Part 36

543 49 0
                                    

RUBUTACCIYAR QADDARAH

*By Maryamah* 💞💞

©2020

*PAGE* 3⃣6⃣



Cikin Ikon Allah da ana so da ba'a so Cikin Hamdah dai yashiga wata na biyar kuma zuwa yanzu ta samu saukin laulayi se dan abinda ba'a rasa ba. Tayi kyau kwarai haka cikin yai mata kyau ga jikinta daya qara murje wa har wani kyalli take yi. Yanzu kam Tsakaninta da Abdurrahman sedai kallo Dan gaba daya ya fita harkarta kwatakwata anata bangaren ita hakan ma yayi mata dadi dan har mantawa takeyi da zamansa a gidan in dai ba haduwa sukayi ba yaringa kallonta kuwa kenan yana hadiyar yawu tareda hararar cikin dayai girma kai bakace wata biyar ne ba, ita dai sedai tace "nan gani nan bari wannan ciki se na haifeshi ya shaqi iskar duniya daga nan nasan inda dare yaimin Dan dama zamansa nakeyi, banzo da ciki ba bakuwa zan koma gida in raine shi ba" Abdurrahman kam baya tankata sedai yayi murmushi Dan shi kadai yasan abinda yake kullawa zuciyarsa dan bafa wai ya haqura bane, shifa bakin da Hajiyarsa tace zata masa akan cikin ne fa yasa ya daga qafa amma jira yake ta manta ya aiwatar da nufinsa.

Tsakanin Dan Adam da zuciyar sa se Allah ana haka a farkon watanta na bakwai a gidan kuna cikinta ya shiga wata shida wata rana tana zaune ya sameta fuska cike da nadama akan abinda ya aikata, cikin lafuza masu taushi ya ringa bata haquri yana cewa

"kiyi hakuri Wife wallahi sharrin shaidan ne, dazu ina office naji wani wa'azi da wani malami yayi akan falalar rainon Yaya nima naji ina kwadayin ladan yanzu nayi nazari na gane cewa baiwa ce babba Allah yai mana kuma nagano Gaskiya kiyafemin ina son abi da yake cikin ki zamu raineshi tare insha Allah" haka yayi ta lallabata. Dukda dokin zuciyar data hau da irin tarin haushinsa datake ji akace zuciya bata da qashi sai gashi ta sakko ta kuma yarda musamman yanda ya marairaice yana mata rantsuwa akan ya tuba, nan da nan suka koma normal komai ya wuce tamkar babu wani abu daya taba shiga tsakaninsu. Yanda yake bata kulawa kuwa abin se ya baka mamaki, seda ya tabbatar ya wanke duk wani laifinsa a idon kowa dan har Kano ya dauketa suka je bayan sun dawo ya shiga nema musu Visa akan Dubai zasu tafi acan zata qarasa rainon cikin har ta haihu. Idan ya fita kuwa komai ya gani naci ko wanda ya shafi kayan jarirai seya siyo ya kawo mata.

Akace kishi kumallon mata nan da nan se Shaidan ya shiga zuciyar Hajara yake kitsa mata cewa abinda take gudu ya faru Hamdah ta kwace mata miji tunda gashi tun ba'a je ko Ina ba hankalinsa duka ya koma kan ta Ina ga ta haihu ai ita tata ta kare a gidan, seta chanza mata gaba daya, yar hirar da suka saba da girkin datake kawo mata duk ta dena. Datayi mata magana seta ce yanzu ai taga tana da me debe mata kewa shiyasa ta ja baya ta basu fili suci soyayyarsu da tsinke, murmushi kawai Hamdah tayi bayan dataji wannan furucin nata tasan kishi ne zallah yake damunta dan haka bataga laifinta ba ita ma setayi baya da ita kawai tunda wanda ya hada ya raba.

Wata ranar Tuesday da safe tana zaune Abbah yaje gidanta. Wannan shine Karo na farko tun auranta gidan Abdulmalik daya kaita da kansa be qara zuwa ba sefa ranar da Abdulmalik din ya rasu se yau kwatsam gashi a Kaduna gidanta. Ranar har kuka seda tayi dan dadi ganin mahaifin nata haka tashiga masa hidima duk abinda hannunta yakai kai seta dakko masa ta ajiye har seda ya gaji yana ta murmushi zuciyarsa fal farin ciki ganin ta kwantar da hankalinta. Sun dade suna hira, sosai ya kara mata nasiha akan dai hakuri sannan ya dan taba duk abubuwan data masa dan zama tayi zatayi kuka wai seya ci komai haka ya dinga yafitarsu kadan kadan yana ci. Se yamma ya tafi yabarta da tulin tsaraba da kuma kewarsa.

A yanzu bata da wata damuwa tunda ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa a gidan auranta. Cikinta Dan kimanin wata bakwai ya fito yayi girma sosai a jikinta kamar wani wata tara yai bala'in yi mata kyau. Kamar kullum tana zaune acikin falonta sanye take da doguwar riga dinkin kasar Oman blue wadda ta bude sosai daga kasa hakan yasa bata takura ta ba, kankarar madara ce tuli a gabanta wadda Yusra kanwar Abdurrahman tayomata take ta faman dirka dadi da sanyin madarar ya dauke mata hankali har bataji sallamar da Abdurrahman yake ta famanyi ba seda ya janye kwanon Qanqarar sannan ta dago kanta a shagwabe tana jifansa da wani kallo. Murmushi me kyau  yake mata yana qare mata kallo a ransa yace
"God I love this girl amma tayi fuck up ko wa yace mata seka haihu kake samun farinciki a rayuwa oho" seya zauna a kusa da ita bayan ya janye kwanon yana dubawa

"Sannu madam me kika samu haka babu tayi?" Ya fada yana kai hannunsa kan qanqarar, seyayi saurin daukewa yana harararta cikin wasa kafin yace

"Wato sanyin dana hanaki sha ne ko". Seda ta cire katuwar kankarar da ta tura abaki tana cije hakori saboda yanda sukayi sanyi sannan tace
"kankarar madara ce fa kawai nagani a gidan Yusra shine ta aikomin da ita dazu"

"Bana hana ba Banyarda ba salon ki sa yarona yazo da mura ko to ba dani ba karna qara ganin irinta a gidan nan ita dai data qulla qawance da asibiti tayi tayi kina kallo dukka yaranta Pneumonia ne dasu" ya karasa yana kwashe qanqarar ya zuba a cikin wata baqar leda daya gani a gurin. Kukan shagwaba dake kara narkar dashi ta shiga yi masa tana cewa

"yanzu fisabilillahi Dan bakasan zafin da ciki na yakeyiba ka hanani shan ice cream yanzu kankarar ma ka kwace".
" An zo gurin" ya fada a zuciyarsa sanda wani tunani ya bullo masa sharp sharp, a fili kuwa se yace

"To yi hakuri indae Ice cream ne zan kawo miki roba daya dai amma ba da yawa ba kin yarda" kai ta daga masa alamar ta yarda da haka ya samu tabar shan kankarar. Ya kwashe dukka ya fita da ita sannan ya dawo suka ci gaba da hira yana mammatsa mata kafafuwanta da suka kumbura sosai, wani lokacin yakan tausaya mata ganin yanda cikin duk ya chanza ta lokaci daya duk ta kumbura dukda se yaga kamar kyau ma take qarawa. Se bayan magrib ya fita Kaman yanda yai mata alqawari kuwa tun daga ranar kullum da daddare se ya siyo mata Ice cream guda daya jal ya kawo mata haka suka ci gaba da rayuwa.

RUBUTACCIYAR QADDARAHWhere stories live. Discover now