Part 46

739 43 0
                                    

RUBUTACCIYAR QADDARAH

*By Maryamah* 💞💞

©2020

*PAGE* 4⃣6⃣

Abdul'ahad
Hannaye biyu yasa ya dafe kansa kafin ya miqe duk da jirin dake neman kadashi. Yana jin yanda take rusa kuka a wayar tana maimaita ta shiga uku ta lalace, seya kalli Fahad dake tambayarsa ina zashi ya masa alamar yana zuwa. Can gefe in da babu kowa nesa da yan karbar gaisuwar ya samu ya zauna kansa yana sara masa ba kadan ba. Idanunsa da suka masa nauyi a lumshe yana jinta har lokacin bata bar kukan ba. Gajiya yayi kuma bata da alamun yin shiru yasa ya bude baki yace

"Naji amma ke kadai kika shiga ukun yanzu dai meya faru keda baki da aikinyi se tayarwa da mutane hankali" yayi maganar a nutse cikin kwantaccen sauti, seta dakata da kukan kamar anyi ruwa an dauke. Lallai ma wannan yaci uwar rainin wayo wato ita kadai ta shiga uku? Ai kuwa ya tabowa kansa ya hadu da kwalba uwar sharri, seta sa hannunta ta goge hawayen da suke zubo mata tace

"Ni na shiga uku ni kadai ko, ok nayarda amma ka sani taka na zuwa ranar dana haife Dan shegenka na kawo shi gidan ku inda ake maka kallon mutumin kirki gurin matar taka daka tafi gurinta ka barni, ranar ni da kai se muga wanda ya shiga uku, koda yake tsaya bazan yi haka ba, kenan ma na qulla  alaqa dakai tunda mun hada iri, bari kawai zan zubar dashi se nazo na musu bayanin irin zaman da mukayi nidakai a London, mtsw kashe wayar tare dayin jifa da ita a bango ta kuwa tarwatse nan take. Safa da marwa ta shigayi cikin dakin, ko kadan ita bata jiyo rauni da kuma damuwar da take a cikin muryarsa ba sema Izza da taqama kawai zuciyarta ta kitsa mata. Wato ya shanye mangwaro ya yada kwallonsa ko? Ya gudu ya barta to wallahi yayi kadan. Bazata daukarwa kanta zunubi biyu ba gana Zina gana kisan kai kuma Bazata fuskanci wannan abin kunyar ita kadai ba, zata raini cikin nan kawai ta haifeshi duk duniyar da yake seta iske shi ta kai masa daga nan ta yanke duk wata alaqa dake tsakaninta dashi. Ta yanda baze sameta ba bare ma ya liqa mata dan. Seta sake fashewa da wani kukan, ta yaya zata raini ciki har wata tara ta haife ba tare da wani ya sani ba? Kodai gurin zama zata canza ita yanzu tacewa su Zulaiha me? Anya bazata bar London ba ta koma wata qasar ta yanke communication da kowa har se randa ta haihu?

'Idan kika gujewa mutane ubangijinki kuma dayake kallonki a ko ina ya zakiyi dashi, zaki iya boye laifinki a idon mutane amma a gurin Allah fa?? Kenan ma kin zabi jin kunyar lahira akan ta duniya kenan?" Zuciyarta ce ta lissafo mata wadannan tunannen, seta durqushe a gurin tareda sakin sabon kuka me cike da dana sani da Nadamar da bata da amfani a cewarta. Shedan ya rudeta takai kanta ta baro. Dama wannan itace illar zaman mace ita kadai da mutane da yawa suka kasa fuskanta, iyaye suke daukar yayansu mata ko maza su kaisu wata uwa duniya su samar musu da duk wani jin dadi da sunan karatu basu san me hakan ze iya janyowa ba. Bazata ce duka ba amma ita kanta yanzu misali ce, nata iyayen sun yarda da ita a matsayinta na bazawara sun turata har London karatu ta zauna ita daya ba qarqashin kowa ba yanzu ga sakamakon data yo musu, ta biyewa so ta cuci kanta dan ba iyayenta ta cuta ba.

"Allah sarki Abbah, Mumy ku yafemin I failed you, i break ur trust i know you won't be able to forgive me for this"  kalaman Abba na nasiha da yake mata kullum akan kamun kai ta tuna. Maganar sa kenan ta tsare mutuncinta kar taganta inda bata da kowa ta canza daga Hamdar sa zuwa wata daban gashi yanzu ta masa babban tukuici da cikin shege, Aman daya taso mata ne ya tsaida tunanin da kukan, nan ta shiga sheqashi babu ji babu gani. Ta jigata kwarai jikinta yayi laushi seta kwanata a gurin kawai tana maida numfashi tareda kiran sunan Allah tasan shi kadai ze kawo mata dauki a wannan lokacin, inama ta mutu kawai ta huta da wanna abin kunyar...

Nigeria

Wayar ya cire daga kunnensa ya kalla nan ya tabbatar da tayi hanging. "Idan na haife maka dan SHEGE na kawowa matar taka da ka tafi gurinta ka barni ranar se muga wane ya shiga uku tsakanina dakai" kalaman suke masa yawo akai, "SHEGE" ya qara maimaita kalmar, could it be ciki ne da ita?? Seya miqe kamar wanda aka ma allura ya shiga neman number ta, idan har da gaske ne dole ya taka mata burki, tsaf yasan Hamdah tana iya masa ganganci da ciki dole ya nutsar da ita ta koma taitayinta. Tsabar yanda ya rude bema gane wayar a kashe take a keta gaya masa ba seda ya kira kusan sau goma sannan ya gane. Jifa yai da wayar daidai lokacin da Fahad ya qaraso yai nasarar cafketa dan tun dazu yake lura da yanda yake ta zarya shi kadai.

RUBUTACCIYAR QADDARAHHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin