*RUBUTACCIYAR QADDARAH**By Maryamah* 💞💞
©2020
*PAGE* 1⃣2⃣
ABDUL'AHAD
WACCEN RANAR.Tun bayan daya sauke Hamdah ya bar kofar gidansu gudu yake shararawa kamar me barin duniyar. Tunda yake a duniya mace bata taba ci masa mutunci irin na yau ba, shi mace zata kalla tace waye ze aureshi? Shi zata cewa wai tana da wanda take so? Har ace yayi lalacewar da mace zata kalli idonsa tace bata sonsa? "Illar kula kananan yara kenan" zuciyarsa ta raya masa. Haka ne dan ya tabbatar inda tasan me takeyi bazata kasa gane matsayinsa a zuciyarta ba, ashe hasashen banza yai dayake tunanin gininsa ya isa yabe a cikin zuciyarta. Gefen titi ya faka motar ya kwanta a steery zuciyarsa kamar zata fashe zabar yanda take bugu, yanda yake sauke numfashi kamar wani wanda kunama ta harba ga zufa na keto masa dukda Ac dake busa cikin motar. "Yah Allah ka dubeni kar kasa na rasata, i have submitted all my love to her ita kadai ce hope dina". Hawayen da besan lokacin da suka fara zuba ba ya shiga sharewa yana neman wayarsa dan ya kira Fahad, shi ya bashi gurguwar shawara inda be nemi kusanci da ita ba da komai ya zo masa da sauki amma yanzu fa? Ta ya ma ze fara tunanin cireta a ransa?
" To tace bata sonka se yaya?" Zuciyarsa ta tambayeshi. Tabbas dole ya qyaleta ko da kuwa hakan zeyi ajalinsa tunda har ta budi baki tace bata sonsa. Yana can tunani har besan Fahad ya dauki wayar ba se da ya kashe yavkirashi ringing din ya farkar dashi."Where are you?" Ya tambayeshi a shake."Ina office meya faru" Fahad din ya bashi amsa yana mamakin me ya samu Abokin nasa dan daga jin muryarsa yasan babu lafiya.
"I'm sending you my location come meet me please" kit ya kashe wayar ya shiga WhatsApp ya tura masa da location din, kwanciya ya kumayi kawai ya rasa wanne tunani zeyi a ciki, me ya kamata yayi yanzu? Ya barta ne ko kuma ya ci gaba da pushing har seta amince dashi?. Besan tsahon mintinan daya dauka a wurin ba har Fahad ya zo. Window ya dan kwankwasa masa sannan ya cire lock din Fahad ya shiga motar. Kallon Abdul'ad yayi da idonsa suka kada sukayi Ja sosai da alama akwai babban abinda yake damunsa.
"Dr what's wrong ko baka da lafiya ne?.
Seda ya ja iska sannan cikin wata murya me nuna rauni yace " Fahad Hamdah ce, tace bata sona bazata aureni ba wai tana da wanda take so" ya qarasa maganar yana jin dacin kalaman a zuciyarsa, wani irin kishin ta yake ji ya tsani koma waye wannan daya rigashi shiga zuciyarta."Dr wasa takeyi" Fahad ya samu courage din fada bayan shirun daya yai. "Wasa Fahad, ni abokin wasan tane aka ce maka"
"Ba haka nake nufi ba may be tana so ne taga yanda zakayi reacting ne" se ya katse shi da cewa "Aa. Hamdah is very straight forward person, she talks everything straight from her heart. Kuma tun farko bata taba yimin karya ba dama ta gayamin tana da wanda take so, kai ka ce na gwada kuma yanzu gashi abinda nake gudu ya faru I'm heart broken". Ya qarasa maganar a sanyaye tamkar ba Abdul'ahad baShiru Fahad yayi na dan wani lokaci, yasan duk yanda zeyi convincing dinsa a lokacin ba yarda zeyi ba dan haka yace masa " Believe me Dr tana sonka she just wants to play you around ne, amma kasan me zakayi yanzu" girgiza masa kai yayi alamar Aa yana jira yaji ya fada masa wata magana da bata gamsheshi ba ya naushe shi. Yasan halin abokinsa sarai, girma sukayi suka ga kansu tare baze iya cewa ga sanda suka fara Abota ba dan haka ya saita nutsuwarsa tsaf sannan yace "Give her some space. Kar ka qara kiranta mujira I'm very sure zata neme ka da kanta bet me".
Kallonsa yai na dan wani lokaci yana juya maganar a zuciyarsa. Ba laifi yayi Na'am da shawarar Fahad dan haka ya gyada masa kai Alamar ya yarda. Hakan ya bashi damar Ci gaba da bashi shawarwarin yanda ze shawo kanta, sun dade sosai sannan sukayi sallama kowa ya tafi gida.A masallacin kofar gidansu ya tsaya yayi sallar Magriba tare da Azkar dinsa sannan ya shiga gidan. Da sallama ya shiga palour wata Kyakykyawar Mace tana zaune cikin shiga me kyau ta amsa masa. Fara ce amma ba can ba tana da matsakaicin jiki haka tsahonta ba can doguwa bace. A kallo daya bazaka tantance shekarunta ba saboda hutu da ya taimaka wa jikinta wurin komawa kamar wata matashiya yar shekara 40. Kallonsa take tana murmushi har ya qarasa inda take ya zauna a qasa daidai kafarta " Ammi na sannu da gida"
"Yawwa Galadima ya aikin yau ka dade kai da kace min da wuri zaka dawo" ta fada tana shafa kansa. Kamar karamin yaro ya dora kansa akan cinyarta yana sauke ajiyar zuciya sannan yace "Ammi na dan biya wata unguwane sannan mun tsaya da Fahad a hanya".
" Ko dai gurin surukar tawa kaje ne" ta fada cikin sigar tsokana.
"Ammi can naje amma tace bata sona" Dariya tayi sannan tace "Haba dai anya akwai macen da zata ce bata son Galadima na santalelen saurayi son kowa kin wanda ya rasa kaidai kilan kayi mata wani abun ne take so ta hukunta ka, shiyasa na ganka duk wani iri kenan".
Muryar Kanwarsa Fadila ya jiyo tana cewa " Yaya wannan Farar budurwar taka dan Allah ka aureta wallahi Ammi baki ganta ba har na fara Imagining irin yaran da zasu haifa masu kama da Yaya Farare irinta". Kallonta kawai yayi tareda yin guntun murmushi sannan ya tashi ya nufi Dining dan yunwa yakeji.
Bin bayansa tayi tana cewa "Kaji Yaya ka aureta dan Allah yaushe ma zaka kaini mu gaisa da ita Allah ina sonta" "Fadila tace bata sona se ki bari idan na samo wata se na kaiki ku gaisa" ya fada yana zuba abincin dan a duniya baya wasa da cikinsa, kai ko bashi da lafiya seya ci abinci. Haka ta ringa masa surutu har ya gama cin abincin ya tashi Ammi na zaune a cikin palour tana musu dariya. Fadila ita ce Autarsu, duk cikin kannensa yana ji da ita sosai.
"Ammi ina su Khadija ne naji gidan shiru se wannan parrot din".
"Sun tafi gidan Amina na manta ban gaya maka ba jiya tayi barin yan biyu shine na turasu su taya ta zama tunda mijinta baya nan" Ammi ta bashi amsa. "Ayya Allah ya bata lafiya bari nayi wanka senaje na duba ta"
"Zan bika Yaya" Fadila ta fada kamar tana jira yace ze je gidan. "Kije ki shirya karki kuma batamin lokaci" ya fada yana fita daga palour zuwa part dinsa dan yin wanka. Har 11pm na daren ranar yana gidan Amina kanwarsa datake bi masa, Abdul'ahad mutum ne me matukar son yan uwansa. Yana matukar tausayinsu, Yayyensa biyu Saudah da suke kira da Hajia karama ita ce babbarsu, tayi aure tuntuni suna zaune a America da Yaranta hudu se me bi Mata Fatima ita ma tayi aure a Lagos tana da yara biyu da cikin na uku sannan shi se Amina me Da Daya se kuma twins dinsu Khadija da Hafsa sannan Auta Fadila. A zamansu ya duba wayarsa yafi sau dari duk a jiran tsammanin ganin text ko kira daga Hamdah amma babu ko daya a ciki har Amina ta lura dashi take tambayarsa ko lafiya dan dama tunda ya shiga tasan akwai wani abu dayake damunsa. Ba komi yace mata kawai yana duba lokaci akwai abinda zeyi dan haka yacewa Fadila ta tashi su tafi badan ta so ba ta bishi dan dai Ammi taja mata kunne akan karta kwana ne. A hanya duk irin surutun data ke masa be tanka mata ba har suka zo gida, a get ya tsaya ta sauka ya qara fita ita dai ta shiga tana mamakin me yake damunsa haka ina zashi da daren nan dan kadan ya rage sha biyu tayi.Cikin school ya tafi a daren dan akwai abubuwan dayake so ya dauka a office dinsa. Sanin ko karfe nawa ne akwai attendant a office din Registerer ya saka shi rubuta takarda yaje ya kaimusu sannan ya tafi gida lokacin har daya ta gota. Ya riga yayi niyya baya jin akwai abinda ze dakatar dashi, a daren ya hada duk abinda yake da buqata, karfe shidda yaiwa Ammi da Fadila sallama ze tafi Abuja ze tsaya gurin Baba yai kwana daya sannan ya wuce Singapore akwai wani Team dayai joining zasuyi wani Research work akan Gene mutation in Snakes, A da ya jingine aikin amma yanzun shine right time daya kamata yayi, yana buqatar abinda ze dauke masa tunaninta daga ransa. Kwansa daya Abuja ya daga Kasar Singapore ya qudurcewa ransa yabar kowa da komai daya shafe ta, baya tunanin ze qara waiwayar Nigeria ma nan kusa.
Ba karamar wahala yasha ba kafin yai over coming tunaninta daga ransa dan abin kamar tishi harta kai idan yana aiki yana ganinta a ciki, duk macen daya gani kuwa sunanta Hamdah se dakyar abin ya fara rabuwa dashi ya ajiye batun aure ko soyayya a gefe, bayajin ze qara waiwayarsu nan kusa.
*****************
CIGABAN LABARIAbdul-ahad zaune shida abokanansa Master, Aliyu se Mustapha. Abokanasa ne tun zamanin sa sukayi karatu tare a Cambridge, dukkansu mutanene masu hazaqa kamarsa shiyasa Abotar tasu tayi qarko yanzuma dukka tare suke research work din. Mustapha dake ta faman danne danne cikin waya ne yace "Nigeria is on fire wani yayi wuf da jewel yayiwa gayu game over" kallonsa sukayi gaba daya banda Guru da kwatakwata hankalinsa baya tare da hirar da sukeyu yarasa meke damunsa akwana biyunnan yana yawan tsintar kansa da faduwar gaba daya rasa dalilinta sannan ga tunanin HAMDAH AMMANI da ya addabeshi. Wani lokacin ya kanji kaman ya kirata amma seya kasa. Yana matuqar kewarta, sonta ya kasa barin zuciyarsa a kullum kamar qara masa akeyi.
"Kai gaskiya yarinyar nan ta qeru Guy dinnan yaci Maza dayawa wasa irin wannan zukekiyar yarinya haka" sambatun Mustafa ne yakatse shi bedai ce komai ba illah kallonsu daya keyi jin yanda suke zuzuta kyan yarinyar. Gaba daya suka hada kai suna kallon hoton se zuzutu sukeyi.
"Man Kalli ka gani mana I'm sure ko wannan Aljanar data lashe maka zuciya bata kai wannan kyauba" Aliyu ya fada cikin sigar wasa. Murmushi yayi tareda karban wayar yana cewa "bana tunanin akwai wata mace dazata kai kyan HAMDAH a idona her beauty has no match to me...."maganar ce ta makale masa, Idan dai ba idanuwansa keyi masa gizo ba Tabbas HAMDAH ce wannan. Tayi kyau har ta gaji cikin wani hadadden Swiss lace black me adon flower red haskenta ya qara fitowa fuskar nan tasha light make up ze iya rantsewa be taba ganin tayi kyau irin wannan ba.Wata irin juwa ce fara daukansa daga zaune ga Amai na kokarin taso masa kafofin jikinsa babu wacce bata fitar da gumi duk kuwa da sanyin AC dake dakin. Scrolling din hotunan yaci gaba dayi aransa yana addu'a Allah yasa dai Kamace ko kuma mafarki yakeyi sedai addua'arsa bata karbu ba lokacin dayai tozali da bakin sako, katin gayyatar daurin Auran Abdulmalik Kamalu Dala da Hamdah Ahmad Ammani nan take ya gyara zama kaman wani dan bori a qasa, baya neman sauran qarin bayani itace, itace za'a aura wa wani Babu ko tantama Hamdan sace.
"No it can't be possible" ya fada on top of his voice tareda cilli da wayar ta bugu da bango a take tayi kwatskwatsa, mikewa tsaye yayi jikinsa na rawa kamar mazari abin tausayi se kawai ya yanke jiki ya fadi a gurin.To ya zata kasance 😳🥺🥺
Vote
Like and
Share
CZYTASZ
RUBUTACCIYAR QADDARAH
RomansStory of two lovers Hamdah and Abdul'ahad who were blindly in love but didn't realize until it was too late for them, yes they are meant to be together but destiny keep them apart..