Part 41

687 54 2
                                    

RUBUTACCIYAR QADDARAH*

*By Maryamah* 💞💞

©2020


*PAGE* 4⃣1⃣


"Ka cuceni ka yaudareni ka kuma ci Amanar yarda wallahi se Allah ya sakamin wannan itace soyayyar da kake iqirarin kana min dama abinda kake muradi kenan meyasa tun farko baka bayya na manufarka akaina ba". Shiru yayi mata saboda Ubangiji ne kadai yasan yanayin da yake ciki a lokacin, wata duniya yaje ya dawo da be taba sanin wanzuwarta a doron qasa ba. Lallai hausawa sunyi gaskiya da sukace wai garin dadi na nesa, amma abun ya so ya daure masa hankali kadan.

Dukda besan mace ba a rayuwarsa be taba kusantar wata mace ba se yau amma a karance yasan komai game da mata. Hamadah tayi aure har sau biyu amma a yanda ya sameta idan badan ya sani ba he can swear with his own life that she is Virgin. Takai ta zarce duk wani hange da tunaninsa, her inner beauty is far beyond his imagination. Ubangiji ya mata baiwar daya tabbatar ba kowacce mace ba dan idan duk matan haka suke da babu wawan da ze yarda yai asarar Mace kamarta. Kukan da take yi yana neman ya hanashi tunanin da yake me matuqar dadi da qawata zuciya. Beqi su dawwama a wancan yanayin ba har qarshen numfashinsa. Nutsuwa da kwanciyar hankalin daya samu da ita ta zarce misali, se kawai ya birkito ta gaba daya ta dawo saman jikinsa dukda irin zazzabin dayaji yana bi masa qashi da tsoka kaman ana gasa shi a Oven.

"Allah yai miki albarka AYSHATU Ubangiji ya baki abinda kike so duniya da lahira yanda kika farantamin kema Allah ya miki sama da haka". A cikin kunnenta dukka yayi wannan maganar, dukda irin kukan da take amma seda ta dan tsagaita na wani lokacin dan kalamansa sun mata Dadi. Sun tuna mata da daren farkon ta da Habibinta Marigayi Abdulmalik yanda yaringa rawar jiki yana sa mata albarka. Abdurrahman bazata dorar da komai akansa ba dan sambatune mara sa kai ya keyi shi amma Abdul'ahad fa? Idan ta tariyo maganganun daya ringa gaya mata dazu kwakwalwarta ai bazata iya dauka ba shiyasa ma bata bada muhimmanci gurin riqesu ba.

Seta saki sabon kuka lokacin dataji yana qoqarin sake maidasu ruwa. Se a sannan hankalinta da tunaninta suka dawo daidai ta tuna da danyan aikin da suka aikata. Fuskarsa ta riqe da hannayensa dayake aika mata saqonni dasu kafin ta mirgina da sauri ta sauka daga gadon se kuma ta kwalla qara tareda durqushe wa a gurin tunawa da babu komai a jikinta.

"Wane dare ne kuma jemage be gani ba Ammata, dan Allah tashi na kalleki sosai na qara godewa Allah bisa irin ni'imar da yayimin" magana yake cike da qarfin hali saboda zazzabin daya fara cin qarfinsa har jijinsa ya fara rawa. Yana kwance yana kallon yanda ta hada kai da gadon tana kuka abin tausayi taqi tashi ta kuma qi magana dukda irin roqonta daya ringayi. Abu daya take maimaitawa "ya cuceta ya bata mata rayuwa bazata yafe masa ba se Allah ya musu hisabi ita dashi tunda fin qarfinta yayi ba a son ranta ba" har muryarta ta dashe tsabar kuka ga ciwon kai da zazzabin ita ma yana neman kamata.

Babu daya a maganganunta da suke masa dadi, amma shi ta ina ze farawa wannan yarinyar me shegen kafiya bayani? Zama ta yarda ta saurareshi ne  a yanda ta hau dokin zuciyar nan shedan na qara buga mata ganga? Kukanta ya ishe shi, se kawai ya mike tsaye da niyar zuwa inda take ya rarrasheta ko ze samu tayi shiru cikin tsautsayi jiri ya debe shi ya tafi gaba dayansa ze fadi da azama ta tareshi suka koma a tare suka kwanta kansa a qirjinta yana fitar da numfashin wahala me azabar zafi. Ba shiri kuka ya tsaya cak dan jin zafin jikinsa na barazanar qona mata fata ta shiga tattaba kansa zuwa wuyansa tana cewa

"Meya sake ka baka da lafiya jikinka yayi zafi Abdul'ahad sosai". Yanda ta rude se kuma ta bashi tausayi. Yasan Hamdah tana sonsa koda bekai yanda take sonsa ba, se kawai ya qara narkewa a jkinta yanayin yanda fatarsu ta manne guri daya ya masa dadi ji yake kaman ya rabe biyu ta shige ya sake hadewa, dakyar ya bude baki yace

RUBUTACCIYAR QADDARAHWhere stories live. Discover now