https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
ƘAWATA CE! 💕
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
©OUM-NASS
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
FITA TA GOMA SHA UKU
Haɗejia, Jigawa, Nigeria.
"Oh an dai jin kunya wallahi. Girma kuma ya faɗi, wasu mutanen kamar tauraruwa masu wutsiya suke, suna giftawa ta gabanka suna barinka da sharrinsu. Yayin da wasu suke kamar kaska duk inda mai jini yake nan suke lafewa har sai sun tsotse musu jininsu tas."
"Uhmm, in ji mai ciwon haƙori, ai idan ana sallah ba a magana, Yaya Jummai. Wasu zuciyoyinsu kamar ruɓaɓɓen tumatur take, da take tafe da zagwanyewar kamala, da mutuntaka, ta kuma zama abar ƙyama a yayin da aka yi karo da ita. Yo Allah na tuba banda lalacewar ɗan bushiya me ya kai shi gujewa ƙayar magarya."
Dariya Yaya Jummai ta yi, tana girgiza kanta "Kin dai mai miki a jiki da ya ga ana susa ake tuno masa da mikinsa.
Shi yasa da ya ga tabo yake tuna shima yana da ajiyayen tabon nasa."Ammu da ke gefen sashenta tana girka tukunya tana jin duk maganar da suke, ta kuma yi amanna a kan cewar da ita suke. Wannan shine abun da ta so gujewa faruwarsa, ta so dakatar da auren Nabeela tun kafin ta tare gidan.
Amma kuma ihunta sai ya zama bayan hari ne, kasancewar kurarta da ta daɗe da yin kura, ta rasa me yasa jarrabawar rayuwarta ta kasance ta hanyar Nabeela ce, ta kuma rasa samun mutum ɗaya da zai fahimci cewar ba laifinta ba ne, ba a son ranta ba ne Nabela ta zama abin da ta zama a yanzu da kuma a baya.
Tana da haƙuri, tana da kawaici, tana gudun abin da za a ce ita ce ta yi shi. Amma kuma Nabeelanta bata da haƙuri, bata da kawaici, duk kuma abin da za a ce ta yi, koyaushe shine abin da ta ke so take kuma aikata shi.""Sallama alaikum. Sannunku munafukai ana ruwa kuna ƙirgawa, ana ga wata kuna hadari ya rufe. Yanzu ke Laure, ban da lalacewar irin ta ki har yaushe ne kuka yi daɗi da Jummai ɗin da har za ku zauna tare kuna jefa Magana ga Hadiza. Kodayake shi cinikin munafurci saurin amsuwa yake, tururuwa kuwa idan ta so lalacewa sai ta fara fiffike tana tashi sama.
Amma wallahi ku ji da kyau, ku kuma riƙe a ranku cewar, babu wanda ya kuskurewa tsallakewa ƙaddara. Kuma da kuka zauna kuke ta ƙulunfuto da kinibibi irin naku na munafukai, babu abin da zai faru. Mun kai Faɗimatu gidanta, mun kuma barta cikin aminci, babu wani shege ko shegiyar da zai tsallaka siririyar ƙafarsa ya je gidan dan ya wargaza mata rayuwar aurenta.
Idan kuma hassadar ce take ƙara rarakar cikinku, to a banza zaku mutu a turbuɗaku a ƙasa ku rasa amsar tambayoyin da aka muku. Sabod kun mutu da zunuban wasu a kanku." Baba Adamu kenan da zuwansa gidan kenan ya ji maganar da matansa suke yiwa Ammu. Yana kuma ganin yanda take share hawayen da wofintar da maganganun nasu."Yanzu me muka ce? Ba dama mu yi hira sai ya zama munafunci, Babansu. Gaskiya dai ana girmama daɗaɗɗen zama, kuma dai da kake cewa za mu mutu mu rasa amsar tambaya duk mai ya kawo zancen mutuwa fisabillah!" Jummai ta faɗa tana turo bakinta.
"Goɗai-goɗai da mu, da yaranmu da jikokinmu, amma bamu wuce baƙaƙen maganganunka ba, kullum abu ɗaya kamar wutar murhu. Yo ko wutar idan ta mutu ai tana zama toka.""Eh ba shakka, Jummai! Wato goɗai-goɗai da ke kike faɗa min kin wuce ƙarfin faɗa, amma kuma baki wuce na munafunci ba. Tunda gashi har kina kashe hannu da kishiyarki da kike jin kamar ki hura wuta ki afka ta. To ni ba za a yi wannan sakarcin da ni ba. Idan kuma kuka ci gaba, ina mai tabbatar muku za ku tsinci jakarku a waje. Yo ni Allah na tuba banda ma na sha ruwan allo na kwankwaɗi tawada mata har wuya za su min. Wallahi sa'arku ɗaya na yiwa Malam alƙawali amma da tuni na zubar da ku na kwaso wani. Yo malamai nawa ke sakin mata su auro wasu, ai ba kaina farau ba."
Daga haka ya juya yana kallon Ammu da take risinar da kanta ƙasa, tana jin maganarta kamar sauƙar ƙanƙara a zuciyarta.
Harara ya zabga mata yana jin kamar ya doketa a wajen dan takaici "Ke kuma zanga lokacin da zaki sauya. Kullum zafinki da baƙar zuciyarki na sauƙa ne a kan yaran da kika haifa, amma ga 'yan sa'a kamar baƙar doluwar bagidajiya haka kike.
Mtss ai ni wallahi Faɗimatun ta min daidai da bata iyo soloɓuyon rayuwarku ba, ni nasan kwafina ce, abin da kawai ta ƙara ni ban da son zuciya da son abin wani."
Daga haka ya kaɗe babbar rigarsa ya wuce sashen su, har ya shige kuma ya juyo.
"Saura na ji wata matar ta sake cewa wani abu." Ya baza labulen ɗakin nasa ya shige.Harara Jummai ta aikatawa Ammu "Aikin banza. Ku dai rayuwarku a munafurci zata ƙare, da haɗa wani da wani."
Daga haka ta shige sashen nasu, itama dai Lauren miƙewa ta yi ta shige sashenta. Tana jin ƙafafuwanta sun sage sun mata nauyi. Nauyin wankin babban bargon da Baba Adamu ya musu, da kuma kunyar tunatar da ita kowacece Ammu a gareta.*****
Abuja, Nageria.
Dare a kance Mahutar bawa, amma ga Nabeela ya zama tsani na wahalarta, tun da ta shigo ɗakin abubuwa suka cinkushe a kanta, bata ga koda mutum ɗaya da ya damu da kasancewarta a wajen ba.
Babu mijin da yake tutiyar cika alƙawarin da ya ɗauka, ko haushin karnuka nata tsinkayi jinsa ba, balle ta sa rai akwai wani abu da ke raye a duniyar.
Kukan da cikinta ke yi yana kururuwa da nema agaji, ya tunatar da ita adadin shuɗaɗɗun kwanakin da ta ɗauka ba tare da sa abin kirki a cikinta ba. A ganinta na wannan lokacin ya kamata ya nemi agajin ba, domin anan wajen bata ga inda tausayin ya ke ba.
Tasha ji ana cewa amarya ko ta buzuzu ce ana ɗokinta, to amma ita gashi bata samu ko tallafin gani da ido ba, ko magana guda ɗaya bata tsinkayeta a tare da mutumin da ya amsa sunan mijinta ba.
Wannan ba damuwa ba ne a gareta, domin abubuwan da suka fi zama damuwa a gareta suna da yawa, yawan da baki ba zai iya faɗarsa ba.
Miƙewa ta yi tsaye tana zagaya tsakiyar ɗakin, tana dafe da cikinta da ya ƙulle mata tam.
A da bata yin cikekkiyar awa huɗu ba tare da ta kai abu a bakinta ba, saboda bata jumirin yunwa, duk da cin da take da shi, hakan bai hana gyambon ciki kanannaɗe rayuwarta da 'yan hajinta ba.
Zata iya cewa tun haɗuwarsu dw Nabeeha ta nemi wannan ciwon ta rasa. Ta kuma yi bankwana da shi a tare da ita.
Amma kuma yau da alama yana son waiwayowa rayuwarta. Ɗaga kanta ta yi tana kallon agogon da ke saƙale a bangon ɗakin, ƙarfe 2:15am.
Rarrafawa ta yi ta shiga Toilet ta kwankwaɗi ruwa, saboda ta duba firjin da ke ɗakin babu komai a cikinsa.
Ruwan da ta sha ya taimakawa cikinta ƙwarai wajen tasowa, sai dai kuma ba a je ko ina ba ta fara jin cikin nata na murɗa mata, tana jin wani abu na tasowa yana hargutsa tunaninta kafin kuma ta yi wani tunani ta fara kwarara amai.🌹🌷🌹🌷🌷
Ƙawata ce! Paid book ne a kan N300 kacal, akwai free pages da za su biyo baya a gaba.
Ga masu buƙatarsa za su iya turo kuɗin ta wannan accnt 👉3051894647 Hajara Ahmad Hussain polaris Bank. Su tura katin shedar biyansu ta wannan lambar 08030990232 ko +234 703 513 3148 Ga wadda basu da accnt kuma za su iya turo katin waya na mtn ta waɗannan lambobin.
Ga 'yan Niger kuma za ku iya tura tura carte moov ta 400 zuwa ga number +227 84 50 64 76#KWTC
#NWA
#CMNTS, LIKE SHARE,
#GIRMAMAWA
#DABANNE.Oum-Nass
YOU ARE READING
ƘAWATA CE
AcciónLabari ne akan ƙawaye biyu masu halayya ɗaya! Labarin sadaukarwa a inda bata kamata ba! Ƙauna marar algus! Yarda marar iyaka! Aminci marar gudana! Tafiyar hawainiya da rikiɗewarta! Idan kun fara zaku so jin tafiyarsa. "Ita kaɗai ce ƙawar da na tas...