Part 2

949 85 2
                                    



*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

*By Maryamah* 💞💞

©2020


Shaf Guru ya manta da lamarin wata Hamdah harya gama abubuwan da zeyi yai shirin tafiya gida. Mukullin motarsa ya shiga nema Amma yace daukeni inda ka ajiye, wani abokin aikinsa ne ya leka office din jin motsin mutum "Dr ashe kadawo dazu naga fitarka Ina ta daga maka hannu baka ganiba".
Kallonsa yayi da mamaki aransa yana tunanin yaushe ne ma ya fita "So she took my car" ya fada a fili sedai instead yaji haushi se kawai yaji ta birgeshi kawae, gaskiya tana da liver shi kuma yana son mutum mara tsoro.
Wayarsa yadauka kawai yakira drivernsa akan yazo yadaukeshi aransa yace "let see if she will return it".
Hamdah kuwa Akan kwanar layinsu suka hadu da Mumcy data gaji da zaman jiranta "su Hamdah kuma yau wa aka tsokano Nidai babu ruwana wlh karma ki lossafani cikin rigimarki. Me tsaya miki kiyi rashin jin baya nan ga kuma yayanku can Baffa yazo".

Baki ta cuna takarawa motar wuta aranta tana cewa "ita Mumcy kullum nice mara gaskiya bayan batasan me mutuminnan Dan rainin hankali Yayi min ba ai dai shiya fara tsokanata" koda ta isa gidan guri me kyau ta samarwa motar ta ajiye sannan ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo gidan seya kalli motar dan dae sunsan babu me irinta a gidan, sanin Hali yasa Babu Wanda yabi takan ta bare motar da ta shigo da ita Dan in da sabo Halin Hamdah ne tada zaune tsaye.

Seda aka Kwana biyu a tsakani Yah Baffa ya tasata agaba da tambayar Inda ta samo mota. Rasa abin ce mata yayi illa Kallon ta kawae da yake, amsar da tabashi tayi bala'in daure masa kai Wae "Motar Malamin muce"
"Shine yabaki aro ko yaya?"
"Aa"
"Se akayi yaya?"
Tiryan tiryan ta labarta masa yanda abin ya faru Tundaga farko.
"kyaci ubanki ranar da kika dauko fadan dazesa adaureki shashasha me kalar salahai se masifar fitina azuciya".
Cuna baki tayi abinda yazame mata jiki tana kunkuni "Mutum kullum bashida aiki seyiwa mutane fada wae ma meya kawo shi gidan oho".
"Ki fada afili mana karamar mara kunya wlh duk Abbah ne ya lalataki inba haka ba tsabar tsaurin ido kidaukowa mutum mota". ita dai ko ajikinta Dan ko ba komai ta koyawa guru hankali" ya taka da kafa ko ya hau lift" ta fada a zuciyarta. Ranar baccin ta tayi harda minshari cike da kwanciyar hankali. Washe garin ranar kasan cewar bata da lecture yasa ta wuni a gida, ido kawai Mumcy ta zuba mata tun tana jiran taga anzo daukar mota har dare yayi taji shiru, gajiya tayi ta tambayeta "Wai Hamdah yaushe zaki mayar musu da motarsu ne?"
"In mayar ko suzo su karba?" tabawa Mumcy amsa hakan yasa takama bakinta tayi shiru aranta ko addu'a take Allah ya kawo Abubakar a gobe juma'a Dan shi kadai ke taka mata birki kan duk iskancin da takeyi. fatanta Allah ya shirya mata Hamdahnta Dan fitinar yarinyar tayi yawa kwata kwata bata da tsoro.

Ranar Monday 8:00am tai mata a class Dan bata so tabar wata kofa da abu ze hadasu bare ya wulakantata tunda Akwai jikakkiya a tsakaninsu. kamar kullum be kara ko minti daya ba yashiga ajin, idonsa akan ta yafara sauka yadan kalleta for some seconds Wanda har mayun yammata masu kallonsa suka hankalta da inda yake kallo nan fa kishin Hamdan ya kamasu Dan asaninsu babu wata mace data ishi Guru kallo Amma se gashi yana kallon wannan fitsararriyar yarinyar da bata ganin kan kowa da gashi.
Ammani Kaman yanda suke kiranta zan iya cewa babu Wanda besantaba afadin BUK both new nd old site. Kasancewarta kyakykyawar mace ajin farko. Fara ce tas koma mu kirata yellow Dan hasken Hamdah har kashe ido yake.bata da tsaho can haka ba gajeriya bace tana dai tsakiya haka girman jikinta sam bata da kiba Amma Allah ya mata kira mai kyau domin saman ta da kasan ta acike yake dam. Babbab abinda ke daukar hankalin Maza akan ta shine kalar kwayar idonta data kasance Grey colour da wani irin sparks Kaman na gold dole in ka kalleta kasake kallo gata da shiru shiru a fuska. Kyanta ya tarar da gayu dukda Hamdah bata kwalliya a fuska amma tana shiga ta burgewa da komai hassadarka dole ta burgeka dan kusan duk wani abin gayu ko kyalekyale na mata a kaf campus din a wurinta ake fara koya. Mutane da dama nayi mata kallon me girman kai kodan rashin shiga sabgar mutane da batayi sefa wadanda suka Santa ko wadanda suke good time ba. ZAHIRIN HAMDAH kenan
A badini kuwa sunan da Ake kiranta a gida shine Fitilar sharri Dan Idan kanason siyan balai da kudinka to ka takali Hamdah. Bata da tsoro ko kadan sannan bata san wani abu rufa rufa ba. Gaba gadi take komai nata. Tana tsananin son abinda take so hakanan tana tsananta kiyayyah ga abinda bata so hakanan bata da Wuyar sabo ko kadan in har jininku ya hadu.Wannan itace HAMDAH AHMAD AMMANI a takaice.
Awa biyu (2hrs) lecture ta daukesu Kaman kullum bayan yagama ya basu short gun test tareda Assignment. Sit by sit yake bi yana tattara takaddun "Meet me in my office" kunnanta yajiyo mata dai-dai lokacin da yazare ta ta takardar Wanda kafin ta dago har ya wuce illah kamshin turarensa dana mouth fresh dinsa daya barmata. Da harara tabi bayansa ta murguda baki sannan tace "se kazo ka daukeni ae kamar wata yarka kana commanding dina" kasa kasa tayi maganar dan ko Afeeya dake kusa da ita be zama lallai taji me tace ba amma yanda yake watching moves dinta bakinta kawae ya kalla ya gane abinda tafada tsaf, se yai murmushi, da ido ya mata alama da "karkizo zakiga abinda zanyi". Yana fita kuwa ta dane kan desk tana tsarawa kawayenta irin dinki da shigar da zasuyi ranar Dinner Aysha.
Agogo ya kalla for the second time kimanin 1hour kenan da barinsa class din. bayan fitarsa sarai yasan basuda wata lecture Dan haka yayi qwafa sannan ya miki ya nufin ajin, Clique members dinta ne zaune Dukkansu Maza da Mata sun zagayeta Banda dariya Babu abinda sukeyi. Labarin wani Bayeraben Professor Abokin Aikin Abbanta a University take basu Dayake sonta. yanda take kwatanta fuskar mutumin Wai dayaga picture dinta seka rantse da Allah tana gurin "I'm telling you Prof Balogun yafi mutuminnan kyau kai A swear ko Obasanjo albarka munin mutuminnan ze iya saka meciki tayi miscarriage Wae shi be yadda ba sona yakeyi" yanda take exergirating Abun ne yake qara basu dariya Shigowarsa tasa kasu yin shiru Dif kaman ruwa ya cinyesu banda Oga Hamda dake kokarin nemo picture din Prof Monkey Tana ci gaba da cewa "wae fa da Abba ya hadamu a waya mugaisa harda wani Babe yake cemin niko dariya nake kaman kaina ya kwance..." daga kanta tayi da niyyar mika musu wayar su gani se ganin mutum tayi akanta kamar gunki. "Ke wato bakiji me nace miki ba ko".
Seka rantse bashi yayi maganar ba. Dukda yanda zuciyarta ke bugu hakan be hanata dauke kai tayi Kaman ba ta jishi ba. "Wai bada ke nake magana ba ne ehe".. "Toh ai ganinayi sunana HAMDAH ba keba.......Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata da ta sakata kasa qarasa abinda tayi niyyar fada "I give just 2 minutes to come to my office if not (ya murda hannunsa) wlh nida ke ne yau a makarantar nan".
Sosai ta tsorata, zata iya cewa ba'a taba mata tsawa kamar haka ba. Babu shiri Ta mike jikinta na rawa tabi bayansa. A tare suka shiga office Din Dan har suna kusan cin karo. Kallonta kawae yakeyi Wanda har seda ta tsargu. Seyanzu ya gano zallar yarinta a tareda ita in ya rantse beyi karyaba bazata haura shekaru 17 zuwa 18 ba.
"How old are you?"
Kallonsa kawai tayi irin karaina min hankali tareda dauke kai.
"I'm I not talking to you?"
Ya fada cike da hargagi Dan yarinyar tafara kaishi bango." I'm 17" ta bashi amsa. Hawaye na taruwa a idonta. "No wonder she is like this dan mutum me cikakken hankali bazeyi abinda takeyiba" ya raya hakan a zuciyarsa.
"And what about my car?"
"Ur car?"
"Yes or u want to fool me again"
"Oh sorry tana gida you can come and carry it when you are ready".
Dukka idonsa ya bude akanta yana kallonta gaba daya ta dinke masa kwakwalwa in banda Hmmm babu abinda ya iya cewa kafin ya nemi guri ya zauna. "Saboda ni na kaita Gidan naku?" dakyar ya furta maganar yana relaxing akan kujerar sa. Bata amsa ba daman be saka rai da zata amasa masa ba dan haka ya ci gaba "return it to where you took it inkinga dama kuma ko ki rike Danni ba tsiyar mota nakeyiba". Yana kaiwa nan ya Shiga tattara system dinsa da wasu takaddu yayi waje ya barta a tsaye a wurin yana jin lokacin data fashe da kukan daya fi kama dana takaici. "Kudos" ya fada yana murmushi ko ba komai tayi kuka ya rama abinda tayi masa.
Ina wuta HAMDAH ta jefa GURU, kuka Take kamar wadda ya daka, wato itace take tsiyar mota? Ai dai ya gani ba a kasa take yawo ba bare ya gaya mata wannan maganar. Su Maryam dake tsaye a waje suna saurarinsu tsab sukayi saurin shiga bayan fitar sa. Dakyar suka lallasheta "kinga abinda nake gaya miki ko gashinan yanzu kinja ya gaya miki magana kuma kiyi addu'a tunda yayi marking face dinki Allah ya raba ku kawae. Gida tawuce Dan batajin zata iya saurarar wata lecture again Wanda ko a gidan bawanda ya kulata illah khaleefa daya bita ya karbi key din motar Guru don ya cire Battery gudun samun matsala Dan wannan bashine karo na farko ba datayo awon gaba da motar mutane sedai babu wacce ta taba kwana. Tundaga wannan rana bata qara bari koda ido sun hada dashi ba, ko lecture yake zata kifa kanta a desk ne daya fahimci haka shima se ya tattarata ya watsar dan tana nema ta ja masa raini a gurin sauran Daliban ajin.
©️2⃣0⃣2⃣0⃣

RUBUTACCIYAR QADDARAHWhere stories live. Discover now