RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*By Maryamah* 💞💞©2020
*PAGE* 3⃣2⃣
Karfe 4 na yammacin ranar Alhamis tayiwa Ni'ima a gidansu Hamdah kamar yanda sukayi alkawari. Halinda mijinta kuma yayanta ya shiga a jiya shi ya qara qarfafa mata gwuiwa akan abinda take da niyyar yi. Ita da kanwarta Safeena sukaje wadda batasan menene sukaje yi ba ta dai ce kawai tazo ta rakata gidansu wata friend dinta suka bar little Hamdah acan gidan nasu.
Tana zaune ana mata baqin Lalle bayan tacire Ja dayayi bala'in yiwa Fatarta kyau a daya daga cikin dakunan BQ saboda cikin gidan ya fara cika da Jama'a yan biki kamar ba bikin bazawara ba. wayarta ce ta dauki qara, me lallen ce ta daga tareda saka mata wayar a speaker. Bayan sun gaisa ne take shaida mata gata a gate dan haka ta tura Amrah ta shigo da ita.
Ko kadan batayi tsammanin ita bace har fuskarta ta kasa boye mamakin, guri suka samu suka zauna Safeena da bata da baqunta tashi ga zuzutun lallen da ake mata
"Kai amma yayi kyau sosai se kace Amarya" ita dai Hamdah Murmushi kawai tayi a zuciyarta tana tunanin meya kawo wannan matar kuma. Dambun naman da akayi na gara da soft drinks ta saka aka kawo musu har lokacin Ni'ima batayi magana ba saboda ganin me lallen da kuma Inteesar Matar Yaya Baffa da ita ma aka saka mata lallen.
"Kiyi hakuri kinzo kuma ina dan uzuri i thought i will finish before the time i gave you but unfortunately kuma na zarta". Murmushi Ni'ima ta mayar mata kafin tace
"Ba komai zan iya jira dukda ina dan sauri nabar yarinya a gida".
" Ba matsala we can talk here ai" hamdah ta fada ganin Ni'ima na kalle kalle. Dukda abin be mata ba, she wanted them to have some privacy suyi magana ta fahimtar Juna amma tasan in tace seta jira har an gama zata bata lokaci. Little zata iyayin kuka and shi kansa ze iya kiranta at any time ta dawo gida dan haka tacewa Safeena ta fita waje dan bata so taji maganar da zatayi, tasan ta da surutu zata iya zuwa ta gayawa Mamansu da sauran Sisters dinta, tana qunquni tana komi ta fita dan ita lallen ma taso ayi mata.
Bayan Safeena ta fita ne ta koma kusada Hamdah ta zauna suna fuskantar juna, kallon inda Inteesar take ta sakeyi dan batajin ta me lallen sosai kilan yayarta ce dayar ko kuma ita ce Amaryar da ake bikin.
"Karki damu feel free to talk we are all family" Hamdah ta fada tana mata murmushin karin qarfin guiwa. Seda ta yi shiru for some moment sannan ta fara magana
"Hamdah nasan zakiyi mamakin ganina and you will ask your self on what is so important that i want to discuss with you" se ta danyi shiru kadan. Hamdah data tattara hankalinta gaba daya akanta tace
"Yes ina jinki"
"To cut it short Hamdah mijina nazo nemawa auranki". Ba Hamdah ba hatta me lalle seda ta saki kwarkwaronta tsabar mamaki karma Inteesar taji labari abinka da Yar jarida seta yi saurin qarasa sabule lallen da takeyi ta matso kusa sosai kodai kunnenta ne bejiyo mata daidai ba. In between dariya Hamdah tace
"You must be kidding wane mijin naki kika zo nemawa auran wa?"
Seta gyara zamanta cikin son nuna mata da Gaske ta keyi tace
"You know who I'm talking about, amma tunda ta haka kika biyo muje a baki sanshi ba Ni Ni'ima nazo Nemawa Mijina Abdul'ahad auranki ke Hamdah".
Seta dakata kadan tana kallonta sosai, lallai matar nan ta samu matsala in ba haka ba ita zata zo nema ma mijin nata ma aure? se kawai ta daure fuska dan abin ma yafi kama da rainin hankali, dakatar da me lallen da mamaki ya hanata ci gaba tayi ta gyara zamanta sosai sannan tace
" Shine ya aiko ki?" Ta tambayeta cikin tsare gida alamar babu wasa. Seta girgiza kanta
"Ba shi ya aiko ni ba nina aiko kaina sabida naga hakan....."
"Dakata malama, be it shi ya aiko ki ko ke kika aiko kanki ki koma I'm not interested in your Goddam Husband inda nasan ke ce da tun farko ban answer wayarki ba" Hamdah tayi maganar cikin dacin rai wanda a qarqashin zuciyarta wata wutar kishi ce take ci. Tun asalin Hamdah me zafin kishi ce bare a yanzu kuma akan abinda take so.
"Ki tsaya mu fahimci juna Hamdah dan Allah, Yaya Abdul'ahad loves you so much. Dukkan shekarunnan hankalinsa da tunaninsa yana kanki, Hamdah aure kawai nake amma bansan menene soyayyar miji ba, mijina ke yake so ke kadai yake kallo a matsayin mace". Shiru ne ya ratsa palour, ita Ni'ima tayi shiru ne sakamakon wani abu da taji yana taso mata me daci irin yanda takeji duk lokacin da ta tuna mutumin data fi so akan komai da kowa wata yake so daban, ita kuwa Hamdah jikinta ne yayi sanyi qalau da kalaman Ni'iman. Me lalle da Inteesar kuwa sunzama hoto kowa ta bude baki tana sauraron ikon Allah to da alama wannan matar bata san meyake faruwa ba.
"Hamdah ki taimaki ne ki auri mijina muna buqatar ki a cikin rayuwarmu auransa ne kadai zesa nima nasamu farin ciki kamar kowacce yantacciyar Mace. Hamdah hatta Yata tafi so da dokin ganinki sama da kowa a duniyar nan, kinsan meyasa? Saboda da sunanki ta fara koyon magana. Hotonki yazamar mata kamar ibadah a kullum shi take fara kallo har ta fahimci shi kadai ne abinda yake saka Babanta farin ciki. Hamdah kinga irin murnar da tayi ranar data ganki as small as she is 3years amma ta iya gane abinda take gani a hoto tun daga ranar kullum kukanta a kawo ta gurin Namesake bata a sauran magana se taki ko dan ita bazaki taimaka ki aureshi ba".
Tuni hawaye sun gama wanke mata fuska. Duk wata kalma da take fada jinta take kamar tana tsirawa kanta allura amma yaya zatayi? Bata so ta zama meson kai bakuma taso ta raba wannan soyayyar, Kifa kanta tayi akan cinyarta tana ci gaba da kukan dukda tasan abinda hakan ze iya haifar mata.
Tausayinta ne ya shafe haushin daga zuciyar Hamdah, wannan wace irin mace ce da zata iya sadaukar da Mijinta, mijin ma irin Abdul'ahad alfaharin kowacce mace. Se ta zamo daga kan kujerar da take, bata damu da lallen Hannunta ba ta qarasa ta dagota tareda rungumeta itama tana zubar da Hawaye.
" Ni'ima kodan wannan sadaukarwar da kikayi bazan iya auran sa. Taya ma kike zaton zan iya qara kallonki bayan na aurar miki miji? Nasani son da kike masa ne yasa har kike qoqarin nema masa nasa farin cikin koda yaci karo da naki amma ni bazan so kaina ba, Naso Abdul'ahad ada amma na haqura dashi daga lokacin dana ganki a cikin rayuwarsa. Bazan iya shiga na rusa muku ginin da kuka faro ba......" Seta yi saurin rufe mata baki tana cewa
"Aa karkice haka ke din kece cikon farin cikin gidan mu. Our home is incomplete without you, we been living a sorrowful life, ki taimaka ki kawo farin ciki a tsakaninmu we want you in our life" Tayi maganar tana qara qanqameta.
Seta janye jikinta a hankali ta koma kan kujerar zuciyarta na mata wasi wasi kala kala. Meya kamata tayi? Shin ta amince da buqatar Ni'ima ko yaya?
"Wannan matar bata cancanci haka ba Hamdah, tsaya ma wa kike tunanin ze dakatar da wannan auran amma dae ba Abba na ko?" Zuciyarta ta tambayeta.
Inteesar data kai qololuwa a mamaki ta sauke numfashi tana kallon Ni'ima da ta dena kukan se ajiyar zuciya takeyi tace
"Sannu da qoqari yar uwa gaskiya gobe dole inyi publishing labarinki Jarumar mace tazo nemawa mijinta aure amma sedai anyi rashin sa'a kin makara dan wani ya rigaku zuwa".
Seta kalleta sosai dason jin qarin bayani.
"Kwarai kuwa da alama baki san gobe ne daurin auranta ba wannan qunshin ma da kikaga ina mata na biki ne gobe iyanzu mun kaita Garin Gwamna insha Allahu" Indo me lallece ta qarasa mata bayanin ganin kamar bata gane me Intee take fada mata ba.
Seta bude baki da alamar mamaki take binta da kallo, kai ta gyada mata cikin tabbatarwa kafin ta nemo Invitation card din daurin auran a wayarta wanda harda picture dinta dana Abdurrahman din a gefe ta miqa mata jiki na rawa ta karba ta duba.
"Ubangiji Allah yasa hakan shi yafi alkahiri idan kuma akwai sauran dama muna nan bamu hakura ba" Ni'ima ta fada bayan data miqa mata wayar dan ta tabbatar babu sauran wani abu ayanzu kuma ya qara makara kar na wancan lokacin. Jakarta ta dauka ta miqe da kyar saboda nauyin da taji kafafuwanta sunyi mata daidai da shigowar Safeena da ta gaji da jira a waje, saurin tareta tayi tana tambayarta lafiya
"Mutafi gida bana jin dadi Safeena" nan da nan hankalinta ya tashi dan ko kadan basa son abinda ze jawo motsawar jikin yayar tata. Kamata tayi suka fita bayan sunyi musu sallama tana ta mita wai ta zauna tana ta magana gashinan ta jawo wa kanta wahala ita dai bata ce mata ta tafasa ba tunani takeyi kawai a zuciyarta Halinda Abdul'ahad ze iya shiga. Rabonta dashi tun jiya a bakin Fadila taji wai ya dawo a dakin Ammi ya kwana tun daga nan tasan babu lafiya. Koda safe waya yayi mata takai masa kaya yayi wanka acan ya fita bata da tabbacin ina ya tafi ko ya dawo gidan yanzu. Wani irin sharp pain taji tundaga kafarta har maqoshinta se tayi saurin riqo hannun Safeena dake tuqi tana ci gaba da Mita
"Safeena mu wuce hospital please its getting worse" cikin karfin hali tayi maganar dan haka Safeena tayi saurin chanza wa motar direction. Kafin suje asibitin ta gama galabaita dan har ta fara aman Jini ga jikinta da yayi wani mugun zafi kamar an anjona heater. Kuka Safeena take kamar me lokacin da aka shiga da ita ICU ta shiga kiran number Mamansu amma busy, Abdul'ahad ta kira akayi sa'a yana kusa da gurin dan haka ba shiri ya tafi asibitin.
Hankalinsa yakai kololuwa gurin tashi ganin yanayin da take ciki, likitoci uku ne akanta suna qoqarin ceto rayuwarta to wai ma meya sameta of sudden haka? Matar da suka rabu lafiya dazu babu wani alamar ciwo a tare da ita.
"Daga ina kuke" ya jefawa Safeena dake kuka hannuwanta dukka biyu aka tambaya.
"Nima ban sani ba Yaya kawai cewa tayi nazo na rakata gidansu wata friend dinta da mukaje ma korata waje tayi sukayi magana shikenan fa da muka taho tace na kawota asibiti bata jin dadi".
Safa da marwa ya shigayi, wace qawarta taje gidansu da bata gaya masa ba? A kwanakin nan he is suspecting that she is up to something amma koma mene ba wannan bane damuwarsa a yanzu, samun lafiyarta shi ne first priority dinsa daga nan se yaji koma mene a bakinta. Yafi awa daya a gurin sannan yan gidansu suka qaraso harda Amminsa da qanwar tata Maman Ni'ima ta kira ta sanar da ita. Haka suka zauna jigum jigum kowa da kalar tunaninsa fatansu kawai Allah ya tashi kafadunta. Se mu tayasu a Amin.
****************
A bangaren Hamdah duk yanda su Inteesar suka so suyi maganar qi tayi qarshe ma tace musu tana so maganar ta zama sirri bata yarda su gayawa kowa zuwan Ni'ima ba, sukuku aka gama lallen ta wanke ta koma main house din anan ta tarar da mutanen da suka taru. Daurewa tayi aka shiga gaisawa kowa yana mata Allah sanya alkhairi da fatan zaman lafiya ta ringa amsa musu da Amin tana murmushin da bekai zuciya ba.
Dakinta tashiga tayi wanka bayan ta fito tana zaune agan dressing mirror, wayarta ce a hannunta tana jujjuyawa tunani take ta kirashi ko Aa? Zuciyarta ce tafi tafiya akan ta kirashin ko ba komai tana so taji dalilin dayasa ya turo mata matarsa. Seda tayi masa 5 missed calls be amsa ba lokacin yana can ana dibar jininsa wanda za'a qarawa Ni'ima da suka ce volume na jininta yayi qasa sosai.
Tsaki tayi tareda jefar da wayar akan gado, dan rainin wayo ita zata kirshi ma yaqi answer wa to yayiwa kansa haka ta ringa mita har ta gama shiryawa ta shiga sabgoginta. Har dare tana sauraron ko ze kirata, lokacin da agogo ya buga karfe shabiyu daidai ta cire rai takuma tabbata baze kirata ba a wannan lokacin ma. Seta tuna waccen ranar data ringa jiran kiransa irin haka wanda shi ya bata qarfin guiwar yanke decision dinta a wancan lokacin, yau ma ya qara tabbatar mata baya buqatar ta a cikin rayuwarsa. Ya tabbatar mata daya rabu da ita a karo na biyu, se kawai ta fashe da kuka, kukan da bata san dalilin yinsa ba.
ESTÁS LEYENDO
RUBUTACCIYAR QADDARAH
RomanceStory of two lovers Hamdah and Abdul'ahad who were blindly in love but didn't realize until it was too late for them, yes they are meant to be together but destiny keep them apart..