FITA TA 19

46 6 1
                                    

https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS

     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA GOMA SHA TAKWAS

   Haɗejia Jigawa, Nigeria.

"Sai na ji kamar kina magana da Fatima?" Abba Aminu ya faɗa a lokacin da yake riƙe da labulen ɗakin Ammu.
   "Eh, ita ce." Ta bashi amsa a taƙaice.
"Ya take? Ina fatan tana lafiya?"
"Fiye da yanda za a ambata a baki."

Ya kula tana bashi amsar ne cikin gatse da kuma cije baki irin na wanda aka sa shi magana dole.
   "Kira min ita na yi magana da ita."
"Babu kati a wayana."
"Ba ni lambar na kirata a wayata." Miƙa masa wayar ta yi, ya shiga wajen kiran, sai dai bai ga lambar da aka kira a lokacin ba.

   "Da wani layi ta kira ki?"
"Babu suna."
"Kamar ya babu suna?"

"Kamar dai yanda ka san tana ɓoye lambar waya kafin ta kira, tana sake su a duk lokacin da ta so, wanda bai da gaskiya ina zai tsaya a waje ɗaya? Abu ne a buɗe da ka daɗe da riƙe shi."
Labulen ɗakin ya saki ya shigo ɗakin ya tsaya a gaban Ammu yana murmushi yana kallonta.
  "Har yanzu kina jin haushin Fatima? Ko kuma dai kin haɗa haushin har da ni mahaifin Fatiman?"
   Ɗago da kai ta yi tana kallonsa da mamaki, sai kuma ta sunkuyar da kanta ganin yanda ya mata gizo, ta san Aminu na da haƙuri, yana da kawaici, sai dai a kan komai da ya shafi Nabeela yana rasa wannan. Duk da yana ƙoƙarin danne hakan da son share ƙaunar da yake mata fiye da sauran yaran sa.

    "Me yasa zan ji haushinka?" Ta tambaye shi tana ƙara matse fuskarta da fito da yanayin damuwarta.

   "Saboda ina damuwa da lammuran, Fatima. Na kuma yi miki kashedi da iyaka a kan al'amarin aurenta."
  A wannan karon ta ɗago da kanta ta yi tana kallonsa.
  "Zaka iya yin komai da nuna ikonka a kaina, saboda da ni da su duka mallakinka ne. Ba kuskure ka yi ba, ba kuma abin da ya dace ne baka yi ba, ka nuna ƙarfin iko da ƙumajinka kamar sauran mazan. Ba zan aikata abin da zai sa ka ji na tsallake iyakokin da ka shimfiɗa min ba, ba zan yi kuskuren shiga rayuwar auren Nabeela ba, ko da a sigar hira ne."

  Hannayenta ya kamo ya riƙe a cikin ruƙonsa wanda hakan yasa ta ɗago da tana kallonsa tana jin wani rauni na ƙara ƙaruwa a tare da ita, tana jin kamar ta saki kuka, kukan da ta daɗe tana son ta yi tun bayan shuɗewar wasu abubuwa, tun bayan tafiyar Nabeela gidan mijinta bata samu sauƙi ba, bata tsallake tuhumar mutame ba, bata huta da gorace-goracensu mai kama da zagin da suke mata ba, wasu ma kai tsaye suke gabatar da fuskarsu gareta suke zazzaga mata kwandon tijara.
    "Ki yi haƙuri a kan komai, Hadiza. Komai ɗin da ya faru a baya da wanda zai faru a gaba. Ki bar tunani a kan mutane da kuma son wanke kanki daga garesu, domin ko kina shiga ruwan zamzam kin  faɗawa na zuma kina komawa cikin alkausara dan ki yi sheƙi, idan kika fito sai wani yace kin bar jikinki da hazo.
  Ba zaki iyawa Ɗan Adam ba, ba zaki iya zama fara ƙal a idanuwansu ba, zagi ba zabon abu bane, ba kuma rauni ne dake fito da tsiron miki a jikinmu ba, ki barsu su yi, idan sun gama xa su koma kan wani ne. Kawai ki amsa daga abin da ƙaddara ta baki, ta baki mai kyau da mafi kyau daga yaranki, a ƙarshe sai ta bayyana Fatima a matsayin ƙaddara mafi wahala dan kawai a jarraba imanin yanda zamu amsheta.
  Ina son Fatima sosai, Hadiza. Ina sonta fiye da sauran yarana, ina tausayinta saboda yanda rayuwarta ta zama a hargitse a bar gudu ga sauran mutane. Na san kema kina sonta, idan aka cire tsoron maganar mutanen da kike yi."

   Kukan da take riƙewa ne ya ƙwace mata, hakan yasa ta faɗa ƙirjinsa tana kukan "Ya zan yi da rayuwata ne, Abbansu? Kowa zagina yake saboda Nabeela. Kowa baya son magana da ni da zuciya mai kyau, tun bayan auren Nabeela da mijin Nabeeha har yau ko ƙofar gida ban leƙa ba. Saboda a cikin gidama ban tsira da habaicin mutane ba, ina ga idan na fita.
  Ya zan yi da rayuwata? Me yasa ƙaddara ta zaɓe ni  a sigar cin Amana ne?"
   "Ba kuskurenki ba ne, Hadiza. Ƙaddararki ce ta zo a haka, ki yi haƙuri ki karɓeta a yanda ta zo miki, kin ji. Ki yi fatan alkhairi ga rayuwar auren Fatima, ki nema mata shiriya da yafiya daga Ubangiji, komai zai wuce, zai wuce ne ya zama kamar ba a yi ba, kafin mu an zagi dubu ya mu, yanzu labarinsu ya wuce, an manta da su  ko a tarihi an rasa mai bada labarinsu. Muma kuma zai wuce ɗin in sha Allah."

   "Ina fatan naga wannan ranar." Ta yi maganar kafin ya amsa kuma ya ji buyagin kiran sunansa da Baba Adamu yak ƙwalawa.

   "Wai Aminu ba zaka fito mu je gaisuwar mutuwar nan ba sai rana ta take? Ni na rasa uban me zai yi a gida rana fatsau-fatsau ga yara ga komai."
  Da sauri ya fita yana murmushi yana shafa kansa da girmama tijarar yayan nasa da baya jin kunyar koma da faɗarsa.

  "Yi haƙuri yaya na tsaya duba wasu kaya ne."
  Harara Baba Adamu ya zabga masa "Eh ai gashi nan garin ɗauko su ka jiƙe da ziffa."
   A lokacin ya kai kallonsa ga rigarsa ya yi saurin baza hiraminsa yana murmushi suka tafi.

***
ABUJA, NIGERIA.

  Tun bayan maganar da ta shiga tsakaninta da Nu'aiym a kan fara aikinta, bata sake yarda sun haɗa hanya da shi ba. Duk da gidan ya mata girma sosai, babu wanda take gani, babu wanda take yin magana da shi, ko kukunta da yake dafa abinci yana jerewa ne kafin ta fito, a yawan lokuta tana ganin rashin dacewar sakar masa ragamar girkin gida. To amma ya zata iya, saboda ba a mayar da ita mutum a gidan ba.
  Hayaniyar da ta ji a gidan da surutun yara yasa ta gyara ɗaurin ɗankwalin doguwar rigarta atamfa da ke jikinta, mai adon pink ɗin fulawa da ratsin fari. Ta ɗauko mayafi ta kalar pink ta yane kanta da shi, ta fito falon.
   Ja ta yi ta tsaya a lokacin da idanuwanta ya sauƙa a kan Aarif da Aafiya, da suke ta tsalle-tsalle suna surutu.
  Wani ni'imtaccen sanyi ya ratsa tun daga maƙogwaranta har zuwa zuciyarta, sayin da take jinsa kamar na sauƙar ƙanƙara ne a tsakiyar garwashi.
   Murmushi ya suɓuce mata a laɓɓanta, tana ƙara takunta da faɗaɗa dariya a kan fuskarta "Ya Allah. Suwa nake gani kamar Nurainey?" Ta yi maganar da faffaɗan murmushi a kan fuskarta.
  Da sauri yaran suka tsaya daga tsallen da suke, suka waiwayo zuwa gareta, ganinta yasa suka kwantsama wani sabon ihun murna suna rige-rigen isa gareta.
   "Maama!"  Yaran suka faɗa suna rugowa da gudunsu.
    "Aarif!!" Wata murya mai tsawa ta faɗa daga bayan yaran, muryar da ba su kaɗai ba, hatta Nabeela sai da ta tsorata sosai da jin ta.
  Cikin sauri da taku mai ƙarfi ya fara takawa yana isowa gaban yaran ya musu shamaki a tsakiyarsu, bayan ya jefi Nabeela da mugun kallo, kallon da ya ƙara hautsina 'ya'yan hanjin cikinta.

  Ya ɗauki Aafiya a kafaɗarsa ya riƙe hannun Aarif ɗin, ya kalli Nabeela da fusatattun idanuwansa "Wannan ya zama karo na ƙarshe da zan hanaki bayyana fuskarki a gabana. Idan ba haka ba, zan nuna miki asalin waye ne ni.
  Sannan ki cire maitarki da zulamarki a kan yarana, domin idan kika yi yunƙurin lashe musu zuciya kamar yanda kika lashe ta mamansu har ta mutu, to a wannan gaɓar zan yi shari'a da ke. Daga nan har kotun ƙololi ta duniya.
Mayya kawai, mai baƙin naci." Yana gama faɗar haka yaja hannun yaran suna kuka da ɗago mata hannu da kiran sunanta Maama ya tisa ƙeyarsa yana masifa a kan su masa shiru.

   Kamar wadda aka dasa a tsaye a wajen haka ta buɗe baki da ido tana kallonsa, tana jin sautin kukan yaran na amsa Amo a kunnenta kamar zai fasa mata shi. Hawayen da take tunanin ta dakatar da su daga sauƙa a idanuwanta suka samu damar gangarowa da ƙarfin gaske.
   Bata ga laifinsa ba, bata ji haushin kowata kalma daya faɗa mata ba, sai dai abin da take ganin yafi komai ƙona mata rai shine rabata da yaran. Sa shamaki mai girma a tsakaninta da yaran Nabeeha, wannan shine  horo mafi girma da xa a yi mata.

  
🌿🌹🌷🌹🌷
Ƙawata ce! Paid book ne a kan N300 kacal, akwai free pages da za su biyo baya a gaba.
  Ga masu buƙatarsa za su iya turo kuɗin ta wannan accnt 👉3051894647 Hajara Ahmad Hussain polaris Bank. Su tura katin shedar biyansu ta wannan lambar 08030990232 ko +234 703 513 3148 Ga wadda basu da accnt kuma za su iya turo katin waya na mtn ta waɗannan lambobin.
  Ga 'yan Niger kuma za ku iya tura tura carte moov ta 400 zuwa ga number  +227 84 50 64 76

#KWTC
#NWA
#CMNTS, LIKE SHARE,
#GIRMAMAWA
#DABANNE.

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now