Part 43

702 46 0
                                    

RUBUTACCIYAR QADDARAH*

*By Maryamah* 💞💞

©2020

*PAGE* 4⃣3⃣

Tana shiga dakin taci birki, tama rasa abinyi ta ina zata fara. "Ya ubangiji ka rufamin asiri Allah na tuba" abinda kadai take iya maimaitawa kenan. Tana jinsa ya na buga kofar amma tayi banza dashi dukda wata zuciyar tana ce mata "ki bude, idan har hasashenki gaskiya ne tun wuri kusan abinyi ai bake kadai ya shafa ba" har ya gaji ya rabu da ita Seta durqushe a gefen gadon ta fashe da wani irin kuka kaman Marainiya. Wace Qaddarar ce kuma haka ta ke neman tarar da ita?

"Ubangiji ka sa ta zomin da sauki ka bani abinda zan iya" ta fada cikin wani irin sauti me ban tausayin. Tarin nadama da dana sani suka lullubeta, tana ganin tafi kowa laifi dan ita ta bashi fuska kuma be taba mata dole ba, duk tsiya dai itama tana bada Hadin kai tunda ba daureta yakeyi ba. Soyayya batayi mata rana ba a wannan lokacin meyasa tun farko bata hango wannan illar ba? Ita yanzu ya zatayi? Batasan iya lokacin data dauka ba da abinda ya faru bayan nan qarshe kawai ta farka taganta cikin jikin Abdul'ahad.

Baza ta iya fadar ainihin abinda ya faru ba amma ta tabbatar wani al'amari ya kasance. Yanda yake sunkuyar dakai ya kasa koda kallonta seta mike kawai kuka na neman kwace mata ta fada cikin bathroom. Seda tayi me isarta sannan tayi wanka ta dauro Alwala lokacin karfe uku harda Rabi na dare ta fara jero nafiloli, Irin kukan da take yi me ya daga masa hankali dan ya banbanta dana ko yaushe. Yana kwance yana kallonta afarko ya zata sabon halin data koya ne se daya ci gaba ya gane akwai abinda yake damunta. Jira yayi ta sallame Raka'ar da take ya dagata cak ya aza kan gadon yabita ya kwanta a gefenta hannayensa biyu cikin gashin kanta yana ya mutsawa. Addu'oi ya ringa tofa mata a hankali ta fara tage kukan se Ajiyar zuciya datake saukewa ajere ajere har ta nutsu lokacin har an fara kiraye kirayen Sallar asuba.

"Hamdah ki dena yawaita kukan nan bashida kyau fa dan Allah" ya fada cikin sauti me rauni. A maimakon shirun da tayi seya dawo mata da abun sabo. "Waifa kilan akwai dan sa ko Yarsa a cikinta" tausayin kanta dana Abinda zata haifa din suka kamata seta sake fashewa da wani sabon kukan tana miqewa zaune daga jikinsa. Kaida Guiwa ta hade ta ringa kukan me ban tausayi shidai yana zaune ya kasa tabuka komai dan besan me kuma aka mata ba. Tambayar duniya taqi magana karshe tace in yana so tayi shiru ya fita yabar mata dakin. Allah sarki seya miqe shima duk ya sukurkuce lokaci daya. Idonta biyu akayi sallar Asuba, tana idarwa ta dora daga inda ta tsaya da kukan karshe se Bacci barawo ne yak nasarar saceta tana kukan.

Karfe 2pm har ta gota sanda ta farka. A maimakon kan sallaya data kwanta seta ganta akan Gado lullube da Duvet. Kallon dakin tayi sosai seta gane dakinsa ne saboda kamshinsa daya kama ko ina wanda ada take bala'in so Amma yanzu se taji yana neman tayar mata da zuciya. A sanyaye ta zubo fararen qafafunta qasa tana kallon ko ina na dikin, Fitsari datake ji ya sa ta miqe ba shiri ta shige toilet din seda tayi shi sannan ta samu nutsuwa, cikinta ne yayi wani kuka seta fita zuwa kitchen dan har wani jiri jiri take ji. Ta rasa me yasa kwana biyun nan in taji Yunwa duk seta firgice. Yoghurt ta samu 2L data daga se robar ta sauke ta nemi kujera ta zauna tana sauke numfashi minti biyu Amai ya taso mata seda ta Amayar da yoghurt din tas sannan ta kuskure bakinta da ruwa ta fita daga kitchen din tana jin kaman Aman ya tafi da duk wata kasala data tashi da ita. Sallah ta farayi dan lokaci ya tafi sannan ta shiga gyaran gidan da kuiya tasa kwana biyu bata yi ba. Seda ta gyara gidan tsaf ta bi duk wani lungu da sako ta saka turaren wuta masu azabar qamshi nan da nan gida ya dau harami kaman wani gidan Amaryar Kanuri. Kafin ta gama aikin har Magriba ta kawo kai.

RUBUTACCIYAR QADDARAHحيث تعيش القصص. اكتشف الآن