin.
  Ƙara wayarta ta yi alamun shigowar saƙo a  cikin wayar, kamar ba zata buɗe ba sai kuma ta yi hanzarin miƙewa ta ɗauko wayar ta buɗe saƙon.
   _A duk lokacin da kike ciki damuwa, ki tuna Ubangijinki na kusa da ke, zai saurareki da zarar kin kai kukanki gare shi. Kar kiyi kuka da yawa, karki shiga damuwa da yawa, ki tuna adadin ƙuncin da nake shiga a lokacin damuwarki._
  _Nabeeha Nameer_

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now